Alfarma Radio Kano

Alfarma Radio Kano Kafar Yada Labarai Mai Zaman Kanta dake gabatar da Shirye - Shirye a Shafukan Sada Zumunta.
(1)

Alfarma Radio Kano karkashin Jagoranchin Ahmad Yasin Bin Ali na taya Al'ummar Kiristoci Murnar Zagoyowar bikin Kirsimeti...
24/12/2024

Alfarma Radio Kano karkashin Jagoranchin Ahmad Yasin Bin Ali na taya Al'ummar Kiristoci Murnar Zagoyowar bikin Kirsimeti na Shekarar 2024 da bikin sabuwar Shekarar 2025.

Dafatan za'ayi lafiya a kammala lafiya, muna Shawarar Kiristoci da suyi amfani da Wannan dama wajen yin Addu'a ga kasarmu Nigeria.

Jama'a Barkanmu da warhaka, Yau litinin 22 ga watan Jumadha akhir 1446, dai-dai da 23 ga watan disambar 2024, Azumi saur...
23/12/2024

Jama'a Barkanmu da warhaka, Yau litinin 22 ga watan Jumadha akhir 1446, dai-dai da 23 ga watan disambar 2024, Azumi saura kwana 68

Idan akace ka fadi Kalma daya akan Motarnan me zakace???
22/12/2024

Idan akace ka fadi Kalma daya akan Motarnan me zakace???

Qazanta ne ka kwana da wando washegari kayi sallah da shi, da wuya mutum ya kwana ba tare da ya zubar da wani abu ba. — ...
20/12/2024

Qazanta ne ka kwana da wando washegari kayi sallah da shi, da wuya mutum ya kwana ba tare da ya zubar da wani abu ba. — Inji Sultan Ahmad

Me zaku ce ?

KA HADA KOKUMBA-KARAS-DABINO KA CI07082728653Ka nemi kokumba guda daya da karas kwara daya da Kuma dabino Mai laushi qwa...
20/12/2024

KA HADA KOKUMBA-KARAS-DABINO KA CI

07082728653

Ka nemi kokumba guda daya da karas kwara daya da Kuma dabino Mai laushi qwara biyar.
Zaka wanke su da ruwa sosai sai ka zauna ka tauna kokumba ka tauna karas ka tauna dabino a lokaci daya har ka cinye.

1.Yana Karawa idanu haske da lafiya.

2.Yana maganin zafin jiki.

3.Yana saukarda jinin dake yawan hauhawa.

4.Yana Karawa hakora karfi.

5.yana tafiyarda gajiya.

6.Yana Karawa ciki lafiya.

7.Yana amfanar zuciya, Koda da Hanta.

8.Yana Karawa jiki kuzari.

9.Yana saita tinani.

10.Yana maganin bayan gari Mai tauri.

11.Yana maganin basir.

12.Yana rage barazanar cutukan daji.

18/12/2024

Muna Godiya ga! Faruq Hassan Dagumawa bisa kasancewa mabiyin da yafi kowane dadewa yana bibiyarmu

Real Madrid Ta Lashe Gasar INTERCONTINENTAL CUP CHAMPIONS! 🙌Bayan data doke Kungiyar Pachuka daci 3-0.
18/12/2024

Real Madrid Ta Lashe Gasar INTERCONTINENTAL CUP CHAMPIONS! 🙌

Bayan data doke Kungiyar Pachuka daci 3-0.

Shugaban majalisar wakilai, Tajuddeen Abbas ya goyi bayan ƙudurin dokar haraji Shugaban Majalisar Wakilai, Tajudeen Abba...
18/12/2024

Shugaban majalisar wakilai, Tajuddeen Abbas ya goyi bayan ƙudurin dokar haraji

Shugaban Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, ya ce karancin harajin da Najeriya ke samu ya kasance wani babban cikas ga ci gaban kasar.

Abbas ya bayyana haka ne a wajen gabatar da kudurin kasafin kudin 2025 ga wani zama na hadin gwiwa na majalisun taraiya da shugaban kasa Bola Tinubu ya yi a Abuja a yau Laraba.

