Flash News Hausa

Flash News Hausa Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Flash News Hausa, Media/News Company, Katsina, Katsina.

Wace jiha ce a Najeriya tafi kusa da Jamhuriyar Nijar?
19/11/2023

Wace jiha ce a Najeriya tafi kusa da Jamhuriyar Nijar?

Saleh Boko, ɗalibi a jami'ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU) da ke Bauchi. Anyi ittifaki duk Nijeriya babu ɗalibin da ya k...
19/11/2023

Saleh Boko, ɗalibi a jami'ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU) da ke Bauchi. Anyi ittifaki duk Nijeriya babu ɗalibin da ya kai Saleh Bada himma da nacin karatu.

Dalilin Mutuwar Auren Jarumar Kannywood,  Aisha TsamiyaDaga Mukhtar Yakubu AUREN fitacciyar jarumar Kannywood A’isha Ali...
19/11/2023

Dalilin Mutuwar Auren Jarumar Kannywood, Aisha Tsamiya

Daga Mukhtar Yakubu

AUREN fitacciyar jarumar Kannywood A’isha Aliyu Tsamiya ya daɗe da mutuwa, a binciken da mujallar Fim ta yi.

Mutane sun daɗe su na raɗe-raɗi kan idan auren ya mutu ne saboda irin hotunan da ake ganin ta na sakawa a TikTok masu nuna kamar ita ba matar aure ba ce; yadda ta ke saka sautin waƙoƙin Kannywood, ta na bi ta na rerawa ya haifar da kokwanto game da matsayin auren nata.

Binciken da Majiyar Focus News Hausa mujallar Fim ta yi a ‘yan kwanakin nan ya tabbatar da mutuwar auren.

Wata majiya mai tushe ta kurkusa da jarumar ta shaida mana cewa auren ya mutu tun a watanni uku zuwa huɗu da su ka gabata.

Majiyar ta ƙara da cewa mutuwar auren “ba wani abin mamaki ba ne saboda irin yadda su ka daɗe su na kai ruwa rana ita da mijin ta.”

Majiya ta ce: “An daɗe ana zaman doya da manja a tsakanin ta da mijin. Ba a yi ma zaton auren zai kawo lokacin da su ka rabu ɗin ba saboda tun farkon auren matsalar ta fara kuma ta rinƙa ci gaba, wanda hakan ya haifar da wasu matsaloliin daga baya wanda su kaɗai su ka sani, sai dai kuma Allah.”

Majiyar ta ƙara da cewa: “Babbar matsalar da na sani a game mutuwar auren A’isha Tsamiya da mijin ta ita ce, ta na zargin sa da yin soyayya da wasu matan da ita kuma ta ke ganin hakan ba zai yiwu ba. Hakan ya haifar da rigingimu a tsakanin su lokaci zuwa lokaci har daga ƙarshe dai da matsalolin su ka taru su ka yi yawa, abin ya kai ga rabuwa.”

A bara, mujallar Fim ta ba ku labarin cewa an ɗaura auren A’isha Muhammad Ali (Tsamiya) da wani mutum mai suna Alhaji Buba Abubakar a ranar Juma’a, 25 ga Fabrairu, 2022 a Masallacin Malam Aminu Ibrahim Daurawa da ke Kano, akasin inda katin gayyatar ɗaurin auren ya nuna, wato masallacin Sheikh Zarban da ke Kwanar ‘Yan’awaki, a ‘Yankaba, Kano.

Ba a yi wani biki ba, sannan sanin ko waye ta aura ya kasance babban sirri wanda ta yi ta nuƙu-nuƙun ɓoyewa har zuwa yau ɗin nan.

A yanzu da auren ya mutu, ba a sani ba ko A’isha Tsamiya za ta koma harkar fim ne ko a’a. Amma dai ta ci gaba da kasuwancin da ta saba yi a baya na tallar zannuwa da sauran kayayyakin ƙawa na mata.

Ta taɓa mallakar shago a Khairat Plaza da ke daura da sakatariyar NYSC da ke unguwar Janbulo a Kano.

