26/03/2024
SHAWARI KAN HANYOYIN GYARAN TILAWAN QURAN MAI GIRMA
1. Maimaita kowani Rubui sau adadi masu yawa kaman sau 50 ko 60 ko 70 ko sama da haka karatun yazama cikin Kulawa da Nitsuwa da kuma dalibi ya zama yanason yin karatun
2. Yin Sallan dare da izu daya ko biyu ko sama da haka cikin Kulawa da hadda tareda tadabburi da nitsuwa kar ayi gaggawa
3. Rubuta Qurani a Allo inda hali tareda sanin Qaidodin Rubuta Qurani da koyon rubutashi
4. Ikhtibaar ga dalibi a qalla duk sati sau daya ayi masa tambayoyi kaman 10 ko sama da haka, Sannan Yakamata ayi ikhtibaar wa dalibi cikin Qurani aqalla tambayoyi 300 kuma Kar yayi kuskure da yawa kuskuren yazama kadan sosai
5. Musaffa tsakanin mutum biyu ko sama da haka na wasu izuzzuka amma kar arinqa bata tilawa sonsamu ya zama babu kuskure kuma ayi karatu anitse sosai da kulawa da mutashabihaat
6. Yin Musabaqan Qurani da niyyan gyara Tilawa da kuma niyyan neman yardan Allah wajen Karatun Qurani da Naci da neman Shawarin Malamai kan hakan
7. Tasmiin kowani Izu a gaban Malamai kaman 10 ko sama da haka ayi karatun cikin Nitsuwa da tajwidi sonsamu kar ayi kuskure cikin kowani izu kuma karatu cikin Nitsuwa da tajwidi da kwadayin karatu
8. Kulawa da Mutashabihaat ( Ayoyi Masu K**a ) da banbancesu, rubutasu, da kuma yawan tunosu duk lokacin buqatan haka
9. Yawan Sauraron Karatun Quran cikin Kulawa da kuma niyyan gyara tilawa
10. Lizimtan Mushaf (Qurani) guda daya Na Karatu
11. Addua
Rubutawa
Yusuf Muhammad Dukku
16- Ramadan - 1445
26- March- 2024