Kaura Namoda Online TV

Kaura Namoda Online TV Kaura Namoda Online TV, Gidan TV a Kafar Sadarwa ta Zamani.

Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un Gobara ta tashi a Kasuwar Kara dake cikin birnin Sokoto.Allah Ya sauqaqa, Ya tsare ga...
22/01/2025

Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un

Gobara ta tashi a Kasuwar Kara dake cikin birnin Sokoto.

Allah Ya sauqaqa, Ya tsare gaba, Amin

FITAR KUTSUAdo Aleru Yayi Fitar Kutsu a Wani Harin da Yan Bindiga S**a kai Masa a Maboyarsa. 21/01/2025.Kasargumim Dan T...
21/01/2025

FITAR KUTSU

Ado Aleru Yayi Fitar Kutsu a Wani Harin da Yan Bindiga S**a kai Masa a Maboyarsa.

21/01/2025.

Kasargumim Dan Ta’addannan Ado Aleru Ya ranta a na kare inda yayi fitar kutsu a wani harin da jami’an Tsaron Sojojin Operation Fansar Yamma s**a kai masa a maboyarsa dake Munhaye dajin Danjibga dake karamar Huk**ar Mulki ta Tsafe.

Majiyar sirri sun tabbatarwa da Zagazola cewa Jami’an tsaron sunkai wannan hari ne a maboyar dan bindigar inda s**a jikkata da dama daga cikin yan bindigar sai dai ansamu labarin cewa Ado Aleru baya cikin wadanda wannan harin ya rutsa dasu wanda ana kyautata zaton yayi fitar burtu ne a lokacin da aka kai harin.

Jami’an Tsaron OPFY Sun tabbatar da cewa sun baza komar su don sanin inda dan bindagar ya shiga tare da shan alwashin sai sunga bayanshi da yardar Allah.

Muna Kira da su kara matsa kaimi Gada su gajiya har sai sunga bayan wadannan Azzalumai.

Ubangiji Allah Ya kara Ba’a Jami’an Tsaronmu Nasara.

An naɗa Saifullahi Muhammed a matsayin Kwamandan Hukumar Tsaron Dajin Najeriya shiyyar Arewa maso YammaHukumar Tsaron Da...
16/01/2025

An naɗa Saifullahi Muhammed a matsayin Kwamandan Hukumar Tsaron Dajin Najeriya shiyyar Arewa maso Yamma

Hukumar Tsaron Dajin Najeriya (NFSS) ta nada Saifullahi Muhammed, dan asalin karamar hukumar Kano Munincipal daga jihar Kano, a matsayin kwamandan shiyyar Arewa maso Yamma. Wannan nadin ya zo ne bisa jajircewarsa da ƙoƙarin sa wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiya a Najeriya.

Nadin wanda ya fara aiki daga ranar 13 ga watan Janairun 2025, ya samu amincewa tare da sanya hannun babban kwamandan Hukumar Tsaron Dajin Najeriya, Amb. Osatimeh Joshua, da Shugaban Kwamitin Amintattu, AIG (Rtd) E. E. Amakulor, k**ar yadda yake a doka ta 5, 6, karamin sashe na A da B na kundin tsarin mulkin Majalisar Hukumar Tsaron Dajin Najeriya.

A jawabinsa na karbar aiki, Saifullahi Muhammed, ya bayyana jin dadinsa bisa amincewar da shugabancin hukumar NFSS ta yi masa. Ya jaddada kudirin sa na ci gaba da inganta ayyukan hukumar a shiyyar Arewa maso Yamma.

“Abin alfahari ne gare ni da aka danƙa min wannan nauyi. Zan himmatu wajen inganta ayyukan Hukumar Tsaron Dajin Najeriya a shiyyar Arewa maso Yamma, kuma zan yi aiki ba tare da gajiyawa ba da duk masu ruwa da tsaki don tabbatar da cewa Najeriya ta zama wuri mafi aminci da zaman lafiya ga kowa da kowa.”

Da wannan nadin, Saifullahi Muhammed zai zama cikin sahun shugabanni masu hangen nesa da aka dorawa alhakin karfafa ayyukan tsaro a fadin Najeriya. Zai kuma inganta hadin gwiwa da al’ummomin yankin, hukumomin tsaro, da sauran masu ruwa da tsaki don kawo ƙarshen matsalolin tsaro a yankin.

Hukumar Tsaron Dajin Najeriya ta sake jaddada kudirinta na bada karfin gwiwa, karfafa tsaro da kuma bayar da gudumawa wajen samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a ƙasar nan.

11/01/2025

Ikon Allah

Allah jadada rahama ga Malan Jafar

Lallai Amurka na fuskantar barazana mai girma...Yayin da wasu yankunan ƙasar ke fama da tsananin sanyin dusar ƙanƙara. S...
11/01/2025

Lallai Amurka na fuskantar barazana mai girma...

