06/09/2022
Ruwan Sama Ya Yi Sanadiyyar Kashe Mutum Biyar Da Lalata Gidaje 3,813 A Katsina
Mutum biyar ne s**a mutu sannan gida 3,813 s**a lalace sak**akon wani ruwan sama k**ar da bakin kwarya da aka yi a kananan hukumomi 13 da ke Jihar Katsina a Najeriya.
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Jihar ce ta bayyana haka ranar Litinin din nan.
A yayin da yake hira da manema labarai, kakakin hukumar, Malam Umar Muhammad, ya ce mutum uku sun mutu a karamar hukumar Kankara yayin da mutum biyu s**a rasu a Mai’adua.
Ya bayyana cewa gwamnatin Jihar tana yin dukkan abin da ya k**ata domin ambaliyar ruwa ba ta auku a jihar ba, yana mai cewa an kafa kwamitin gaggawa wajen ganin ba a fuskanci barkewar amai da gudawa ba.
Ya ce: “A Kankara, gidaje 176 sun rushe, a Danja kuma gida je 125 s**a lalace, sai kuma Kankia inda gidaje 86 s**a rushe, yayin da a birnin Katsina gidaje 620 s**a lalace, Musawa 482, Batagarawa 361, Kusada 311 yayin da Sabuwa gidaje 111 s**a rushe.
“A Zango, ruwan saman ya lalata gidaje 105, a Batsari, ya rusa gidaje 443, a Funtua gidaje 258 sun rushe, a Safana gidaje 581 sai kuma Ingawa kusan gidaje 154 s**a rushe.
“Kazalika gidaje 176 sun rushe yayin da mutum uku s**a rasu a ibtila'in a Kankara yayin da gidaje 154 s**a lalace a Ingawa.”