05/08/2024
SAI JAM’IYYARKA TA KORE KA IDAN NA FALLASA WANI SIRRINKA, HON Abdulmumin Jibrin YA SAKE MAYAR WA DOGUWA MARTANI
..YA BUKACE SHI YA ƘYALE KWANKWASO
An jawo hankalina a kan wasu kamalai da ake alaƙanta su da Hon Alhassan Ado Doguwa a matsayin martaninsa kan gargaɗin da na yi masa a baya kan ya bar kalamansa na rashin kan gado, inda yake s**ar lamirin Jagoran NNPP/Kwankwasiyya na ƙasa da ma duniya baki ɗaya, ya mayar da hankalinsa kan ayyukansa na majalisa saboda akwai jan aiki da gabansa da yake jiran shi a can.
Kodayake abin da na yi tsammani daga wajensa shi ne ya ba jagoranmu haƙuri kuma ya ja bakinsa ya yi shiru, domin kare mutuncinsa a bainar jama’a da kuma la’akari da yanayin zaman ɗar-ɗar din da ake ciki a Kano, sai dai ban yi mamaki ba kan yadda Alhassan ya mayar da kansa kamar wani ɗan wasan kwaikwayo inda ya koma soki-burutsun da ya saba da jin ya fi kowa. Kallon da ya kamata jama’a su yi wa kalaman Alhassan ke nan sannan su yi watsi da su a ƙaton kwandon shara.
Har yanzu ina nan a kan kalamaina na baya, kuma bugu da ƙari, zan so in yi ƙarin haske da waɗannan bayanan a matsayin ƙarin martani ga Alhassan.
1- Na yi murna da yadda Hon Alhassan Doguwa ya yi amfani da wani ɓangare na Gargaɗina inda ya ba ni amsa BA Kwankwaso ba. A martanina na baya, na ƙalubalance shi da cewa ni zai soka, saboda ni ne sa’ansa, ba Kwankwaso ba. Martanin da ya yi min ya tabbatar da cewa tabbas ni ne sa’an nasa, ba Kwankwaso ba. Na gode wa Alhassan a kan haka, kuma ina mai tabbatar masa da cewa na shirya masa mu ci gaba da fafatawa. Ina so ya ɗan tsaya ya yi nazari a kan dalilin da ya sa Kwankwaso bai TAƁA tsayawaya mayar masa da martani ba. Zai fahimci cewa Kwankwaso ya shi Alhassan sa'an sa bane. Mune sao'in Alhassan.
2- Martanin da Alhassan ya yi ya daɗa tabbatar da raunin da yake da shi na shugabanci, musamman idan aka yi la’akari da shekarunsa. Da a ce shekarunsa ba su kai haka ba, da an yi masa uzuri. Duk da cewa Kwankwaso ya shafe tsawon shekaru yana kawar da kai ga zagi da cin zarafin da Alhassan yake masa, amma Alhassan ya ƙasa jurewa ko na tsahon kwana daya gargaɗi kawai da nayi masa kan ya ƙaurace wa ci gaba da zagin mutumin da ya fi shi ta kowanne fanni na rayuwa na b***e inna aika masa da zagi. Wancan ba ma zaginsa aka yi ba, gargaɗi aka yi masa, amma ya kasa natsuwa. Idan aka fara musayar zage-zage, wataƙila ya tsinci kansa a gadon asibiti. Ina fatan ya yi amfani da hikima a maimakon haka.
3- Gaskiya ne, ni dalibi ne a 1992, to amma shi ma Alhassan yana kammala karatu ya tsinci kansa a Majalisar Wakilai. Amma ni lokacin da na shiga majalisar, na kammala karatuna na digirin digir-gir kuma na yi karatu a Jami’ar kasuwanci na Havard da London, kuma gogaggen ɗan kasuwa ne sannan mai taimakon al’umma, a lokacin da Kwankwaso ya raine ni har na shiga majalisar. Bugu da ƙari, Kwankwaso, saɓanin Alhassan, sai da ya yi aikin gwamnati na tsawon shekaru 17 sannan ya yi digirinsa na biyu a Ingila, sannan ya yi wasu karance-karancen kafin ya lashe zaɓen majalisa sa kuma mataimakin Shugaban Majalisar mai wakilai mutane wajen dari shida 600.