Yayin da wasu yankunan ƙasar ke fama da tsananin sanyin dusar ƙanƙara. Sai ga wutar daji na babbake Los Angeles tun ranar Talata, wanda hakan ya janyo asarar rayuka, gidaje da dukiya mai yawa.

Kwatsam kuma jiya jaridar "The New York Times" ta ruwaito girgizar ƙasa a birnin San Francisco.

Ya wajaba su miƙe haiƙan da addu'o'i!

SAUKAR AL QU'RAN MAI GIRMAKaitsaye Daga Wajen Taron Saukar Alqur'ani Maigirma Ta Dalibai Mahardata Alqur'ani Su (54) da ...
08/01/2025

SAUKAR AL QU'RAN MAI GIRMA

Kaitsaye Daga Wajen Taron Saukar Alqur'ani Maigirma Ta Dalibai Mahardata Alqur'ani Su (54) da Kuma Masu Saukar Allo Su (150) A nan Makarantar Rahamaniyyah lil Tahfizul Qur'an Dake Khaulaha Bakin Kasuwa Kaura Namoda

Karkashin Jagorancin Khalifa Sheikh Mal. Kabiru Usman

08 January, 2025

25/12/2024

SHUGABAN KASA

Jin waɗannan kalamai a bakin shugaban ƙasa, abin tayar da hankali ne!

21/12/2024

MAKARANTUN ISLAMIYYA

A Makarantun ku na Islamiyya Kuna ko yawa yara yadda ake sallar Gawa a aika ce

Batun lantarki a Kaura Namoda Jinjina ta musamman ga Kungiyar Yan kasuwa ta Kaura Namoda karkashin jagorancin Alh Habibi...
13/12/2024

Batun lantarki a Kaura Namoda

Jinjina ta musamman ga Kungiyar Yan kasuwa ta Kaura Namoda karkashin jagorancin Alh Habibi.

Kungiyar Yan kasuwa ta Kaura Namoda sunyi tattaki harbzuwa ofishin KAEDCO da ke Gusau kuma sun gana da mahukuntan kamfanin na rarraba lantar ki a jihar nan, sun kuma yi masu bayani akan cewa WAI ana samun karamchin wutar ne daga Kainji, saboda haka wutar ba ta isa a raba ta ko ina.

Sai dai sun kulla wani alkawari da Yan kasuwar ta yadda za a samu dubarun da za a yi domin a rika samun wutar ko yaya ne a Kaura Namoda nan bada jimawa ba.

Sai dai a Kula, kowa ya kashe wutar Gidan ahi Ko ya cire fuse tunda an Dade ba a kawo ba Kar tazo ba a Sani ba ko akwai wata matsala a samun damuwa.

Akwai bukatar sauran kungiyoyi su shirya suna su tafi KO suyi tarayya da Kungiyar Yan kasuwa don a cimma nasara.

A.B.Kaura
Development Journalist
[email protected]

ZABA6AR KANSILAWannan Itace Zababbar Kansilar Mazabar Shinkafi Ta Kudu Dake Karamar Hukumar Shinkafi Ta Jihar Zamfara Ha...
20/11/2024

ZABA6AR KANSILA

Wannan Itace Zababbar Kansilar Mazabar Shinkafi Ta Kudu Dake Karamar Hukumar Shinkafi Ta Jihar Zamfara
Haj. Hadiza Shehu Shinkafi.

Wane Fata Zakuyi Mata ?

Daga Aliyu Abdulaziz madawaki kucheri 󱢏

WUTAR LANTARKI Wutar lantarki a Arewacin Najeriya ta sake lalacewa karo na goma 10 a cikin shekarar 2024 bayan ƙwanaki k...
05/11/2024

WUTAR LANTARKI

Wutar lantarki a Arewacin Najeriya ta sake lalacewa karo na goma 10 a cikin shekarar 2024 bayan ƙwanaki kaɗan da gyarawa k**ar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Ya lamarin yake a inda kuke ?

YARAN SUN SAKI ISKAR  YANCIJin jina ta musaman ga duk kanin lauyoyin da s**a tsaya akan zan cen yaran nan, da bayin Alla...
05/11/2024

YARAN SUN SAKI ISKAR YANCI

Jin jina ta musaman ga duk kanin lauyoyin da s**a tsaya akan zan cen yaran nan, da bayin Allah da s**a yi ɗawai niyar kai masu abinci da sutura da magani, da Malamai da shuwagabannin da s**a sa baki akan wannan lamari.