ALLAHUMMA SALLI ALA SAYYIDINA MUHAMMADIN WASALLIM WA'ALA ALIHI WASAHABIHI WASALLIM
19/11/2023

ALLAHUMMA SALLI ALA SAYYIDINA MUHAMMADIN WASALLIM WA'ALA ALIHI WASAHABIHI WASALLIM

Yau Shekaru 6 Kenan Da Zargin Maryam Sanda Da Kashe Mijinta A Rana Mai K**ar Ta Yau 19 Ga Watan Nuwamba 2017 Aka soma za...
19/11/2023

Yau Shekaru 6 Kenan Da Zargin Maryam Sanda Da Kashe Mijinta

A Rana Mai K**ar Ta Yau 19 Ga Watan Nuwamba 2017 Aka soma zargi Maryam sanda da laifuka biyu da s**a haɗar da kashe mijin nata Bilyaminu Bello.

A watan Disamban 2017 ne aka gurfanar da Maryam Sanda bisa zargin kisan mijin nata.

A lokacin da yake yanke hukuncin, alƙalin ya ce an samu dukkanin wasu shaidu da s**a tabbatar da cewa Maryam ce ta aikata wannan laifi.

Ya kuma yi watsi da iƙirarinta na cewa mijin nata ya faɗi ne kan fasasshiyar tukunyar Sh**ha, abin da ya janyo mutuwar tasa.

Ya kuma bayyana cewa hujjojin da aka gabatar sun gamsar da kotu cewa ta caka wa mijin nata wuƙa ne yayin da faɗa ya kaure a tsakaninsu

A lokacin da alƙali ya zartar da hukuncin wadda ake tuhuma ta yi ƙoƙarin rugawa domin guduwa daga zauren kotun sai dai jami'an tsaro sun riƙe ta.

Daga Saliadeen Sicey

MASHA ALLAH : An samar da sabuwar na'urar dan adam a masallacin harami na makkah, ita naurar duk abinda ka tambayeta zat...
19/11/2023

MASHA ALLAH : An samar da sabuwar na'urar dan adam a masallacin harami na makkah, ita naurar duk abinda ka tambayeta zata amsa maka cikin sauki da sauri. | Allah Ya karawa Annabi Daraja.

HOTO: 📸 Amjad Ibrahim wakilin ATP na kasar Saudiyya

INNALILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UNHaziƙin Sojan Najeriya Ya Rasu Sakamakon Haɗarin Mota A KatsinaAllah Ya Yi Wa Haziƙin ...
19/11/2023

INNALILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN

Haziƙin Sojan Najeriya Ya Rasu Sakamakon Haɗarin Mota A Katsina

Allah Ya Yi Wa Haziƙin Matashin Sojan Najeriya, Kabir Auwalu Rasuwa Sakamakon Haɗarin Mota Da Ya Rutsa Da Shi Akan Hanyar Katsina Zuwa Kano, Jiya Asabar.

An Yi Jana'izarsa K**ar Yadda Addinin Musulunci Ya Tanada A Unguwar Hajj Camp, Cikin Garin Katsina.

Allah Ya Jikansa Da Rahama!

Karin wasu sabbin hotunan Amarya kuma matashiyar Likita Na'ima Idrís Allah  yaba da zaman lafiya da Zuri'a Dayyaba!
18/11/2023

Karin wasu sabbin hotunan Amarya kuma matashiyar Likita Na'ima Idrís

Allah yaba da zaman lafiya da Zuri'a Dayyaba!

KACICI-KACICI: Ya Sunan Wannan Bawan Allah Kuma Sana'ar Mi Yake?
18/11/2023

KACICI-KACICI: Ya Sunan Wannan Bawan Allah Kuma Sana'ar Mi Yake?

Mai Martaba Sarkin Kano Na 14 Khalifa Muhammadu Sanusi II Ya Karɓi Baƙuncin Sheikh M***i Menk A Gidansa Dake Legas, Yau ...
18/11/2023

Mai Martaba Sarkin Kano Na 14 Khalifa Muhammadu Sanusi II Ya Karɓi Baƙuncin Sheikh M***i Menk A Gidansa Dake Legas, Yau Asabar

Sabon Hoton Amarya Kuma Matashiyar Likita Na'ima Idrís Allah Ya Ba Da Zaman Lafiya Da Zuri'a Dayyaba!
18/11/2023

Sabon Hoton Amarya Kuma Matashiyar Likita Na'ima Idrís

Allah Ya Ba Da Zaman Lafiya Da Zuri'a Dayyaba!

