05/04/2024
Daga Kontagora
Rahoto cikin hotuna yadda aka gudanar da Muzaharar Qudus Day a garin Kontagora, jihar Neja.
Jin kadan da kammala sallar Juma'a yau 26ga watan Ramadan 1445BH, dai dai da 5th ga watan April, 2024.
Yan uwa musulmi almajiran Sayyid Ibraheem Zakzaky (H), na yankin Kontagora s**a fito domin nuna goyon bayan su ga al'ummar Palestine.
Muzaharar ta faro daga Babban Masallacin Juma'a na garin dake tsohuwar Kasuwa. Inda ta Rasta tsakiyar garin Kontagora, a karshe aka rufe muzaharar a bakin Asibitin Tagwai.
Daruruwan Yan uwan ne S**a halarci muzaharar a yau. Suna tafe dauke da tutocin kasar Palestine. Tare da rera baitocin nuna goyon bayan su ga al'ummar Palestine da HMK Israel take kashe.
Wakilin Yan uwa almajiran Sayyid Zakzaky (Sheikh Ibrahim Ahmad Imam) ya gabatar da jawabin rufewa. Tare da bayyana makasudin wannan fitowar ta yau.
Malamin yayi takaitaccen jawabin, inda yajawo hankalin al'ummar Musulumi na cikin garin Kontagora da cewa, “al'amarin Palestine ya shafi kowanne Musulumi Mai shaidawa da Kalmar Shahada. ”
Daga karshe aka rufe da addu'a aka sallami mahalar. Anyi lafiya an tashi lafiya.
📸Photo credit :
©Kontagora Media forum
5th April,2024