FADA A TSAKANIN JAGORORIN YAN BINDIGA DADI NA JIHAR ZAMFARA. DA KATSINA YAYI, AJALIN ALHAJI BALDI KAMAR YADDA RAHOTON BBC HAUSA YA BAYYANA
Video Sanata Dandutse Da Marigayi Umaru Musa Siyasar Su Iri Daya Ce Idan Suka Tashi Yin Alkairi Sunayine Dan Allah Ne Cewar Hon. Murtala Muhammad Malamiyya Funtua Ya Bayyana Haka Ne Yayin Tattaunawar Shi Da Tashar (Maf Ku Kalli Cikakken Video a Channel Din Mu Na Youtube Mai Suna Dandutse Media Reporters, Katsina Media Reporters
Bantaba ganin mutumin da baya jin kunya irin Rarara ba.😲
Yan sanda sun kama dattijon da yayi lalata da ƙananan raya a jihar Katsina
An bayar da rahoton mutuwar mutane da dama tare da jikkata sakamakon harin da Isra’ila ta kai a sansanin ‘yan gudun hijira na Jabalia mai cunkoson jama’a a Gaza. Jamilu Garkuwan Dandutse Dandume
Rundunar 'Yan Sanda na Jihar Kano ta kama wani Dan Damfara - Abdullahi Haruna Kiyawa
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu A jawabin da ya gabatar ta kafafen yaɗa labarai a yammacin yau ya bayyana yadda gwamnati ta shirya antayo maƙudan kuɗaɗe ta fannoni da dama domin ragewa mutane raɗaɗin gyaran karayar tallafin mai da ake ciki a halin yanzu. Ga kaɗan daga cikin tanade-tanaden:
1. Bawa manyan masu masana'antu 75 jari mai rangwame har na naira biliyan ɗaya kowannen su. Wanda za su biya a tsahon watanni 60.
2. Masu matsaƙaita da ƙananan sana'o'i za su amfana da naira biliyan 125 domin haɓɓaka jarinsu.
3. Daga cikin waccan biliyan 125 gwamnati za ta bada ja'iri kyauta (mai haɗe da ƙa'ida) na naira 50,000 ga masu ƙananan sana'o'i mutum 1,300 a kowace ƙaramar hikima.
4. Sauran biliyan 75 za su tafi wajen masu matsaƙaitan sana'o'i inda za a bawa mutum 100,000 rance mai rangwame na naira 500,000 zuwa miliyan ɗaya wanda za su biya a hankali cikin shakara uku.
5. Tunda sai da ruwan ciki ake janyo na rijiya, Shugaban Ƙasa ya bada umarnin fito da abinci har ton 200,000 tare da takin zamani ton 225,000 domin rabawa ga mabuƙata.
5. Nan ba da jimawa ba gwamnati za ta samar da ƙananan moticin bus masu amfani da gas har guda 3,000 domin kawo rangwame a kuɗin sufuri da jama'a ke fama da shi. Waɗannan motoci za a raba su ne ga kamfanonin sufuri domin gudanar da su.
6. Haka nan kuma gwamnati ta ware maƙudan kuɗaɗe domin noma hekta 500,000 a ɓanagarori daban-daban na ƙasar nan. Baya ga samar da abinci wannan shiri zai samarwa da matasa marasa aikin yi sana'a ta wucin-gadi.
A ƙarshe, ga waɗanda suka saurari cikakaken jawabin za su ji yadda Shugaba Tinubu ya nuna tausayawa da halin da ake ciki, ya bada haƙuri, ya kuma sha alwashin ƙawo ƙarshen wannan yanayi cikin gaggawa da taimakon Allah.
Matashin da ya rataye kansa a wani kauye, Gargadi: wannan bidiyo yana dauke da hoton gawa a bayyane .
Mataimakin shugaban kasa Kashima Shettima ya isa birnin St. Petersburg na kasar Rasha domin wakiltar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
Jamilu Garkuwan Dan-dutse Dandume
Mataimakin shugaban kasar zai bi sahun sauran shugabannin siyasa da 'yan kasuwa a wajen taron koli na Rasha da Afirka karo na 2 da kuma dandalin tattalin arziki da jin kai na Rasha da Afirka da ke mai da hankali kan dabarun inganta dangantakar da ke tsakanin Rasha da nahiyar Afirka da dai sauransu.
Har ila yau, mataimakin shugaban kasa Shettima zai halarci tarukan kasashen biyu da wakilan manyan jami'an gwamnatin kasar Rasha da abin ya shafa da kuma shugabannin 'yan kasuwa domin tattauna dangantakar da ke tsakanin Rasha da Najeriya.
Ya samu tarba daga Jakadan Najeriya a kasar Rasha, Abdullahi Shehu da tawagar gwamnatin kasar Rasha.
Tun da farko dai mataimakin shugaban kasar ya bar birnin Rome na kasar Italiya bayan halartar taron tsarin samar da abinci na Majalisar Dinkin Duniya.