Yadda auran wani matashi ɗan shekara 17 da amaryarsa 'yar shekara 16 ya tayar da hankalin gwauraye da tuzuran yanar gizo...
18/11/2023

Yadda auran wani matashi ɗan shekara 17 da amaryarsa 'yar shekara 16 ya tayar da hankalin gwauraye da tuzuran yanar gizo.”

Allah yaba da zaman lafiya da Zuri'a Dayyaba!

Kashi 95 Cikin Ɗari Na Ƴan Najeriya, Yunwa Ce Matsalar Su, Cewar Dakta Babangida Rumah
18/11/2023

Kashi 95 Cikin Ɗari Na Ƴan Najeriya, Yunwa Ce Matsalar Su, Cewar Dakta Babangida Rumah

Ya sunan wannan Film din ?
18/11/2023

Ya sunan wannan Film din ?

Yadda hukumar NSCDC ke karbar horo a helkwatarsu dake birnin tarayya Abuja.
18/11/2023

Yadda hukumar NSCDC ke karbar horo a helkwatarsu dake birnin tarayya Abuja.

Kacici-Kacici: Waye zai iya fada mana Mutane nawa ne a cikin wannan Hoton ?Yau Zamuga Masu Lafiyar Ido 👀
18/11/2023

Kacici-Kacici: Waye zai iya fada mana Mutane nawa ne a cikin wannan Hoton ?
Yau Zamuga Masu Lafiyar Ido 👀

Ubangiji Madaukakin Sarki Bai Taba Yin Wata Ni'ima Ga Mutanen Dake Rayuwa Aban Qasa Ba, Face Aiko Da Annabi Muhammad (SA...
18/11/2023

Ubangiji Madaukakin Sarki Bai Taba Yin Wata Ni'ima Ga Mutanen Dake Rayuwa Aban Qasa Ba, Face Aiko Da Annabi Muhammad (SAW) A garesu.

Shiyasa Babban Masoyin Annabi (Saw) Yake Cewa;-

*مواهب رب العرش طه محمد # ورحمته وهو الرحيم فأكرما*
Allah Yaqara Tsira Da Aminci Ga Annabin Rahama Da Iyalan Gidansa Tsarkaka Tare Da Sahabban Ababan Shiryarwa, Ameen.

~ Fatima Abdulhadi Hotoro

INNALILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UNMun Samun Labarin Rasuwar Farfesa Yusuf Yakubu Gamzago Na Jami'ar Ahmadu Bello Dake Za...
18/11/2023

INNALILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN

Mun Samun Labarin Rasuwar Farfesa Yusuf Yakubu Gamzago Na Jami'ar Ahmadu Bello Dake Zaria.

Allah Ya Yi Wa Farfesa Yusuf Yakubu (Turakin Danejin Katsina) Na Sashen Nazarin Siyasa A Jami'ar Ahmadu Bello Dake Zaria Rasuwa A Daren Jiya Juma'a, Bayan Gajeruwar Rashin Lafiya.

Za A Yi Jana'izarsa A Gidansa Dake Layin Liman Sa'idu, Sabon Layi A Garin Funtua, Jihar Katsina Da Misalin Karfe 11:00 Na Safiyar Yau Asabar.

Muna Roƙon Allah Ya Jikansa Da Rahama!

Yadda ɓarayi s**a sace duk sabbin ƙofofin da aka saka tare da kwanon da aka yi Rifi a Makarantar firamare ta Bello Aliyu...
18/11/2023

Yadda ɓarayi s**a sace duk sabbin ƙofofin da aka saka tare da kwanon da aka yi Rifi a Makarantar firamare ta Bello Aliyu dake Kofar Doka Zariya Jihar Kaduna.”

