23/11/2024
Lado kazama hantsi leka gidan kowa
A cigaba da kokarin da mukeyi dan ganin cewa yakubu lado dan marke ya samu kuri’a a kowanne gida dake fadin jihar katsina a cikin shirin mu na “operation lado Gida-Gida “ a yau cikin ikon Allah wakilai na sun Kai Ziyara wajen shuwagabannin “MIYETTI ALLAH” reshen karamar hukumar Bakori dan ganin cewa suma sunzo sun bayar da Tasu gudunmuwar dan a fatattaki tsinstsiya a jihar katsina.A cikin jawabin shugabar mata ta kungiyar ta tabbatar mana da bamu goyon baya Dari-bisa-Dari dan ganin yakubu lado dan marke yazama sabon gwamnan jihar katsina a shekarar 2027 da karfin ikon Allah.