HFN Hausa Fox News

HFN Hausa Fox News Wannan shafin na HFN Hausa Fox News mun bude shi don kawo labaran hausa

Wannan ginin shine yafikowane gini tsawo a duniya.  Shin akwai wanda zai iya fadamin sunanshi.???
25/02/2024

Wannan ginin shine yafikowane gini tsawo a duniya. Shin akwai wanda zai iya fadamin sunanshi.???

Uwargidan Tsohan Shugaban Kasa, Hajia Aisha Buhari Ta Cika Shekara 53 Da Haihuwa A DuniyaWace Irin Fata Za Ku Yi Mata?
18/02/2024

Uwargidan Tsohan Shugaban Kasa, Hajia Aisha Buhari Ta Cika Shekara 53 Da Haihuwa A Duniya

Wace Irin Fata Za Ku Yi Mata?

MUSULUNCI YA SAMU KARUWA;Wata Baiwar Allah Mai Suna Serah Ta Karbi Addinin Musulunci A Wurin Maulana Sheikh Dahiru Usman...
18/02/2024

MUSULUNCI YA SAMU KARUWA;

Wata Baiwar Allah Mai Suna Serah Ta Karbi Addinin Musulunci A Wurin Maulana Sheikh Dahiru Usman Bauchi RA A Yau Talata A Gidansa Dake Bauchi, Inda Ta Canza Sunanta Daga Serah Zuwa Sayyada Aisha.

Allah Ya Tabbatar Da Ita Kan Wannan Addini Na Musulunci.

Tuni dai aka take wasa tsakanin Najeriya da Ivory Coast.Ko mene ne hasashen ku?
11/02/2024

Tuni dai aka take wasa tsakanin Najeriya da Ivory Coast.

Ko mene ne hasashen ku?

Yadda sojan Najeriya Yaji Rauni Yayin Da Motar Manjo Janar Ta Taka Wani Bam Da Bøkø H@r@m S**a Dasa A Yobe
07/02/2024

Yadda sojan Najeriya Yaji Rauni Yayin Da Motar Manjo Janar Ta Taka Wani Bam Da Bøkø H@r@m S**a Dasa A Yobe

An k**ashi da shanu 55 da tumaki 6 a Garin Karaye.Isah Lawal, Dan Shekaru 33, Dan Ta'adda ne dake zaune a kauyen Kaya, K...
07/02/2024

An k**ashi da shanu 55 da tumaki 6 a Garin Karaye.

Isah Lawal, Dan Shekaru 33, Dan Ta'adda ne dake zaune a kauyen Kaya, Karamar Hukumar Giwa, Jihar Kaduna. An k**ashi da shanu 55 da tumaki 6 a Garin Karaye, bayan ya baro Dajin Birnin Gwari da yunkurin kafa sansanin garkuwa da mutane a daji tsakanin Gwarzo da Karaye dake Jihar Kano.

Mafi Yawan 'Yan Nijeriya Suna Ganin Ina Da Hannu A Tsadar Rayuwar Da Suke Ciki, Alhali Ni Na Fi Su Shan Wahalar Tsadar R...
06/02/2024

Mafi Yawan 'Yan Nijeriya Suna Ganin Ina Da Hannu A Tsadar Rayuwar Da Suke Ciki, Alhali Ni Na Fi Su Shan Wahalar Tsadar Rayuwa, Cewar Dangote

INNALILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UNYar Siyasar Farko Da Aka Taɓa Zaba A Jihar Jigawa, Mai Dankwali Ta RasuAllah ya yi wa ...
05/02/2024

INNALILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN

Yar Siyasar Farko Da Aka Taɓa Zaba A Jihar Jigawa, Mai Dankwali Ta Rasu

Allah ya yi wa Hajiya Fatima Shahada (Mai Ɗankwali) rasuwa.

Hajia Fatima Shahada ita ce Mace ɗaya tilo a tarihin jihar Jigawa da ta taɓa zama zaɓaɓɓiyar Kansila, a shekarar 1999 a jam'iyyar ANPP da shekarar 2017 a jam'iyyar APC, a mazaɓar Yayari ƙaramar hukumar Hadejia.

Allah Ya Jiƙanta Da Rahama!

BARI NA FADA MUKU GASKIYA✊Duk iskancin da namiji da mace zasuyi a karshe burin kowa ya auri nagari, saidai shi na miji h...
05/02/2024

BARI NA FADA MUKU GASKIYA✊

Duk iskancin da namiji da mace zasuyi a karshe burin kowa ya auri nagari, saidai shi na miji hakan bai zame mishi wahala, domin iskanci a jikinshi k**ar qura ce, yana karkabewa zai koma pes, kuma har ya auri diyar masu mutunci.