Allah ya biya kowa da Alhairi

04/11/2024

RANA TA UKU

Wurin Musabukar Karatun Al'Qur'ani Mai girma Matakin Karamar hukumar Mulki Kaura Namoda wurin Sanar da saka makon yan takar karu da s**a gabatar da Musabukar

Abdul-karim Suleman Kaura

RANA TA UKUDaga Wurin Musabukar Karatun Al'Qur'ani Mai girma Matakin Karamar hukumar Mulki Kaura Namoda Wada take cigaba...
04/11/2024

RANA TA UKU

Daga Wurin Musabukar Karatun Al'Qur'ani Mai girma Matakin Karamar hukumar Mulki Kaura Namoda

Wada take cigaba da guda na Yanzu haka A cikin Masalacin Juma'a na daya a garin Kaura Namoda

RANA TA BIYU Daga Wurin Musabukar Karatun Al'Qur'ani Mai girma Matakin Karamar hukumar Mulki Kaura Namoda Wada take ciga...
03/11/2024

RANA TA BIYU

Daga Wurin Musabukar Karatun Al'Qur'ani Mai girma Matakin Karamar hukumar Mulki Kaura Namoda

Wada take cigaba da guda na Yanzu haka A cikin Masalacin Juma'a na daya a garin Kaura Namoda

Abdul-karim Suleman Kaura

01/11/2024

Subhannallah

Waɗannan fa ba Bandit bane, ba kidnappers ba, ba kuma Ƴan Boko haram bane.

Matasa ne da yunwa da ƙuncin rayuwa ta addabesu s**a fito domin yin zanga zanga aka k**a su aka garƙamesu fiye da kwana 90 😭

Mafi yawancinsu yara ne ƙanana, kana ganinsu kasan suna fama da Yunwa da rashin kulawa!

Zaben shuwagabannin Kananan hukumomi a Jihar Zamfara.Kaura Namoda mu Kula Sosai Kar a Dauki Kara da  Kiyashi.Wata Kila s...
23/10/2024

Zaben shuwagabannin Kananan hukumomi a Jihar Zamfara.

Kaura Namoda mu Kula Sosai Kar a Dauki Kara da Kiyashi.

Wata Kila saboda Jin cewa za a baiwa Kananan hukumomin Mulki kudaden su aki TSAYE, Mutane da yawa sun fito neman kujerar chairman da kansiloli abun ma har da ban tsoro, bayan an gama tsuwwar Rashi Sai ga miliyoyin Kudi ana zubewa ana karbar fomafommai. Tau Muna fatan Alkahri ga masu kaunar Jama'a duk inda suke.

SHAWARA

Dimukuradiyya ta samu gundin zama a Nigeria, amma wasu Yan Nigeria din Suna yi mata Zagoj Kasa ta Hanyar kin Kula da tsarin da tazo da shi. Saboda haka akwai bukatar mu talakawa mu nunawa Yan siyasa mun San abunda mukeyi yanzu.

KU AUNA KOWANE DAN TAKARA A MIZANI NA CHANCHANTA

Kaura Namoda Babban Gari na Biyu Mafi girma a Jihar Zamfara idan ka cire Babban Birnin jihar, Muna Bukatar Nagartattun Mutane da su hai kujerar Chairman da Kansiloli.

Mu bibiyi tarihin kowane Dan takara mu samu bayanai akan ayyukan shi ko aika-aikar shi idan ya taba rike wani mukami. In bai taba rikawa ba mu Dubi yanayin taimakon da yayiwa Al'umma ko yadda yake Kula da su kafin yanzu.

Mu bukaci kowane su ya fadamana miye burin shi idan ya ci zabe, Kuma a bisa wane sharadi yake son takarar? Mu yiwa kan mu kiyamul-laili mu Gudu YAN JARI HUJJA.

Yan siyasa da keda alhakin zabar Yan takara Kuma Kunada nauyi da alhakin da ke kan ku ta Hanyar tsayawa tsakanin ku da Allah ku zabar ma talakawa Mutanen kirki, ba wadanda za Shafa maku Mai ga Baki ba idan Sun samu dama su koma wawurar kudaden Jama'a da Kwace Masu kayayyakin su da Hana masu hakkokan su, ko su mayar da dukiyar al'umma Ganima.

A Tsarin Siyasar wannan Zamani ana Bukatar Shugaba ya zama Mai Ilimi da sanin Mak**ar aiki da Dattako da Tausayin Jama'a da Girmama su.

MU KULA

Ba Garin KAURA NAMODA ba shi kadai bane Karamar hukumar Mulkin Kaura Namoda ba, akwai Sauran Garuruwa da Kauyukan da su ma ya dace a basu hakkin su Kuma a rika shigowa da su cikin al'amuran Mulki da duk abunda ya shafe su.

Dan Uwan ku, Abdulrazak Bello Kaura

18/10/2024

DAN TAKAR CHAIRMAN A KARAMAR HUKUMAR KAURA NAMODA

Muzammil Muhammed Idris

Inaji a jikina tarihi zai maimaita kanshi, yadda mahaifina ya kawo wutar lantarki Kaura nima zanyi sanadin gyara wutar lantarki a Kaura.

Abdul-karim Suleman Kaura

Address

Kaura-Namoda

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Kaura Namoda Online TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Kaura Namoda Online TV:

Videos

Share

Category