TUNATARWA : FARILLAN ALWALA GUDA BAKWAI NE DON ALLAH KARKA WUCE BAKA TSAYA KA KARANTA BA.           FARILLAN ALWALA GUDA...
18/11/2023

TUNATARWA : FARILLAN ALWALA GUDA BAKWAI NE DON ALLAH KARKA WUCE BAKA TSAYA KA KARANTA BA.

FARILLAN ALWALA GUDA 7 NEH:
1. Niyya
2. Wanke Fuska
3. Wanke hannaye zuwa gwiwar hannu
4. Shafar kai
5. Wanke kafafuwa
6. Cuccudawa
7. Gaggautawa

SUNNONIN ALWALA

• Wanke hannaye zuwa wuyan hannu
• Kurkure baki
• Shaka ruwa
• Fyacewa
• Juyo da shafar kai
• Shafar kunnuwa
• Sabunta ruwa agaresu
• Jeranta tsakanin farillah

MUSTAHABBAN ALWALA

• Yin bismillah
• Goga asuwaki
• Kari akan wankewa ta farko a fuska da hannaye
• Farawa daga goshi
• Jeranta sunnoni
• Qaranta ruwa a nisa gabobi
• Gabatar da dama kafin hau.

AKAN FASALIN ALWALA

• Wanda ya manta da wata farilla daga gabobinsa, idan ya tuno sai ya aikata ta da abunda ke bayanta, idan kuma yayi nisa sai ya aikata ta ita kadai, ya kuma sake abunda ya sallata bayan faruwar abun.

• Idan kuma ya bar sunna, to saiya aikata ta ita kadai bazai sake sallah ba.

• Wanda kuma ya mance lam'a sai ya wanke ta ita kadai da niyya, in kuma har yayi sallah by an faruwar hakan toh sai ya sake ta

• Wanda ya tuna da kurkurar baki ko shaqa ruwa bayan ya rigaya ya fara wanke fuska, to bazai dawo gare su ba har sai ya gama alwalarsa, sannan sai yayi su

• Tsettsefe 'yan yatsu hannuwa yana wajaba, an so a tsettsefe 'yan yatsun qafafuwa, tsefe gemu mara dubu yana wajaba acikin alwala, tsefe gemu yana wajaba acikin wanka koh da mai duhu neh.

AKAN FASALIN ALWALA (2)

• Babu yana halatta ga wanda bashi da alwala yayi sallah, koh dawafi, koh ya taba al qur'ani koda acikin gafakarsa neh, bada hannunsa ba saidai idan *juzu'i* neh ga mai neman ilimi acikinsa.

• Yaro a wajen taba al qur'ani kamar babba yake, amma laifin yana wuyan wanda ya bashi al qur'anin ya taba.

• Wanda yayi sallah da gangan ba tare da alwala ba toh shi kafiri neh. Allah yakiya she mu.

(Hafizahullah)

18/11/2023

Cikakken Jawabin Gwamnan Kano Engr. Abba Kabir Yusuf Kan Hukuncin Kotun Appeal Na Yau Juma'a.

Daga Dokin Karfe Tv

Yadda Haɗin Gwiwar Jami'an Tsaro Dake Aiki A Kano S**a Gudanar Da Tattaki Domin Ƙara Wayar Da Kan Jama'a Kan Muhimmancin...
17/11/2023

Yadda Haɗin Gwiwar Jami'an Tsaro Dake Aiki A Kano S**a Gudanar Da Tattaki Domin Ƙara Wayar Da Kan Jama'a Kan Muhimmancin Zaman Lafiya, Yau Juma'a

Bari muga masu lafiyar ido. Me aka rubuta?
17/11/2023

Bari muga masu lafiyar ido. Me aka rubuta?

MASHA ALLAH : Wani bawan Allah kenan a birnin Zariya tare da 'ya'yansa 5 duk cikar su 'yan mata da s**a samu damar hadda...
17/11/2023

MASHA ALLAH : Wani bawan Allah kenan a birnin Zariya tare da 'ya'yansa 5 duk cikar su 'yan mata da s**a samu damar haddace Al'Qur'ani maigirma.”

