Maisallah tv

Maisallah tv News and broadcasting media

YANZU-YANZU: An Ga Jinjirin Watan Ramadan A Garin Damaturu Dake Jihar YobeGanau ba jiya ba ne ya tabbatarwa da RARIYA ga...
22/03/2023

YANZU-YANZU: An Ga Jinjirin Watan Ramadan A Garin Damaturu Dake Jihar Yobe

Ganau ba jiya ba ne ya tabbatarwa da RARIYA ganin jinjirin watan a yanzu haka.

MÚHAWARA: Faɗa Mana Dalili Ɗaya Tak Da Yasa Kaké San Kwankwasó Ya Zama Shugaban Ƙasà ?
23/02/2023

MÚHAWARA: Faɗa Mana Dalili Ɗaya Tak Da Yasa Kaké San Kwankwasó Ya Zama Shugaban Ƙasà ?

MÚHAWARA: Faɗa Mana Dalili Ɗaya Tak Da Yasa Kaké San TINUBU Ya Zama Shugaban Ƙasà ?
23/02/2023

MÚHAWARA: Faɗa Mana Dalili Ɗaya Tak Da Yasa Kaké San TINUBU Ya Zama Shugaban Ƙasà ?

MÚHAWARA: Faɗa Mana Dalili Ɗaya Tak Da Yasa Kaké San ATIKU Ya Zama Shugaban Ƙasà ?
23/02/2023

MÚHAWARA: Faɗa Mana Dalili Ɗaya Tak Da Yasa Kaké San ATIKU Ya Zama Shugaban Ƙasà ?

12/02/2023
12/02/2023

Daga dakin taro na kaura namoda (town hall) muke kawo maku shiri na daddaden tarihin kaura namoda Wanda yake gudana a yanxu

Gayyata!   Gayyata!!   Gayyata!!!Shidai wannan taro na tarihin Kaura Namoda an share kusan shekara biyu ina shiryashi......
12/02/2023

Gayyata! Gayyata!! Gayyata!!!

Shidai wannan taro na tarihin Kaura Namoda an share kusan shekara biyu ina shiryashi......

musamman wajen hada mujallar Kaura Namoda (Kaura Namoda Magazine 2022 Edition) da kuma wajen Tantance wadanda Za'a Karrama.

kuma idan Allah ya kaimu wani lokacin za'a kara hada taron da yafi wannan.

muna fatan duk wani mai son cigaban garin Kaura Namoda Zaizo ya bada tashi gudun mawa da goyon baya.

In_sha Allah zamu kawo maku live stream na abubuwan da zasu wakana a wurin taron

08/02/2023

Bukin sabkar Alqur'an daga makarantar rahamaniyyah ,kaulaha baking kasuwa kaura namoda zamfara State farm

07/02/2023

In_sha yau zamu Fira da kwamitin
Tantancewa na scholarship din jaji

Ina neman alfarmar dukkannin abokaina na wannan dandalin da su zabi Alhaji Atiku Abubakar a matsayin shugaban kasar Naje...
05/02/2023

Ina neman alfarmar dukkannin abokaina na wannan dandalin da su zabi Alhaji Atiku Abubakar a matsayin shugaban kasar Najeriya a zabe mai zuwa.

Bance Atiku Abubakar yafi kowa iyawa ba, ko kuma yafi kowa adalci ba, kuma ban baku tabbacin cewa lallai sai ya gyara Najeriya kamar yadda muka sa rai idan Buhari yahau mulki ba zai gyara ta.

Inada tabbaci da yakini Insha'Allah idan kuka zabi Atiku Abubakar ya zama shugaban kasar Najeriya na tabbata da zaran yahau mulki zai bude bododin Najeriya, wanda hakan zai jawo kayan abinci suyi sauki, kayan kamfanonin gida da na kasashen waje duk zasu yi sauki sosai.

Shinkafar waje, Taliya da sauran su zasu yi mugun karyewa, Insha'Allah Man Fetur zai wadata, za'a samu saukin rayuwa fiye da yadda muke tunani.