Amma mace fa? Ita iskanci a gareta ya wuce qura da zata karkabe, ya koma tabo da baxai goguba, shiyasa dayawan masu wannan hali suke karewa a posting hotuna da videon su na ban tausayi suna bayyana neman miji ko wane iri da rantsuwar zasuyi zaman lafiya amma mazan basa yadda, ciki kuwa hadda abokan lalacewarsu.

Mata suna rayuwa a doron duniya a misalin yadda kifaye ke rayuwa cikin ruwa, suna tare qugiya zai shigo da tana suna ribibin zuwa ci, wanda ya riga k**awa suna kallo za'a janyoyi ya zama nama, amma bazai hana idan an mayar da qugiyar wasu su biyoshi ba.

Dakin da wata tayi jinyar HIV har ta mutu a dakin wata ta k**a haya a matsayinta na student kuma ta ci gaba da irin rayuwar waccan.

Duk wanda HIV yak**a bafa mun fishi wayau bane, yadda ake amfani da condom suma sunayi, amma haka Allah ya fasa condom din ta inda basuyi tinaniba domin yana da hanyoyi uncountable na k**a mabarnata.

A rayuwar iskanci macece baki da riba saidai uban asara, kina ba wani jin dadi bayan bakya sha'awarsa sai ya tada miki, kina bashi jin dadin s*x ke kina jin zafi, kina sashi fita cikin hayyacinshi ke kina kuka.

Kin ci amanar Allah, kanki, iyayenki, mijinki da zaki aura, da 'ya'yanki? Inda mahaifiyarki tayi irin iskancin da kk yi tayi miki adalci? To ke da kk yi kinwa yaranki adalci?

Wllh alhaki kwikwiyo yakan bi mai shi, iyayenki ba mazinata bane duk iskancin da kk bazai shafesu ba iya kanki zai tsaya.

Ya Allah karabamu da irin wa'yannan matayen, kasa sukuma su gane.

Ministan kasa a ma’aikatar tsaron Nijeriya Bello Matawalle ya gana da ministocin tsaro na kasashen Musulmi da ke cikin k...
03/02/2024

Ministan kasa a ma’aikatar tsaron Nijeriya Bello Matawalle ya gana da ministocin tsaro na kasashen Musulmi da ke cikin kungiyar IMCTC, inda ya tattauna hanyoyin da Nijeriya za ta kara hada kai da kasashen Musulmi wajen yaki da ‘yan bindiga.

Gwamnan jihar Jigawa ya karawa ma'aikatan jihar Naira dubu 10k ga kowane ma'aikaci, domin rage musu radadin halin da ake...
02/02/2024

Gwamnan jihar Jigawa ya karawa ma'aikatan jihar Naira dubu 10k ga kowane ma'aikaci, domin rage musu radadin halin da ake ciki.

Gwamnan Jihar Zamfara, Dakta Dauda Lawal Dare A Lokacin Da Ya Ke Sarawa Uwargidansa, Hajia Huriyya A Wajen Bikin Kaddamm...
02/02/2024

Gwamnan Jihar Zamfara, Dakta Dauda Lawal Dare A Lokacin Da Ya Ke Sarawa Uwargidansa, Hajia Huriyya A Wajen Bikin Kaddammar Da Rundunar Askarawan Jihar Zamfara.

Meza kuce game da hakan?

YANZU-YANZU: Naira ta fara daraja, yanzu ta koma N1,400 kan duk Dalar Amurka daya a kasuwar bayan fage.Me zaku ce?
02/02/2024

YANZU-YANZU: Naira ta fara daraja, yanzu ta koma N1,400 kan duk Dalar Amurka daya a kasuwar bayan fage.

Me zaku ce?

Bayan Zanga-Zangar Lumana, Masu Sana’ar Gurasa a Kano Sun Bayyana Dalilan su na Tafiya Yajin AikiDaga Rahama Umar kwaru ...
02/02/2024

Bayan Zanga-Zangar Lumana, Masu Sana’ar Gurasa a Kano Sun Bayyana Dalilan su na Tafiya Yajin Aiki

Daga Rahama Umar kwaru

Kungiyar matan dake yin gurasa a jihar kano ta bayyana cewa tsadar da Fulawa ta yi ya tisalta musu dole su dakatar da Aikin su har sai abun da hali yayi ko kuma idan Mahukunta sun shiga cikin maganar.