Abun mamaki ba ya karewa a duniya. Yadda ‘yan kasar Kongo ke amfani da katako wajen kera wani nau’in keke mai suna Tchuk...
17/11/2023

Abun mamaki ba ya karewa a duniya. Yadda ‘yan kasar Kongo ke amfani da katako wajen kera wani nau’in keke mai suna Tchukudus wajen daukar kayayyaki da mutane.

Daga CGTN Hausa

Sunusi Musa (SAN) kenan babban lauya wanda ya wakilci ACP a Shari'ar Kano.
17/11/2023

Sunusi Musa (SAN) kenan babban lauya wanda ya wakilci ACP a Shari'ar Kano.

YANZU-YANZU: Kotu ta kori karar Gwamna Abba ta tabbatar da Dr. Nasiru Yusuf Gawuna, a matsayin halastaccen zababban Gwam...
17/11/2023

YANZU-YANZU: Kotu ta kori karar Gwamna Abba ta tabbatar da Dr. Nasiru Yusuf Gawuna, a matsayin halastaccen zababban Gwamnan jihar Kano.

Me za ku ce?

Duk Hukuncin Da Kotun Ɗaukaka Ƙara Ta Zartar A Yau Za Mu Karɓa Domin Allah Shine Mai Yadda Ya So, Kuma Mun Yarda Da Kadd...
17/11/2023

Duk Hukuncin Da Kotun Ɗaukaka Ƙara Ta Zartar A Yau Za Mu Karɓa Domin Allah Shine Mai Yadda Ya So, Kuma Mun Yarda Da Kaddara, Cewar Nasiru Gawuna

YANZU-YANZU: Jarumin Finafinan Hausa Abale Ya samu karuwar Ƴa mace.
16/11/2023

YANZU-YANZU: Jarumin Finafinan Hausa Abale Ya samu karuwar Ƴa mace.

Janar Buratai (Mai Ritaya) Zai Maka Shirin 'Idon Mikiya' A Kotu Daga Bello Hamza, AbujaA halin yanzu Tsohon Shugaban Run...
16/11/2023

Janar Buratai (Mai Ritaya) Zai Maka Shirin 'Idon Mikiya' A Kotu

Daga Bello Hamza, Abuja

A halin yanzu Tsohon Shugaban Rundunar Sojojin Nijeriya, Ambasada, Laftanar Janar Tukur Yusufu Buratai (mai ritaya), ya ba gidan watsa labarai na ‘Vision Media Services Limited’ masu shirin Idon Mikiya wa’adin kwana 7 na su janye kage da bata suna da s**a yi masa a cikin shirnsu na mako-mako mai suna, Idon Mikiya da aka watsa ranar 5 ga watan Nuwamba 2023 aka kuma maimaita a ranar 6 ga watan Nuwamba 2023 a tashar talabijin na Farin Wata.

Buratai, ya bayyana haka ne takardar da lauyoyinsa, Yunusa, Umaru & Co s**a rubuta ranar 13 ga watan Nuwamba 2023. Sun zarge su da yin furuce-furuce na bata suna, karya da cin mutumcu ga Mai Girma Ambasada Buratai.

Takardar ta kuma bayyana cewa, an jawo hankalinsu ne a kan shirin mako-mako na Idon Mikiya na ranar 5 ga watan Nuwamba 2023 aka kuma maimaita a ranar 6 ga watan Nuwamba 2023 an kuma nuna shirin ne a tashar Farin Wata aka kuma yada a kafafen sadarwa na kamfanin.

Takardar ta kuma kara da cewa, bayanan da aka yi a cikin shirin karya ne tsagwaronsa kuma cin mutumci ne an kuma yi ne da nufin bata wa Buratai suna, sunan da ya yi shekaru yana tattalinsa. Shirin ya yi hannun riga da abin daya faru a taron da tsofaffin daliban Jami’ar Ibadan s**a shiya a ranar Juma’a 3 ga watan Nuwamba 2023.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa, tun da aka watsa shirin Buratai nata karvar sakonnin ta waya da sauran kafafe daga ‘yan uwa da abokan arziki suna neman sanin gaskiyar maganganun da aka watsa a cikin shirin.

