HK Media

HK Media Media/News, Entertainment and Da'awah
(19)

Abdulmajid Mukhtar Yankaba Ya rubutaIna matukar farin ciki da wannan rana Mai dinbin tarihi a rayuwata Kakata shekarar t...
11/01/2025

Abdulmajid Mukhtar Yankaba Ya rubuta

Ina matukar farin ciki da wannan rana Mai dinbin tarihi a rayuwata Kakata shekarar ta 76years a duniya ta sabke alqurani Mai girma anyi walima yau a madarasatul hidayatul auladin muslimina Kaura namoda, Allah yakara maki lafiya Kakata💖💝💕💓
Gata Uwar Mumunai
Gata Mahaddacciyar Alqurani
Gata Retirement
Allah yakarama Diyanki da Jikokinki Albarka

08/01/2025

Bayar da Waqafin Islamiyya da Alh. Sanusi Ahmad Tijjani Ajiwa

08/01/2025

Rabon Zakkar kayan noma a Gundumar Ajiwa

An gudanar da walimar murna da fatan alheri ga Hon Hon. Abdurkadir Mamman Nasir (Chief of Staff) Shugaban ma’aikatan fad...
07/01/2025

An gudanar da walimar murna da fatan alheri ga Hon Hon. Abdurkadir Mamman Nasir
(Chief of Staff) Shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar Katsina a gidan marayu na Atta’awun Islamic Foundation dake unguwar Dandagoro Katsina.

An gudanar da walimar ne a karkashin jagorancin Dr. Ahmad Musa Abdullahi, daga cikin mahalarta akwai Sheik Yakubu Musa Hassan Katsina yan uwa da abokan arzuki.

Hon. Abdulkadir Mamman Nasir ya bayyana cewa Allah yana linkawa mutane linkin dukiyar da s**a bayar wajen taimakawa marayu, domin yin hakan na kara kusanci da Allah ya kuma kara daga darajar mutane ta hanyar da ba suyi tsammani ba. Ya kara da cewa hakika taimakon marayu yanada nasaba wajen samun nasarar da nayi a rayuwa kuma ya bukaci addu’o’i daga wajen yara da iyayensu mata dake a wannan gida ga gwamnatin jihar Katsina da sauran al’umma.

A karshe an gudanar da addu'a ta musamman ta fatan samun nasara ga wannan matsayi da Allah ya bashi.

07/01/2025
07/01/2025

WALIMA DA YARA MARAYU DOMIN FATAN ALHERI GA HON. ABDULKADIR NASIR {CHIEF OF STAFF KATSINA STATE}

29/12/2024

Shirya kayan sa wa (Tufafi) na fita Da'awah da za'ai a ranar Laraba 1 /1/2025

29/12/2024

Taron bikin shekara daya da kuma karrama wasu bayin Allah da Gidauniyar Hillside Charitable Foundation s**a shiryq

28/12/2024

Daura a garin Katsina kwamitin matasa na jibwis Jihar katsina tare da hadin guiwa da kwamitin Daawa na mal Abdulwahab Kano, na gayyatar yan uwa Musulmi zuwa wajen Daura da Muhadara ta yini daya. Mai taken (Alkurani baya fassaruwa saida Hadisin Manzon Allah SAW)

Wadda zaa gabatar kamar haka: Rana: Lahadi 29/12/24 Da safe daura daga karfe 10:00am zuwa karfe 2:00pm wuri masallacin jumaa na filin kanada sai Lecture da dare 8:00pm zuwa 10:00pm wuri Masallachin Government printing

Malamai Masu Yin Daurah:

1- Malam Anas Assalafi: Tarihin kafuwar su.
2- Malam Muhd Salis Almisriy: Warwarar wasu daga cikin shubuhohin su.
3- Malam Murtadha Anna'isi: Wajabcin aiki da abinda ya tabbata daga Annabi (S.A.W.)

Malamai Masu Lakcar Dare:

1- Malam Muhd Khamis Zakariyya.
2- Dr. Salim Usman.
3- Malam Abdallah Abdulwahhab.
4- Malam Musa Dankwano.
5- Dr. Ibrahim Assudani

26/12/2024

FATHU DIMASHQ
Tarihin Kasar Syria da halin da ta ke ciki a yanzu
Muna farin cikin gayyatar yan uwa musulmi zuwa MUHADARA mai take a sama wadda za ta kasance kamar haka:
Malamai
1. Mal. Haruna Sani Muhammad
2. Ustaz Abdallah Muslim Ibrahim
Bakon da zai yi musharaka damu
Ustaz Abdurahman Muhd Sani
Rana: Alhamis 26/12/2024
Lokaci: Magrib - Isha'
Wuri: Masallacin Ta'awun Gabasawa, Katsina