Tsadar fulawar da muke aiki da ita ta yi yawa, kullum muka je siya sai anyi mana karin akalla Naira dubu daya da dari biyar , yanzu maganar da nake yi muku muna siyan Fulawa sama da Naira dubu 40 to ya zamu yi”.

Shugabar kungiyar masu yin gurasa ta jihar kano Fatima Auwal Chediyar yan gurasa ce ta bayyana hakan yayin wata zanga-zangar lumana da s**a gudanar a a safiyar yau juma’a.

Tace mafi yawancin su duk zawarawa ne suna gudanar da Sana’ar ne domin su rufawa kansu asiri, amma yanzu sana’ar tana neman gagara saboda rashin jari sak**akon tsadar da fulawa ta yi.

” A baya masu sayar da fulawar suna bamu bashi idan mun sayar mu basu kuɗin su, amma yanzu duk sun daina saboda tsadar da fulawar ta yi, to ya ilahi ina zamu sa Kanmu”.

” Muna gudanar da wannan zanga-zangar ne domin mu nunawa shugabannin mu halin da muke ciki, kuma kasuwancinmu na talakawa ne saboda idan s**a ga yadda muke Sana’ar wallahi ba za su iya ba, Muna cikin masifa fulawar da muke aiki da ita tafi karfinmu”.

Fatima Auwal ta bukaci shugabannin a matakai daban-daban da su dubi halin da suke cikin na tsadar fulawa su taimaka musu saboda yawa ‘ya’yan da suke da su, ga shi kuma da wannan Sana’ar s**a dogara wajen ciyar da ya’yan da kuma biya musu kudin makaranta.

Matan dai sun ce dole su hakura da yin gurasar saboda basu da jarin da zasu sayi fulawar, kuma yin hakan wata babbar barazana ce ga al’umma musamman masu karamin karfi wadanda ba sa iya siyan biredi.

Mala'ikan Mutuwa Mai Daukar Ran Dan Adam Shi Kansa Bai San Ranar da Mutum Zai Mutu ba Sai Sauran Lokaci Kadan Sannan All...
02/02/2024

Mala'ikan Mutuwa Mai Daukar Ran Dan Adam Shi Kansa Bai San Ranar da Mutum Zai Mutu ba Sai Sauran Lokaci Kadan Sannan Allah ya Sanar Da shi
Cewa Je ka Dauko Ran Wane Tsarki ya Tabbata A Gare shi – Ya Bayyana Cewa Dukkan Bayi Zamu Koma Gare shi, Kuma Zai Saka wa, Kowane Mutum da Abinda ya Cancanta,
Ya ce : "Lalle ne Zuwa Gare Shi Makõmarmu Take Gabã Daya, Wa'adin Allah Gaskiya ne.

Wato Zuwa ga Allah – Maɗaukakin Sarki Shi Kaɗai ne Mai Iko Akan Komawar mu, Baki Daya Bayan Mutuwa Domin Ya yi Mana Hisabi A Kan Ayyukanmu, Allah
Ya yi Alkawari Kuma Alkawarin Allah Gaskiya, Kuma Allah Ba zai Warware Alkawarinsa ba.
Allah yasa Mucika da Imani Duniya da Lahira

Juma'at Mubarak Yan Uwana Musulumi

DA ƊUMI-ƊUMI: Jami'ar KUST, Kano ta kirkiri 'Mutum-mutumin' da zai rika shara da goge-gogen ofisoshiShugaban jami'ar Pro...
02/02/2024

DA ƊUMI-ƊUMI: Jami'ar KUST, Kano ta kirkiri 'Mutum-mutumin' da zai rika shara da goge-gogen ofisoshi

Shugaban jami'ar Prof Musa Yakasai ya ce tuni an gwada wannan mutum-mutumi, kuma yana aiki yadda ya dace.

Kungiyar Kare 'yancin Musulmi ta Nageriya (MURIC) ta soki kwamitin da gwamnatin Filato ta nada don warware rikicin Mangu...
02/02/2024

Kungiyar Kare 'yancin Musulmi ta Nageriya (MURIC) ta soki kwamitin da gwamnatin Filato ta nada don warware rikicin Mangu

Kungiyar kare 'yancin Musulmi a Najeriya, MURIC ta zargi gwamnanatin jihar Filato da nuna wariya da kyama ga al'ummar Musulmi saboda rashin sanya musulmi ko daya a cikin kwamitinta na tsaro da ta hada mai mutum 11 domin warware rikicin kabilanci a garin Mangu da kewaye.