A kan haka aka nemi masu gudanar da kamfanin su janye shirin tare da buga jawabin ban hakuri a manyan jaridun Nijeriya 3 ciki har da kafar watsa labaran su a cikin kwanaki 7.

DA DUMI - DUMI: Na karɓi sammacin Kotu, amma har Mahadi ya bayyana a busa ƙaho bazan ƙaryata kaina ba, AmdazJarumi kuma ...
16/11/2023

DA DUMI - DUMI: Na karɓi sammacin Kotu, amma har Mahadi ya bayyana a busa ƙaho bazan ƙaryata kaina ba, Amdaz

Jarumi kuma mawaƙi a masana'antar shirya finafinan Hausa ta Kannywood, Abdallah Amdaz, ya ce ya karɓi sammacin kotu kuma zai bita da Hasbunallahu Wani'imal Wakeel, amma dai yace daga yanzu har Mahadi ya baiyana a busa ƙaho, bai ga kotu ko wani Ɗan Adam da ya isa ya saka shi ƙaryata abin da ya faɗa a kan wasu daga cin ƴan Fim ba.

Shi dai jarumi Abdullahi Amdaz yace mafi yawan yan film su na Promoting ɗin abubuwa uku ne, wasu karuwánci, wasu káwalci, wasu kuma ɗaukaka.

Mé zakú cé?

ABIN A YABA: Ya Buɗe Shagon Ba Da Magani Kyauta Ga Yara Marayu Mata Da Kuma Shagon Ba Da Likkafani KyautaShahareren dan ...
16/11/2023

ABIN A YABA: Ya Buɗe Shagon Ba Da Magani Kyauta Ga Yara Marayu Mata Da Kuma Shagon Ba Da Likkafani Kyauta

Shahareren dan kasuwa a garin Jega dake jihar Kebbi, Alh Tukur Wasoso Jega ya bude shaguna guda biyu na magani da likkafani ga mata da yara kanana a kyauta ba kosisin mutum. Duk wanda rashin lafiya ta shafa zai zo a auna shi a ba shi magani kyauta.

Allah Ya saka mai da mafificin alheri, amin.

DAGA AKILU BALA JEGA (ABJ)

16/11/2023

Malamai Zasu Tsayawa Abdullahi Amdaz Ga Duk Wanda Yayi Masa Barazana, Kan Tona Asirin Ƴan Fim

Mé zakú cé?

16/11/2023

WATÁ SABÚWA: Ya K**ata Hukumar Hizbah Ta Fara K**a Karuwai Maza Wáɗanda Suké Zuwà Ana Kwánciya Dasu Ana Biyán Su Kuɗi, Céwar Babiana.

Mé zakú cé?

Ma'ajiyar Alkur'ani dake masallacin harami na makkah | Allah ya karawa Annabi Daraja HOTO: Amjad Ibrahim wakilin ATP na ...
16/11/2023

Ma'ajiyar Alkur'ani dake masallacin harami na makkah | Allah ya karawa Annabi Daraja

HOTO: Amjad Ibrahim wakilin ATP na kasar Saudiyya

A Najeriya Ɗan Daudun da Ya Sauya Halitta ya Koma Mace na Neman Taimako bayan Tiyatar Dashen Ɗuwawun da aka masa Ya zo d...
15/11/2023

A Najeriya Ɗan Daudun da Ya Sauya Halitta ya Koma Mace na Neman Taimako bayan Tiyatar Dashen Ɗuwawun da aka masa Ya zo da Gardama

Wani shahararren ɗan Daudu a Najeriya mai suna Hau Boogie na neman taimakon 'yan Najeriya inda ya buƙaci su tara masa kuɗi domin ceton rayuwarsa, ya ce ba ya son ya mutu.

Ɗan daudun ya shiga halin ni 'yasu ne, bayan da ya sauya halitarsa zuwa na tsaleliyar budurwa, sai dai an sami akasi ne a lokacin da aka yi masa titatar dashen ɗuwawu, inda aikin yazo da gardama har ta kai ga ya koma sanya pampas, yan zu haka yana roƙon 'yan Najeriya su tara masa kuɗi domin ceton lafiyarsa.