Sannan ina da yakinin zai cigaba da tono danyen Man Fetur dake Arewa kuma zai kara kaimi wurin bawa al-ummar Najeriya tsaro kuma Insha'Allah zai gudanar da manyan ayyukan cigaba wa 'yanda zasu amfani talakawan Najeriya.

Na tabbata iya wa 'yan nan ayyukan kadai idan Atiku Abubakar ya gudanar dasu talakawan Najeriya zasu ji dadi kuma zasu yi murna da kasancewar shi a matsayin shugabansu.

Dukkannin abubuwan da na fada wallahi ko baka son Atiku a cikin zuciyar ka, na tabbata kai kasan Atiku zai gudanar dasu duba da kasancewarshi gogaggen dan kasuwa kuma masanin farfado da tattakin arzikin Najeriya.

Bance lallai sai kun amshi rokona ba, nasan kowa nada nashi ra'ayin, amma idan kuka karbi rokona kuka zabi Atiku Abubakar ya zama shugaban kasar Najeriya Insha'Allah ba zai bamu kunya ba

✍️ Comr Abba Sani Pantami

05/02/2023

Now Maisallah tv is on tiktok
L
Kuyi searching maisallah_tv kuyi following

Yakamata Maza Je Ku Hankaltar Da Matan Ku Dangane Da Maganar Canjin Kuɗin Da Gwamnati Take Ƙoƙari Yi.Ga dukkan alamu yad...
22/01/2023

Yakamata Maza Je Ku Hankaltar Da Matan Ku Dangane Da Maganar Canjin Kuɗin Da Gwamnati Take Ƙoƙari Yi.

Ga dukkan alamu yadda gwamnatin Nigeriya ta tsara dangane da canjin kuɗin da tafitar zai tabbata kamar yadda muka ga alama.

A fahimtar da nayi wa shugaban ƙasa Muhammad Buhari wallahi ba wani sassauci da zayyi a kan wannan dokar.

Idan kuwa wannan tsarin ya tabbata haƙika za'a wahala matuƙa, musamman mutanen karkara da kuma matan aure.

Da yawa zaka samu matan aure musamman na karkara suna ajiye maƙudan kuɗi acikin ɗakunan su, wasu ma kawai suna jin ana magana kan canjin kuɗin amma basu yi tunanin dokar ta girma ba, wasu kuma basu san yadda zasu sarrafa kudin zuwa sabbi ba, wasu kuma kaf Lga ɗin su babu Banki.

Shawara ta ga mutanen karkara da matan aure shine tunda kayan gona yayi sauƙi yanzu kowa yaje ya siye kayan gona ya ajiye wannan ita ce hanya mafi sauƙi da zamu rage ma kanmu wannan raɗaɗin da aka jefa mu.

A gaggawa yin haka kar ayi da nasa ni, domin wurare da dama sundena karɓar wannan tsofaffin kudaden.

✍️Nazeer adamu umar

JUMMU'AT MUBARAKYake Dan uwa Ina maka fatan alkhairi a wannan Rana Mai albarka sannan Ina Kara jadadda godiya bisa kulaw...
20/01/2023

JUMMU'AT MUBARAK

Yake Dan uwa Ina maka fatan alkhairi a wannan Rana Mai albarka sannan Ina Kara jadadda godiya bisa kulawarku akan Shanin yakamata a aikin alkhairi
Sannan Ina shawartarku da mutsayi muyi aiki tukuru don gannin gobenmu tayi kyau sannan mucigaba da hakuri da juna dukkan mu wata Rana Sai dai ayi labarinmu
Mu kyauta tsakanninmu da mahallacinmu muyi aiki na kwaira

Allah yasa mudace da alkhairi
Allah yasa karshenmu tafi farkon kyau

✍️Red pen

Allah ya karbi bakuncinka  ya yafemaka kurakuranka alfarmar annabin rahama
17/01/2023

Allah ya karbi bakuncinka ya yafemaka kurakuranka alfarmar annabin rahama

Kasar Algéria ta gida katafaren masallaci da yafi kowane girma a Afrika kuma ya kasance na ukku mafi girma a duniya baya...
17/01/2023

Kasar Algéria ta gida katafaren masallaci da yafi kowane girma a Afrika kuma ya kasance na ukku mafi girma a duniya bayan masallacin Makkah da na Madina.
Masallacin na daukar mutun 120,000.

