06/03/2024
WASU DA AKE ZARGIN 'YAN SA-KAI NE S**A KASHE MALAMIN ADDININ ISLAMA BA JAMI'AN RUNDUNAR ASKARAWA BANE, INJI GWAMNATIN ZAMFARA
Aƙalla mutane goma (10) da ake zargin ‘yan kungiyar ‘yan banga ne aka k**a bisa kisan rashin tausayi da aka yi wa wani malamin addinin Islama a Zamfara.
Wasu da ake zargin ’yan banga ne s**a kashe Sheikh Abubakar Hassan Mada a garin Mada da ke karamar hukumar Gusau a ranar Talata.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta bayyana cewa waɗanda ake zargin da hukumomi s**a k**a ’yan banga ne ba sabbin jami’an rundunar Askarawa (CPG) bane.
A cewar sanarwar, ‘yan banga da aka k**a, gwamnatin jihar ba ta ba su izinin gudanar da kowane irin aikin tsaro ba, saboda ba sa cikin jami’an tsaron al’umma.
“Gwamnatin jihar Zamfara ta samu labarin kisan gilla da aka yi wa Sheikh Abubakar Hassan Mada a garin Mada. Lallai abin takaici ne da za a iya hana shi.
“Jami’an tsaro sun yi nasarar cafke duk ‘yan bangar da ake zargi da aikata wannan danyen aikin.
“Gwamnatin jihar Zamfara ta ɗauki wannan lamari da muhimmanci kuma ta himmatu wajen ganin an gurfanar da duk waɗanda s**a aikata wannan kisan gilla a gaban kotu. Za a yi duk mai yuwuwa don ganin an yi adalci ba tare da tsangwama ba.
“Muna so mu fayyace cewa ‘yan banga da ake zargi da aikata kisan gilla ba su da wata alaƙa da jami’an tsaron al’ummar jihar Zamfara.
“An kafa sabuwar rundunar tsaron jama’a (Askarawa), don kare al’umma ba wai ta’addancin mutane a jihar ba.
“Wannan bayanin zai taimaka wurin magance ruɗanin da ya taso kan asalin waɗanda aka k**a da laifin kisan gillar. Ba za mu taɓa yin ƙasa a gwiwa ba wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
“Muna so mu sanar da jama’a cewa jami’an tsaron al’ummar Zamfara suna da tsarin da zai hana su gudanar da wani aiki ba tare da bin umarnin jami’an tsaron da abin ya shafa ba.
“A bisa binciken farko da ‘yan sanda s**a gudanar, an gano cewa ɗaya (1) daga cikin ‘yan bangar da aka k**a tsohon ɗalibin Shehin Malamin ne da aka kashe, wannan bayanin zai iya taimakawa hukuma ta ƙara fahimtar lamarin tare da ƙ ɗaukar matakan da s**a dace.
“Gwamnatin Zamfara za ta bayyana sak**akon binciken ‘yan sanda ga jama’a da zarar ta kammala.
“A cikin wannan mawuyacin lokaci, muna jajantawa iyalan Sheikh Abubakar Hassan Mada da sauran al’umma baki ɗaya. Allah ya jikansa da rahama tasa.ya huta.
SULAIMAN BALA IDRIS
Babban mataimaki na musamman (kafafen sadarwa da watsa labarai) ga Gwamnan Zamfara
Maris 06, 2024
ABULBANAT 🎙️ 2024.