15/11/2023
t babur allhaji baba hema🚭

“Har abada bazan sake yiwa mata kwalliya a yayin ɗaukar fim ba” - Mansur Make-up Mai sana'ar ƙwalliya a masana'antar shi...
15/11/2023

“Har abada bazan sake yiwa mata kwalliya a yayin ɗaukar fim ba” - Mansur Make-up

Mai sana'ar ƙwalliya a masana'antar shirya finafinan Hausa ta Kannywood, Mansur Make-up, ya ce ba zai sake yiwa Mata ƙwalliya a yayin ɗaukar fim ba, domin ya gane cewa hakan kuskure a Addinin musulunci da kuma al'ada, wanda a baya Mutane da dama sun nusar dashi hakan, amma yana ganin kamar ba masu ƙaunarsa bane, sai yanzu ya fahimci gaskiya.

Mansur ya bayyana haka ne ranar Laraba cikin wani fefen bidiyo, wanda yayi tsokaci akan kalaman jarumi Abdallah Amdaz bisa yadda yake fuskantar ƙalubale daga abokan sana'arsa, bayan wasu kalamai da ya furta a ranar Litinin din da ta gabata a hukumar Hisbah.

Majiya: Mansur Make-up

YANZU YANZU : Yanzu haka ruwan sama ke sauka a birnin Katsina. Ya abun yake a yan kunan ku?
15/11/2023

YANZU YANZU : Yanzu haka ruwan sama ke sauka a birnin Katsina.

Ya abun yake a yan kunan ku?

Jihar legas tana ci gaba da amsa sunan ta na duk faɗin Nijeriya ba wata jiha ɗaya tilo da ta yi mata fintinkau wurin tsa...
15/11/2023

Jihar legas tana ci gaba da amsa sunan ta na duk faɗin Nijeriya ba wata jiha ɗaya tilo da ta yi mata fintinkau wurin tsaruwa kyau da kai ka ce ba Nijeriya ba ce.”

Mawaƙi Abdul K**al Ya Maka BBC Hausa A Kotu, Yana Menan Diyyar Miliyan 120Mawaki Abdul K**al na neman diyyar miliyan 120...
15/11/2023

Mawaƙi Abdul K**al Ya Maka BBC Hausa A Kotu, Yana Menan Diyyar Miliyan 120

Mawaki Abdul K**al na neman diyyar miliyan 120 daga Sashen Hausa na BBC kan amfani da kidan wakarsa ba da izininsa ba

Wani mawakin Hausa mai suna Abdul K**al ya maka Sashen Hausa na BBC a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Kano bisa zargin amfani da kidan wakarsa ta ‘Maryamu’ ba da izininsa ba.

Lauyan mawakin, Barista Bashir Ibrahim Umar ya shaida wa kotun cewa BBC suna amfani da kidan wakar Abdul a shirin su mai suna ‘Daga Bakin Mai Ita’ ba tare da izininsa ba, wanda hakan ke iya janyo masa matsala a harkar sana’arsa.

“Kasancewarsa mawaki mai tasowa, hakan na iya zama matsala gare shi domin wasu za su yi zaton shi ne ya dauki kidan daga BBC don neman shuhura ko wani abu makamancin hakan,” in ji lauyan nasa.

Don haka lauyan ya nemi kotun da ta dakatar da kafar BBC daga ci gaba da amfani da sautin kidan, ya kuma nemi kotun da ta tilasta BBC biyan Abdul K**al diyyar Naira miliyan 120.

Sai dai lauyan BBC, Barista Shakirudden Mosobalage ya mayar da martani cewa BBC ta sayi sautin kidan ne daga hannun wani kamfani da ke zaune a Abuja.

Barista Shakirudden Mosobalage ya kuma roki kotun da ta ba su dama su gabatar mata da wasu takardu, rokon da kotun ta amince da shi.

Alkalin kotun, Mai sharia. N. M. Inusa ya dage sauraron shari’ar zuwa ranar 12 ga watan Disamba

Address

Katsina
Katsina
FLASHNEWSHAUSA

Telephone

+2348036411514

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Flash News Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Videos

Share