29/07/2024
Mukaddashin Gwamnan jihar katsina ya nemi Al,umma su kwantar da hankalin su akan maganar zanga-zangar da aka shirya ya Kuma bayyana kokarin da Gwamnatin takeyi domin magance matsalolin tattalin arziki.a jihar katsina,
Mukaddashin Gwamnan Jihar Katsina, Malam Farouk Lawal Jobe, ya yi kira ga al’ummar Jihar Katsina, musamman Mata da matasa, dalibai, da Yan kasuwa, da ’yan kungiyar kwadago da su shiga tattaunawa yafi ma’ana da gwamnati, maimakon shiga cikin Zanga-zangar da ake Neman yi a fadin kasar Nan,
Yache Gwamnati ta fahimchi irin kalubalen tattalin arzikin da ake fuskanta a yanzu duk da haka ina mai tabbatar muku da cewa gwamnati ta dukufa wajen aiwatar da matakan da za su rage wahalhalu da kuma samar da damammaki ga daukacin al’ummar jihar Katsina. Mukaddashin Gwamnan ya bayyana wasu muhimman tsare-tsare da aka fara: inda yache Mun kafa Asusun Ci gaba na MSME har Naira Biliyan 10 don tallafa wa sana’o’inmu na cikin gida,
Bugu da kari,” Mukaddashin Gwamnan yaci gaba da cewa, “muna bunkasa cibiyoyin gama-gari a dukkanin shiyyoyin Sanatocin mu guda uku, tare da mai da hankali kan sana’ar dinki, sana’o’in fata, , sarrafa noma, da ICT. da sana,oin hannu masu yawa Mun gyara tare da inganta Cibiyar Raya Masana’antu tare da farfado da Kauyen Sana’o’in Matasa na Katsina
Wato (+Katsina Youth Craft village+) domin koyon sana’o’i. don dogaro da Kai,
Mun Ƙaddamar da Dikko BDS Corp domin zai samar da mahimman ayyukan shawarwari na kasuwanci ga ƴan kasuwa masu tasowa bugu da ƙari, mun aiwatar da ƙidayar MSME da safiyo don Jagorantar ayyukanmu na gaba tare da samar da aikin yi ga Al,ummar Katsina don haɓaka guraben ayyukan yi, mun kuma samar da Asusun Tallafawa Lafiyar Jama’a miliyan ₦542 tare da haɗin gwiwar UNDP don taimakawa waɗanda abin ya shafa. ta hanyar kalubalen tsaro,
shirye-shiryenmu na horar da matasa masu koyon aikin kanikanci 3,000 da mata 10,000 a duk fadin kananan hukumomin, an riga an fara aiwatar da su don samar ma jama’armu sana’o’in dogaro da kai a nan gaba”. “Wadannan tsare-tsaren na nuna aniyarmu ta bunkasa tattalin arziki, samar da ayyukan yi, da inganta rayuwar daukacin mazauna Katsina inji Mukaddashin Gwamnan.
Mun aza harsashin samar da makoma mai inganci amma muna bukatar hakuri da hadin kai don samun nasara." Mukaddashin Gwamnan ya bukaci ‘yan kasa da su rika amfani da karfinsu wajen gudanar da ayyuka masu amfani kuma suyi amfani da damar da Allah ya Basu don ganin sun tabbatar da zaman lafiya Kuma Mu hada hannu domin gina jihar Katsina gaba dayanmu,
Mukaddashin Gwamnan ya kara da cewa, “Ya ku ‘yan uwana mazauna Katsina, muna kan wani muhimmin lokaci a tarihin jiharmu, kalubalen da muke fuskanta yanada matukar muhimmanci, ina kira ga kowa da kowa. matasanmu masu ƙwazo, mata Yan kasuwanmu masu himma, ƴan ƙungiyarmu, ta kwadago da duk wani mazaunin Katsina – da mu haɗa hannuwan mu don ciyar da jiharmu gaba "Maimakon zanga-zangar da farkon ta zamu Sani bazamu San karshe ta ba ina roƙon ku da ku shiga cikin waɗannan shirye-shiryen da muka sanya. Ku ziyarci KASEDA, ku bincika shirye-shiryen horarwa, ku ga yadda za ku ci gajiyar Asusun Ci gaban MSME. Mu canza bacin ranmu zuwa wani dalili don samun canji mai kyau,
Katsina jihar mu che mu kadai zamu Gina ta wasu bazasu zo daga wake su Gina Mamu ita ba sai dai suzo don su rusa ta
Mu taru mu gina Katsina don zaman lafiya da kwanchiyar hankaln yaran mu da dangin mu da iyayen mu
Fassarar 👉 Mustapha Ibrahim Kofar Marusa
Media Assistant to Katsina State Governor Ministry of Works Housing and Transport
Wallafar 👉 Ibrahima Kaulaha Mohammed sakataren watsa labarai na Gwamnatin jihar katsina 27 ga Yuli, 2024