Flash News Hausa

Flash News Hausa Media News Company

23/05/2025
Fitaccen malamin addinin Musulunci, a jihar Bauchi, mabiyin darikar Tijjaniyya, Sheikh Junaid, yayi karin haske ga mutan...
05/04/2025

Fitaccen malamin addinin Musulunci, a jihar Bauchi, mabiyin darikar Tijjaniyya, Sheikh Junaid, yayi karin haske ga mutane musulmai masu murna da mutuwar Musulmi ɗan uwansu.

Malamin ya bayyana cewa, "Ko maƙiyinka ne ya mutu, abin mamaki ya tabbata ga mutumin da ke murnar mutuwar wani, domin kai ma wata rana zaka bi hanyar da yabi ita ce (mutuwa) .
— Inji Imam Junaidu Bauchi.

Sakataren kungiyar Izala ta kasa  Sheikh Kabiru Haruna Gombe, ya mika sakon ta'aziyyar rasuwar Sheikh Dr. Idris Abdulazi...
04/04/2025

Sakataren kungiyar Izala ta kasa Sheikh Kabiru Haruna Gombe, ya mika sakon ta'aziyyar rasuwar Sheikh Dr. Idris Abdulaziz Bauchi.

Tare da addu'ar Allah yayi masa rahama, Malamin ya bayyana cewa "Allah ka jikan Dr Idris Abdulazeez Dutsen Tanshi, ka kyautata makwancin sa, ka haɗamu da shi a gidan aljanna firdausi ranar gobe. Allah ka kai haske kabarinsa, Ka gafarta masa kurakuransa, Ka sanya Aljannah ce makomarsa, Ka kyautata bayansa, ka bawa iyalansa dangana ameen.

KALLO YA KOMA SAMA: Tabbas Bala Lau Dan Damfara ne, Amma ba Ɓarawo Bane  — Sheikh Sani Yahaya Jingir.A wani faifan bidiy...
03/04/2025

KALLO YA KOMA SAMA: Tabbas Bala Lau Dan Damfara ne, Amma ba Ɓarawo Bane — Sheikh Sani Yahaya Jingir.

A wani faifan bidiyo dake zaga kafafen sada zumunta musamman na Facebook, an jiyo shugaban Izala reshen Jos Shaikh Sani Yahaya Jingir na kiran shugaban izala bangaren kaduna daya tuba ya dena damfarar mutane tare da daina safarar ‘yan mata zuwa kasar Saudiyya saboda neman kudi.

Sai dai an jiyo Sheikh Jingir yayi 'mi ara koma baya' inda yake kalubalantar dan bello kan wani faifan bidiyo daya saki a ranar Sallah karama bayan kammala azumin watan Ramadan inda ya zargi shugaban da hada baki da gwamnati wajen wawuran kudaden talakawa inda ya bayyana asusun bankuna na Sheikh Bala Lau sama da 30.

Sai dai wani abinda ya dauki hankalin yan Najeriya shi ne, yanda wasu mabiyan sheikh Bala Lau din ke kalubalantar dan bello da kuma kiraye-kirayen a kauracewa saurarensa kasancewar sa karen farautar yahudawa daya zabi ya batawa malamai magadan Annabawa suna.

Wasu yan Najeriya na kiraye kirayen da ya kamata mabiyan Bala lau su karyata dan bello ne da hujja ba zage-zage ba, kasancewarsu makusanta da addini, wanda zagi bai dace dasu ba.

Kalaman jirgir na nuni da cewa yanzu lokaci yayi da ya kamata su hada kai da juna tare da kauracewa aibata juna, saboda hanyar da irinsu Dan bello s**a dauko ta tone tone bazata haifar da da mai ido ba, kamar yadda jaridar ta Rariya Online ta bankado.

Jaridar Rariya Online zata cigaba da farauto abubuwan dake faruwa domin nemo maku irin hadakar da ya kamata kungiyoyin suyi domin kaucewa barazanar baraka dake shirin kunno kai daga makiya addini a fadin Najeriya.

