04/09/2022
KVTC Ta Koya Wa Matan Da S**a Fito Daga Yankunan Da Matsalar Tsaro Ta Shafa A Katsina Sana'o'i
Mu'azu Hassan
Cibiyar horar da sana'o'in mai suna Katsina Vocational Training Center, wadda Marigayi MD Yusufu ya kafa shekaru 20 da s**a gabata, ta horar da mata sana'o'in daban-daban daga kananan hukumomi da ke da matsalar tsaro a jihar Katsina.
Horon, wanda aka yi shi a sansanin horar da masu yi wa kasa hidima da ke titin zuwa garin Mani jihar Katsina, an tara matan a wuri daya ba zuwa ko'ina daga ranar 29 ga Agusta zuwa 6 ga Satumba.
Daga cikin Malamai masu wa'azi da s**a yi wa matan jawabi akwai, Dakta Shaikh Ibrahim Iyal Gafai, Limamin masallacin Juma'a na Nura Mangal, wanda ya yi magana a kan dogaro da aka yi a cikin addini Musulunci da wajibcin sana'a da kasuwanci.
Sai kuma Malam MaHi sabuwar unguwa, wanda ya yi magana a kan hakuri da dogara ga Allah wajen neman halas da duk halin da mutum ya samu kansa.
Malam Aliyu Abdurrahim Sha'iskawa ya nuna masu yadda za su yi addu'a karbabba wajen Allah da addu'o'i ingantattu da Alkur'ani da Hadisi.
da Sayyid Maje Halliru 'Yan Siliyu ya yi masu nasiha mai ratsa zuciya.
Wanda ya jagaranci horarwar, Alhaji Aminu Tukur Unguwar Jaji, ya yi kira ga matan su tabbatar sun yi aiki da sana'ar da s**a koya.
Shugaban Cibiyar Muhammad Danjuma Katsina ya ce sun fito da tsarin horar da mata da ke fama da matsalar tsaro ne, don ya zama wani abin koyi na cewa fara koya wa mutum kamun kifi, ya fi ka ba shi gasasshen kifi.
Danjuma Katsina ya ce, "A wannan horon mun samu tallafi daga mutane biyu, Alhaji Sani Aliyu Danlami shi ne ya biya kudin wurin da aka saukar da masu horon, yayin da Alhaji Malik Anas, Babban Akanta-Janar na jihar Katsina shi ne ya ba da duk abincin da aka ciyar da masu horon sau uku a rana, yayin da Cibiyar ta dauki nauyin horon baki daya."
Malam Danjuma ya ce a ranar Alhamis 29/9/2022 Cibiyar za ta yi gagarumin taron yayen daliban, tare da ba su kayan tallafi.