A ranar Laraba ne dai gwamnan jihar Filato, Caleb Manasseh Mutfwang ya nada kwamitin na tsaro na mutum goma sha daya domin nemo bakin zare dangane da yadda rikicin kabilanci ya dabaibaye al'ummar a 'yan watannin nan.

Shugaban kungiyar ta MURIC, Farfesa Ishaq Akintola a wata sanarwa ga manema labarai "akwai alamar tambaya a ce kwamiti mai mutum 11 amma babu sunan Musulmi ko daya alhali kuma a cikin kabilun da ake rikicin da su a kwai Musulmi. Wannan ya nuna cewa da wuya a yi adalci."

Sai dai gwamnatin jihar Filato ta ce mutane ba su fahimci ainihin aikin komitin ba ne, inda ta musanta zargin nuna wariyar da ake yi mata.

LABARIN MUTUWA!!!😭😭😭😭😭😭😭😭 Dan Allah Albarkacin yau juma'a ka tsaya ka karanta dan Allah ko masu ladan tare dakai Wata ra...
02/02/2024

LABARIN MUTUWA!!!😭😭😭😭😭😭😭😭
Dan Allah Albarkacin yau juma'a ka tsaya ka karanta dan Allah ko masu ladan tare dakai

Wata rana Manzon Allah (saww) ya shigo Masallacinsa sai ya tarar da wasu Mutane suna ta zance suna dariya.

Sai yace musu: "Amma da ace kuna tunowa da Mai yanke jin dadi (Mutuwa) da wannan ya shagaltar daku daga wannan abinda nake gani.

Ku yawaita Ambaton mutuwa domin wallahi babu wata rana da zata wuce fache sai QABARI (yayi ma kansa kirari) yana cewa:

"NINE GIDAN BAQUNTAKA! NINE GIDAN KADAITAKA!! NINE GIDAN TURBAYA!! KUMA NINE GIDAN TSUTSOTSI!!"

Idan aka zo binne Mumini acikin Qabarinsa, sai Qabarin yace masa:

"MARHABAN WA AHLAN.. WALLAHI KA KASANCE DAGA CIKIN MAFI SOYUWAR MUTANE AGARENI ACIKIN MASU TAFIYA ADORON QASA..

YANZU IDAN AN BINNEKA ACIKINA, NINE SUTURARKA NI ZAN AIKATA MAKA SAKAMAKON IRIN ABINDA KA KASANCE KANA AIKATAWA NE".

Nan take za'a fadada masa Qabarinsa har iyakar ganinsa, Kuma za'a bude masa Qofa zuwa gidansa na Aljannah.

Amma idan akazo za'a binne Kafiri ko Fajiri (Mai aikata manyan laifuka) Sai Qabarinsa yace masa:

"BA'A MARABA DAKAI, KUMA BA'A MURNA DA ZUWANKA.

KUMA WALLAHI KANA DAGA CIKIN MUTANEN DA NAFI QINSU DAGA MASU TAFIYA ADORON QASA.

YAU ZA'A BINNEKA ACIKINA, NINE SUTURARKA, KUMA ZAN AIKATA MAKA SAKAMAKON IRIN AYYUKAN DAKA KASANCE KANA AIKATAWA".

Nan take sai Qabarin ya matseshi, har sai Qasusuwan hakarkarinsa sun shige cikin junansu.

(Sai Manzon Allah ya sanya yatsunsa cikin junansu -abisa misali).

Sannan za'a turo masa wasu Manyan MACIZAI GUDA SABA'IN (MASU MIYAGUN KAMANNI).

DA ACE 'DAYAN CIKINSU ZAI HURA QASAR DUNIYAR NAN DA BAKINSA, DA HAR ABADA DUNIYAR NAN BA ZATA TA'BA TSIRO DA CIYAWA BA.

ZASU YI TA SARANSA, SUNA CIZONSA HAR ZUWA LOKACIN DA ZA'A TAFI FILIN HISABI."

- Imam Tirmizy ne ya fitar da Hadisin. sannan Ibnul Jawzy ma ya kawoshi acikin babi na biyu acikin littafinsa mai suna AHWALUL QUBOUR.

Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un!!
Ubangiji Allah yabamu ikon aikata Alkhairi

Address

Sabon Gida
Katsina
820101

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when HFN Hausa Fox News posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to HFN Hausa Fox News:

Videos

Share


Other Broadcasting & media production in Katsina

Show All