FATHU DIMASHQTarihin Kasar Syria da halin da ta ke ciki a yanzuMuna farin cikin gayyatar yan uwa musulmi zuwa MUHADARA m...
25/12/2024

FATHU DIMASHQ
Tarihin Kasar Syria da halin da ta ke ciki a yanzu

Muna farin cikin gayyatar yan uwa musulmi zuwa MUHADARA mai take a sama wadda za ta kasance kamar haka:

Malamai
1. Mal. Haruna Sani Muhammad
2. Ustaz Abdallah Muslim Ibrahim

Bakon da zai yi musharaka damu
Ustaz Abdurahman Muhd Sani

Rana: Alhamis 26/12/2024

Lokaci: Magrib - Isha'

Wuri: Masallacin Ta'awun Gabasawa, Katsina

Za ku iya kallon Facebook Live a HK Media ko Ta'awun Tv and Radio

Sanarwa
HK Media

Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun A yau mun tashi da rasuwar Alh. Bature Kofar Bai Mahaifin ga su Faisal Bature Abubaka...
25/12/2024

Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun

A yau mun tashi da rasuwar Alh. Bature Kofar Bai Mahaifin ga su Faisal Bature Abubakar Abubakar Bature.
Wannan bawan Allah shine ya bayar da babban filinsa aka gina gidajen Marayu na Atta'awun Islamic Foundation (Majalisin Juma'a). Muna rokon Allah ya karbi wannan sadaka ta shi Allah kumabya gafarta masa.
Janaza karfe 11 na safe a gidansa dake Kofar Bai

23/12/2024
Kungiyar Rayuwar Mata ta Nijar ta Rabawa Iyalai 200 Tallafin Abinci a MaradiDaga Mukhtar A. Halliru Tambuwal, Sokoto Ƙun...
23/12/2024

Kungiyar Rayuwar Mata ta Nijar ta Rabawa Iyalai 200 Tallafin Abinci a Maradi

Daga Mukhtar A. Halliru Tambuwal, Sokoto

Ƙungiyar Inganta Rayuwar Mata Musulmi ta Association Islamique Rayuwar Mata ( A.I.R.M) da ke tallafawa mata zawarawa da marayu da mabuƙata a Jamhuriyyar Nijar ta raba abinci ga mutane 200 da aka zaƙulo daga waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa a kwanakin baya.

An ƙaddamar da rabon abincin ne a makarantar Raudatul Ibadurrahmane da ke garin Maraɗi, a Jamhuriyar Nijar ƙarƙashin jagorancin shugabar Ƙungiyar Malama Khadejar Abubacar.

Shugabar ta bayyana cewa, "Wannan tallafi an samo shi ne da haɗin gwiwar wata baiwar Allah da ke zama a Dubai ta hannun wani shiri na kungiyar 'Big Up Project' da ke ƙarƙashin Shugabar Ƙungiyar Melani."

Shugabar ta ƙara da cewa, an raba shinkafa kilo 25, man girki lita 2, katon ɗin taliya da zanin rufa, kasancewar an shiga lokacin sanyi.

Yayin da shugabar take yabawa waccea ta bada gudunmawar ta yi kira ga waɗanda s**a amfana da su yi amfani da shi yadda ya dace. Sannan ta buƙaci Gwamnati da ta ƙara ƙarfafawa matasa gwiwa ta hanyar koya masu ƙananan sana'o'i don su samu abin dogaro ga kansu ba sai sun jira an ba su ba.

Ta yi godiya ga Gwamnan Maraɗi bisa goyon bayan da yake ba su a duk lokacin da buƙatar hakan ta taso.

Gwamnan Jihar Maraɗi, Babban Kwantirolan 'Yansanda Issoufou Mamman, ya yabawa ƙungiyar bisa goyon bayan da take bai wa Gwamnati, sakamakon kiran da take yi kan kowa ya yi nasa ƙoƙarin wajen taimakawa al'umma, a maimakon barin Gwamnati kaɗai ga aikin jinƙan al'umma.

Wasu da s**a amfana sun yi godiya ga wadda ta taimaka da kuma ƙungiyar Rayuwar Mata, da ta yi wannan ƙoƙarin. Sun bada tabbacin yin amfani da abin da aka raba musu yadda ya dace, tare da kira ga masu hali da s**a ƙara taimakawa kasancewar akwai mabuƙata a cikin al'umma da yawa.

Taron ya samu halartar mambobin ƙungiyar da sauran al'ummar Maraɗi daga ɓangarori daban-daban.

Ita dai wannan ƙungiya na ƙoƙarin ganin an tallafawa al'umma musamman mabuƙata, inda take faɗi tashin ganin an samo masu ɗauki daga ciki da wajen ƙasar.

Address

Katsina

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when HK Media posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to HK Media:

Videos

Share