Abin jira a gani yanzu shi ne yanda zata kaya tsakanin masu kare addini da masu kokarin ganin sun tona masu asiri a idon mabiyansu.

A naku nazarin, ko mene ne banbanci tsakanin barawo da dan damfara?

DDL Hausa

INNALILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN Ƴanta'adda Sun Dira Har Cikin Gidansa Sun Yi Masa Kisan Gilla A Abuja Wasu ƴan Ta'add...
03/04/2025

INNALILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN
Ƴanta'adda Sun Dira Har Cikin Gidansa Sun Yi Masa Kisan Gilla A Abuja

Wasu ƴan Ta'adda sun yi kisan gilla ta hanyar sara da s**a, a cikin gidan wannan ɗan agaji mai suna Malam Khalid Adamu, Sakataren kuɗi na Majalisar agaji ta "Lugbe Division" wanda ke yankin (FCT) Abuja a tarayyar Najeriya.

Allah Ya Jikansa Da Rahama!

KAJI RABO: Sojojin Najeriya, tare da hadin gwiwar kamfanin sadarwa na Briech UAS, sun kaddamar da jiragen yaki na farko ...
03/04/2025

KAJI RABO: Sojojin Najeriya, tare da hadin gwiwar kamfanin sadarwa na Briech UAS, sun kaddamar da jiragen yaki na farko kuma mafi girma da aka kera a cikin gida Najeriya, A cewar babban jami'in, kalar wannan jirgi mara matuki na iya ɗaukar bama-bamai yayi tafiya mai dogon zango da shi, don tunkarar makiya.

Jarumar Fina-finan Kudancin Najeriya Ihuoma Sonia Uche ta wallafa wadannan hotuna a shafinta na Facebook don yi wa masoy...
01/04/2025

Jarumar Fina-finan Kudancin Najeriya Ihuoma Sonia Uche ta wallafa wadannan hotuna a shafinta na Facebook don yi wa masoyanta barka da Sallah. Sai dai Jarumar ta rubuta cewa, za a iya kiranta da suna Aisha.

WATA SABUWA: Ƙungiyar Izala Za Ta Maka Dan Bello A Kotu Kan Kan Zârĝìñsa  Da Ya Yi Wa Shugabanta, Shêikh Bala Lau Kaźàfì...
31/03/2025

WATA SABUWA: Ƙungiyar Izala Za Ta Maka Dan Bello A Kotu Kan Kan Zârĝìñsa Da Ya Yi Wa Shugabanta, Shêikh Bala Lau Kaźàfì

Me za ku ce?

JIYA DA YAU KENAN: Yadda ake duban watan Azumin Ramadan a shekarun baya, da kuma yanzu. |Allah ya karawa Annabi Daraja
30/03/2025

JIYA DA YAU KENAN: Yadda ake duban watan Azumin Ramadan a shekarun baya, da kuma yanzu. |Allah ya karawa Annabi Daraja

Hajiya Safara'u Mahaifiyar Gwamnan jihar katsina Dikko Umar Radda ya rasu kamar yadda Katsina Reporters ta ruwaito.
23/03/2025

Hajiya Safara'u Mahaifiyar Gwamnan jihar katsina Dikko Umar Radda ya rasu kamar yadda Katsina Reporters ta ruwaito.

CIKIN HOTINA: Sheikh Prof. Ibrahim Ahmad Maqari, Ya Rufe Tafsir Na Watan Ramadan Da Yammacin Yau Laraba, a Babban Masall...
20/03/2025

CIKIN HOTINA: Sheikh Prof. Ibrahim Ahmad Maqari, Ya Rufe Tafsir Na Watan Ramadan Da Yammacin Yau Laraba, a Babban Masallacin Kasa Dake Babban Birnin Tarayya Abuja.

Address

Katsina

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Flash News Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share