JUMMU'AT MUBARAKDan uwa RAYUWA sauki gareta yadda ka dauketa haka zata zoma, kayi tunani a lokacin baya mutane dake ungu...
13/01/2023

JUMMU'AT MUBARAK

Dan uwa RAYUWA sauki gareta yadda ka dauketa haka zata zoma, kayi tunani a lokacin baya mutane dake unguwarku waddanda yanxu Babu su duk Allah yakarbi abunai

Wannan rayuwar Jindadinta kadan ne, kayi amfani da sauran lokacin ka wurin aiki Alkhairi domin kasamu yarda Allah da tsira ranar gobe kiyama

Allah yasa karshen mu tafi farkon mu kyau🙏🙏

10/01/2023

Watarana wani Bawan Allah ya auri wata Amarya budurwa, a ranar daren farko, Amarya ta tashi ta tsaya a gaban shi tace dashi: "Ka suturta ta ni Allah Zai suturta ta ka! Ka suturta ta ni Allah Zai suturta ta ka!! Ka suturta ta ni Allah Zai suturta ta ka!!!"...

Sai yake cewa da ita: "Baiwar Allah menene ya faru haka!?"

Sai tace dashi: "Bawan Allah banzo gidan ka a matsayin budurwa ba, hasalima nazo da ciki".

Sai yace da ita: "In Shaa Allah zan suturta ta ki"....

Washe gari sai kawai ya yanke shawarar barin garin shi da amaryar shi.. Inda s**a tafi wani gari yaje ya samu wajen zama ya zauna da matar shi..... Sai yake sanar da ita cewa babu ruwan ta da fita ko ina, kuma babu wanda zai shigo mishi gida tunda bai bada fuska ba..

Ana nan ana nan ciki yayi ta girma. Mutumin ya kasance mai yawan ibada wanda sallah bata wuce shi cikin jam'i....

Rannan kawai sai naƙudar matar ta tashi cikin dare. Cikin ikon Ubangiji ta haihu lafiya. Mijin nata yace da ita: "Ki bani yaron nan, In Shaa Allah zan dawo miki dashi cikin aminci"....

Ƙirar sallahr asubar fari ya ɗauki jariri yaje harabar masallaci ya ajiye shi sai ya lallaɓa ya dawo gida...

Bayan jama'a sun fito domin gabatar da sallahr asuba ciki hadda wannan mutumin, kwatsam sai aka ji kukan jariri a gefen masallaci. Aka yi maza aka ɗauko jariri aka ajiye a gefe guda yana ta kukan shi. Aka idar da sallah a nata faman Allah wadai da wacce ta jefar da wannan yaron. Sai Liman yace: "ba Allah wadai zamu tsaya yi ba, mu nemi mafita ya ya za'a yi da yaron kawai, ko akwai wanda zai riƙe wannan yaron?". Kwatsam wannan bawan Allah ya ɗaga hannu yace a bashi yaron In Shaa Allah matar shi zata kula dashi har iya tsawon ranta "...

Haka kuwa akayi a ka bashi yaron ya taho gida dashi yace da ita: "Baiwar Allah ga ɗanki ya dawo gareki cikin aminci, ammana kisani cewa ba yaro na bane"....

Labarin matar sai ya cika gari akan yadda aka tsinci yaro aka kai mata ta riƙe ba tare da wani damuwa ba...
✍️Gen Yasser

10/01/2023

KA DARAJA MUTANE UKU A DUNIYA 🌎
1. Dattijo. 👴🏼
2. Malami
3. Iyaye

Ka tausayawa mutane uku
1. Tsoho
2. mace.
3. Yaro karami

Kada ka manta da Abu uku
1. Mutunci
2. addini.
3. Mutuwa.

Ka tsarkaka Abu uku
1. Jikinka
2. Tufafinka
3. Zuciyarka.

Kada ka daina Neman Abu uku
1. Ilimi
2. arziki.
3. Aljanna.

Allah yasa mudace

✍️Abdulmalik Hassan Malikiyyah

Address

Tafida Road
Kaura-Namoda
0883

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Maisallah tv posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Maisallah tv:

Videos

Share