14/01/2025
Katsina Ta Gudanar da Taron Tattaunawa Don Bunkasa Fitar da Kayan kasuwanci zuwa kasashen Ketare
Katsina City News
Gwamnatin Jihar Katsina, ta hannun Hukumar Kula da Zuba Jari ta Jihar Katsina (KIPA), karkashin jagorancin Gwamna Malam Dikko Umar Radda, ta shirya taron yini guda domin karfafa masu fitar da kaya zuwa kasashen waje. Taron ya gudana a Babban dakin taro ta Munaj Event Center, inda aka tara manyan baki, masana harkar kasuwanci, da shugabanni na hukumomi domin duba hanyoyin bunkasa tattalin arziki mai dorewa.
Taron ya samu halartar manyan mutane da s**a hada da Kwamishinan 'Yan Sanda na Jihar Katsina, Shugaban Hukumar Kwastam ta Najeriya reshen Katsina, Shugaban Hukumar Shige da Fice ta Najeriya reshen Katsina, tsohon Gwamnan jihar Barno Abdulmumini Aminu Mai ritaya, shugabannin yan kasuwa masana, da wakilan hukumomi daban-daban.
A jawabinsa, Darakta Janar na KIPA, Ibrahim Tukur Jikamshi, ya bayyana muhimmancin tallafawa 'yan kasuwa na gida don samun damar shiga kasuwannin duniya. Ya ce, “Jihar Katsina tana da albarkatu masu tarin yawa k**ar amfanin gona, ma’adinai, da masana’antu. Wannan shirin zai ba da karin ilmi da dabaru na magance kalubalen da suke fuskanta k**ar karancin iya aiki, kasuwanni, da kudade.”
Jikamshi ya gode wa hukumomin da s**a tallafa wajen ganin taron ya samu nasara, ciki har da Hukumar Bunkasa Fitar da Kaya ta Najeriya (NEPC), Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Najeriya (NAFDAC), da hukumar Fitar da Kaya da Shigo da Kaya ta Najeriya (NEXIM). Ya ce, “Hadin gwiwarsu ta taka muhimmiyar rawa wajen ganin wannan shiri ya yi tasiri.”
Gwamna Malam Dikko Umar Radda, a jawabinsa, ya bayyana irin kokarin da gwamnatinsa ke yi wajen tabbatar da cewa Jihar Katsina ta kasance a sahun gaba wajen fitar da kaya zuwa kasashen waje. Ya ce, “Noma shi ne ginshikin manufofin tattalin arzikinmu. Mun zuba jari mai yawa wajen tallafawa manoma ta hanyar raba kayan noma, raya noman rani, da bunkasa darajar auduga da kiwo.”
Gwamnan ya kuma bayyana wasu manyan sauye-sauyen da gwamnatinsa ta kawo, k**ar kafa Hukumar Nauyin Kudi, aiwatar da tsarin fansho, da kara inganta al’amuran ilimi da lafiya. Ya kuma yi bayani kan gyaran hanyoyi, samar da ruwan sha, da bayar da tallafi ga masu 'yan gudun hijira.
A jawabinsa, Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Katsina ya yaba da shirin, yana mai cewa zai rage rashin aikin yi da kara tsaro a jihar. Shugabannin Hukumar Kwastam da ta Shige da Fice suma sun yi alkawarin tallafawa wajen magance matsalolin da masu fitar da kaya ke fuskanta.
Taron ya kunshi gabatarwar masana da hukumomi k**ar Hukumar Kula da Inganci ta Najeriya (SON), Hukumar Bunkasa Fitar da Kaya, da Bridge Shipment Inspection Agency, inda aka tattauna kan dabarun shiga kasuwannin duniya da kuma bunkasa tattalin arziki.
Daya daga cikin mahalarta taron ya bayyana cewa, “Wannan shiri ya ba mu dabaru masu mahimmanci don bunkasa fitar da kayayyakinmu.”
Gwamna Radda ya kammala taron da kira ga dukkan masu ruwa da tsaki da su hada kai don bunkasa fitar da kaya daga Jihar Katsina. Ya ce, “Tare, za mu iya kara yawa da kuma darajar kayan da muke fitarwa, ta yadda za mu kirkiri ayyukan yi da habaka masana’antu.”
Manyan abubuwan da s**a ja hankali da habaka taron sun hada da: Halartar manyan jami’an tsaro, shugabannin hukumomi, da masana harkar kasuwanci.
Mayar da hankali kan fitar da kayayyakin gona, Ma’adinai da sauran su, zuwa kasuwannin duniya.
Gyaran tsare-tsaren gwamnati don inganta harkokin kasuwanci.
Karfafa masu fitar da kaya da kayan aiki da dabarun da za su inganta harkokinsu.
Wannan rahoto ya nuna muhimmancin taron wajen bunkasa tattalin arzikin Jihar Katsina da kuma himmatuwar gwamnati wajen cimma burin ci gaba mai dorewa.