A cewarsa, rabon harajin Najeriya zuwa kayan da ake samarwa a kasa, GDP, a halin yanzu ya yi ƙaranci a kusan kashi 10.9 cikin 100 a 2024, inda ya ce yana cikin mafi ƙaranci a Afirka, wanda ya yi ƙasa da matsakaicin mataki na nahiyar wanda ya ke a kashi 15.6 cikin ɗari.

Ya ce yawan kudin da ake tara harajin VAT a Najeriya a kusan kashi 20 cikin 100 ya yi kasa da kusan kashi 70 cikin 100 da kasashen Afirka ta Kudu, Equatorial Guinea da Zambia s**a samu.

Abbas ya ce, tunkarar wadannan kalubale na bukatar sauye-sauyen manufofin haraji cikin gaggawa, don fadada tushen harajin kasar, da inganta bin ka'ida, daidaita harkokin gudanarwa, da kuma rage dogaro da karbar bashi.

Ya ce ‘yan majalisar za su ci gaba da yin aiki tare da gwamnatin Tinubu don ganin an yi gyare-gyaren da ya kamata, kuma mai inganci da kuma la’akari da bukatun marasa galihu.

Yayin gabatar da kasafin kuɗi, Tinubu ya faɗawa ƴan majalisa cewa duk za su lashe zaɓen su a 2027Shugaban kasa Bola Ahme...
18/12/2024

Yayin gabatar da kasafin kuɗi, Tinubu ya faɗawa ƴan majalisa cewa duk za su lashe zaɓen su a 2027

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a ranar Laraba ya yi barkwanci inda ya ce ‘yan majalisar dattawa ta 10 sun “sake cin zaɓe.”

VANGUARD ta rawaito cewa hakan ya faru ne lokacin da shugaban ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2025 ga taron hadin gwiwa na Majalisar Dokoki ta Ƙasa.

Tinubu ya yi wannan furuci ne bayan ya yi kuskure wajen kiran majalisar dattawa ta 10 da sunan ta 11.

Ya yi wannan barkwanci ne bayan wasu daga cikin ‘yan majalisar sun gyara shi, kamar yadda aka gani a wani bidiyo da ya bazu wanda ke da tsawon minti ɗaya da dakika 14.

"Domin cika ɗaya daga cikin hakkokina na doka tare da jajircewa wajen sake gina Najeriya da tabbatar da mun tsaya tsayin daka a tafiya mai zuwa ta samar da makoma mai albarka, na gabatar da kasafin kudin 2025 ga taron hadin gwiwa na Majalisar Dokoki ta Ƙasa ta 11,” in ji Tinubu.

Bayan wannan, ‘yan majalisar sun tuna wa Shugaban cewa su ne Majalisar Dokoki ta 10.

“Ta 10? Na rubuta ta 11, wanda ke nufin kun sake cin zaɓe gaba ɗaya,” Shugaban ya amsa da dariya.

Mun daina rusau sai dai mu kai mutum kurkurku kai-tsaye - Gwamnatin Kano Hukumar Tsara Birane ta Jihar Kano, KNUPDA ta c...
18/12/2024

Mun daina rusau sai dai mu kai mutum kurkurku kai-tsaye - Gwamnatin Kano

Hukumar Tsara Birane ta Jihar Kano, KNUPDA ta ce daga yanzu ta daina rusa gine-gine da aka yi ba bisa ƙa'ida ba, sai dai kawai ta aika wanda ya karya dokar zuwa gidan yari kai tsaye.

Da ya ke zantawa da manema labarai a ofishin sa, shugaban hukumar, Arc. Ibrahim Yakubu Adamu ya ce sashe na 11 da na 12 da na 13 da na 14 da na 15 na dokar da ta kafa KNUPDA sun tanadi hukuncin gidan yarin na shekara ɗaya, har ma da cin tara ga wanda ya karya dokar hukumar.

Mudassir and Brothers 😂😂😂
18/12/2024

Mudassir and Brothers 😂😂😂

Address

Sani Mainagge Along Mandawari
Kano

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Alfarma Radio Kano posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Videos

Share

Category