4- Yayin da bayan shekaru 32, har yanzu Alhassan yana cikin majalisar a matsayin mamba, ba tare da ya yi wani hoɓɓasa na matsawa gaba saboda dalilan da kowa ya san su,
b***e ya zama Mataimakin Shugaban Majalisar, matsayin da Kwankwaso ya taka, kuma shi Kwankwason ya matsa daga majalisar inda ya lashe zaɓen zama mamba a kwamitin rubuta kundin tsarin mulki, ya yi Gwamnan Kano har sau biyu, ya yi Ministan Tsaro, ya yi Jakada na musamman a yankin Darfur na Sudan, mamba a kwamitin gudanarwa na hukumar NDDC, Sanata, mai neman takarar Shugaban Kasa har karo biyu, kuma ɗan takarar Shugaban Kasa sannan jagoran NNPP kuma Jagoran babbar aƙidar Kwankwasiyya a Najeriya da ma duniya baki ɗaya, wacce daga bisani ta haifi Gwamnnoni da ’yan majalisu da ministoci da jakadu da shugabannin hukumomin gwamnati da ma wasu da dama. Dole mu ci gaba da girmama shi saboda a lokuta daban-daban duk mun ci moriyarsa, musamman ma shi Alhassan da Kwankwason ya cetoshi ya koma Majalisar Wakilai a shekara ta 2007, bayan ya shafe shekaru 15 yana ƙoƙarin ganin hakan amma ya gaza, inda daga bisani ya canji wanda ya ke kan kujerar.
5- Ko da sau shurin masaƙi ne, ya kamata Alhassan da ma sauran jama’a su san cewa a kullum Kwankwaso mutum ne mai son zaman lafiya, uba ne, fitila ne, mai gina jama’a ne kuma ɗan siyasa ne da ya fi kowa tasiri a Arewacin Najeriya a yau, kuma yana da tarin magoya baya, musamman talakawa. Kwankwaso ba ya yi, kuma bai taba zuga matasa ko ma kowanne mutum ya tayar da zaune tsaye ba. Ya kamata mutane su kalli kalaman Alhassan a matsayin da suke - na ƙoƙarin neman suna ta hanyar saka Kwankwaso a surutanshi da neman ganin ido na birge wasu a Abuja cewa shi ne jagoran jam’iyyarsu a Kano. Wannan ba sabon abu ba ne, kuma ba zai yi nasara ba. Burinsa shi ne “Gwara kan Kwankwaso da na Tinubu” a matsayin hanya ɗaya tilo da zai sami gindin zama a matakin tarayya. Abin da yake ƙoƙarin faruwa ke nan a Kano a yau da muke ganin alamunsa. Za mu yi iya bakin ƙoƙarinmu mu kuma yi amfani da doka wajen daƙile wannan ɓatancin.
6- Ina ƙara ba Alhassan shawara da ya girmama tsufansa. Ya kamata ya taƙaita fadace-fadacensa da zage-zagensa da kalaman soki-burutsunsa ga iya jam’iyyarsa, inda a cikinta ya yi fada kuma yake ci gaba da yin faɗan da kowa. Maganar gaskiya ita ce idan wasu daga cikin shugabannin jam’iyyarsa, musamman waɗanda suke Abuja, waɗanda yake ƙoƙarin burgewa, s**a san irin kalaman da yake yi a kansu, sai sun kore shi daga jam’iyyar. Amma mu jira lokaci.
Daga ƙarshe, ina jajanta wa Alhassan, wanda bisa ga dukkan alamu yake fama da matsananciyar damuwa, musamman kasancewarsa mai rawani babu sarauta. Amma a matsayin danna-ƙirji, zai iya karbar sarautar “Sardaunan Rawani”. Allah ya ja zamanin Sardaunan Rawani.
Sani Ibrahim P**i
Hadimin:
Hon Abdulmumin Jibrin, MSc SEP PLD, MBA, PhD (Jarman Bebeji)
Ɗan Majalisa mai hawa huɗu, tsohon shugaban kwamitocin Kuɗi, Kasafin Kudi, Sufuri, Harkokin Waje, kuma yanzu haka Shugaban Kwamitin Gidaje da Muhalli na Majalisar Wakilai