03/03/2020
TARIHIN ANNABI MUHAMMADU
__
HIJRAH
Lokacin da Annabi ﷺ da babban amininsa Sayyidina Abubakar (R.A) zasu tafi, sai Abubakar ya ce da Annabi ﷺ, “Ya Ma'aikin Allah, ga wasu raƙuma nan guda biyu waɗanda na tanadar mana domin wannan tafiya!”, s**a kuwa ɗebi guzuri s**a hau waɗannan raƙuma s**a bar garin Makka, s**a nufi wani kogon dutse da ke SAWR, kudancin garin Makkah, inda s**a yi niyyar ɓuya, domin sun san cewa wajibi ne kafiran Makkah su biyo sawayensu.
Lokacin da s**a bai wa garin Makkah baya, sai Annabi ﷺ ya juyo ya fuskanci Makkah ya ce, "A duk duniya ke ce wuri mafi soyuwa a wajen Allah, haka ma a wajena! In ba don mutanena sun wajabta min barinki ba, da ba zan taɓa barinki ba!”
Kamar yadda Annabi ﷺ da abokinsa Abubakar (R.A) s**a yi tsammani kuwa haka aka yi, domin ko da Qurayshawa s**a gane cewa Annabi ﷺ da abokinsa sun fice daga Makkah, ai kuwa sai s**a tayar da mahaya bisa dawaki domin su bi bayansu! S**a dinga nemansu lungu da saƙo. Sai da s**a shafe kwana uku suna nemansu a lungu da saƙon dazuzzukan dake kewayen garin Makka, amma basu gano maɓoyarsu ba.
A rana ta ukun ne s**a iso bakin kogon SAWR inda Annabi ﷺ da abokinsa Abubakar (R.A) suke ɓoye, inda a wannan lokaci wani babban abin al'ajabi ya wakana. Wani gizo-gizo ya zo ya rufe duka ƙofar shiga kogon dutsen da yana, kuma wata kurciya ta zo ta saƙa sheƙa a bakin ƙofar kogon!
Lokacin da mutanen Makkah s**a ƙaraso gab da bakin ƙofar kogon, babu komai tsakaninsu da ganin abinda ke cikin kogo banda wannan yanar gizo-gizo, sai Sayyidina Abubakar (R.A) ya tsorata saboda gudun kar su gansu. Sai ya yi wa Annabi ﷺ magana cikin raɗa yana cewa, “Sun fa zo gab da mu, idan har ɗayansu ya waiwayo, babu shakka zai gan mu!"
A wannan lokaci sai Annabi ﷺ ya ƙarfafa masa guiwa cikin murmushi, yace, “Me kake zato game da (mutum) biyu waɗanda Allah Shi Ne na ukun su?”
ﻻ ﺗﺤﺰﻥ ﺇﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﻣﻌﻨﺎ
“Kar kayi baƙin ciki, lallai Ne, Allah Yana tare da mu!”
(Tawbah: 40)
Wasu daga cikin mutanen nan sun bada shawarar a shiga cikin kogon a duba, amma sai wasu masu hankali daga ciki s**a ce, “Ba ku da hankali ne? Kuna gani har gizo-gizo ya rufe ƙofar kogon da yana, ga tsuntsuwa tana kwanci? Ta yaya za ayi a samu wata halitta mai rai a cikinsa?” Bisa haka s**a gamsu cewa lallai babu kowa a cikin kogon, kuma s**a juya s**a tafi ba tare da sun duba cikin kogon ba. Lallai gaskiya ne wai aka ce raahin sani ya fi dare duhu Kuma haƙiƙa, wanda Allah Ya so Ya ɓatar, babu wanda zai iya ganar dashi.
A cikin kogon ma kuma wani abu ya sake wakana, lokacin da Abubakar (R.A) yake kishingiɗe, yayin da Annabi ﷺ yake kwance ya yi matashi da cinyarsa yana barci Shi kuma yana gadinsa. Abubakar (R.A) ya lura da wani rami a cikin kogon, wanda ga dukkan alamu ba a rasa wani mugun abun dake rayuwa a ciki. Sai ya sanya duddugensa ya toshe bakin ramin, saboda kar wani abu ya fito ba tare da ya lura ba ya zo ya cutar da masoyinsa Annabi Muhammadu ﷺ dake kwance yana barci.
Kamar yadda Abubakar (R.A) ya yi zato ashe kuwa haka ne, ashe ramin wata macijiya ne. Ita kuma ashe ta jiyo ƙamshin jikin Manzon Allah ﷺ kuma ta jiyo maganarsa, ta yi nufin fitowa ta zo wajensa domin ta gaishe dashi ﷺ, ko da ta zo bakin ramin zata fito sai kuwa ta ci karo da ƙafar Abubakar (R.A) ta toshe ƙofar, ai kuwa bata yi wata-wata ba ta fara gartsa masa cizo a ƙafar.
Sayyidina Abubakar (R.A) ba ƙaramin zafi ya rinƙa ji ba a ƙafarsa saboda cizon wannan macijiya, amma bai yarda ya janye ƙafarsa ba daga bakin ramin, saboda ya gwammace ko da zai rasa ransa ya kiyaye lafiyar Manzon Allah ﷺ ! Ko ƙwaƙƙwaran motsi bai yarda yayi ba, saboda gudun kar ya farkar da Annabi ﷺ daga barcinsa. Haka dai gumi ya dinga tsattsafo masa na azaba, idanunsa s**a yi ja, har saida guminsa ya rinƙa ɗigowa a jikin Annabi ﷺ dake kwance a cinyarsa, sannan ne Annabi ﷺ ya buɗe idonsa ya ga halin da abokin nasa yake ciki.
Ko da Annabi ﷺ ya lura da abinda ke faruwa, sai ya umurci Abubakar (R.A) da ya cire ƙafarsa ya bar macijiyar ta fito. Macijiyar ta fito ta gaishe da Annabi ﷺ , sai ya tambayeta dalilin da yasa ta cutar masa da abokinsa, ta gaya masa cewa, ita dai ta jiyo ƙamshinsa ne kuma ta ji maganarsa, ta taho domin ta zo wajensa, shi kuma Abubakar (R.A) ya tare mata ƙofa, shi yasa ita kuma ta yi haka don ta samu ya ba ta hanya!
ALLAHU AKBAR! MACIJIYA (DABBA) FA KENAN TA ZAGE DAMTSE WAJEN KAWAR DA ABINDA YA TARE MATA HANYAR SADUWA DA MASOYI ﷺ , MU MUTANE ME MUKE JIRA? WANNE ƘOƘARI MUKE YI DON GANIN MUN SADU DA SHI?
A wannan lokaci dai Annabi ﷺ ya shafi ƙafar Abubakar (R.A), ƙafar ta warke ta daina zogi, kuma dafin cizon macijiyar ya ɗauke, k**ar ma dai babu wani abinda ya samu Sayyadina Abubakar (R.A).
Ka ji likitan likitoci kenan, mai yaye damuwa, mai ɗauke ciwo anan take, Annabi Muhammadu ﷺ
Allah Ka sada mu da Annabi Muhammadu
(Sall'ALLAHU 'AlayHi Wa Ãlihi WA Sallam)
Ameeen
Allah ya Kara hadamu daku..
©•WALADUN NABIYYI