20/12/2024
Yadda Gwamnan Jihar Kaduna Ya Gyara Babban Asibitin Sanga Da Ya Haura Sama Da Shekaru 30 A Lallace
Daga Abubakar Saraki
...Idan kuka duba hotunan za ku ga yadda Asibitin ya ke a baya da kuma yanzu da aka gyara shi, Wanda gwamnatin Uba Sani ta ke ingantawa tare da daukaka darajarsu.
Gwamnatin Jihar Kaduna, Ƙarƙashin jagorancin Sanata Mallam Uba Sani mai faɗa da cikawa, Ya kusa kammala gyaran babban Asibitin Sanga wato (Sanga General Hospital Gwantu), A ƙoƙarin sa na kawo sauyi da haɓaka ɓangaren kiwon lafiya, Wannan yana ɗaya daga cikin manyan Asibitoci 11 da suke ɓangarorin Sanatoriya Uku da ke Kaduna kuma ake kan gyara su.
Uba Sani, A matsayin sa na jajirtacce mai himma da kishin al'ummarsa ya duƙufa yin ayyuka ba dare ba rana wajen gyara tare da samar da kayayyakin aiki irin na zamani da inganta manyan Asibitoci da ke lungu da saƙo na jihar Kaduna.
Kazalika, Mutane daga ciki da wajen jihar Kaduna suna yabawa gwamna Uba Sani ganin yadda yake ƙoƙari gyara harkokin lafiya da asibitoci a birni da ƙauyuka, Kuma ya zo daidai lokacin da al'umma suke buƙatar irin sa na samar da tsarin da zai sauƙaƙa musu musamman a ɓangaren inganta kiwon lafiyar su.