
15/01/2025
Dambarwar masarautar Kano: A Kotun Ƙoli ma Sarki Sanusi ne zai yi nasara, in ji Falana
Fitaccen lauyan nan mai rajin kare ƴancin bil'adama , Femi Falana, SAN, ya tabbatar da cewa ko da an je Kotun Ƙoli, Sarkin Kano Muhammadu Sanusi ll ne zai yi nasara a shari'ar dambarwar masarautar Kano.
Femi Falana ya yi bayanin hakan ne a taron tunawa da Chief Gani Fewehini karo na 21 da aka gudanar a yau Laraba a Legas.
Taron dai ya samu halartar lauyoyi da dama da masu ruwa da tsaki a fannin shari'a.
Da ya ke gabatar da maƙala a taron, Falana ya ce "Ina so na taya Mai Martaba murna bisa nasarar da ya samu a Kotun Ɗaukaka Ƙara , naji wanda ke Shari'a da shi na cewa zai tafi kotun koli, to ko an je can din ma Sanusi ne zai nasara, kai ko ina ma za a je kai ne da nasara.
"Mai Martaba zama daram, kowa yasan kotun tarayya bata da hurumi kan sha'anin masarauta.
"Yakamata kungiyar lauyoyi ta kasa ta dau mataki kan yadda wasu lauyoyi ke yaudarar wadanda su ke karewa a kotu, ya kamata mu ceto mutuncin wannan tsarin", inji Falana.