11/08/2025
Zamfara Ta Sake Fuskantar Hari: Sama da Mutum 140 Sun Shiga Hannun ‘Yan Bindiga a Mako Guda
Daga { Abubakar Bashir Adam Yakasai}
Kungiyar Zamfara Circle Community Initiative ta bayyana cewa a tsakanin ranar 4 zuwa 10 ga watan Agusta, 2025, ‘yan bindiga sun kai hare-hare a ƙauyuka 15 a faɗin jihar Zamfara, inda s**a yi garkuwa da mutane 144, s**a kashe 24, tare da raunata wasu 16.
Rahoton ya nuna cewa hare-haren sun shafi ƙananan hukumomi daban-daban, ciki har da:
Bakura: Sabe, Tungar Yamma, Sauru, Lambasu, Dogon Madacci, Dankalgo, da Kwanar Kalgo.
Tsafe: Chediya, Kucheri, Yankuzo, da Katangar Gabas Bilbils.
Mafara: Tabkin Rama, Matsafa, da Ruwan Gizo.
Gummi: Rafin Jema.
Bukkuyum: Adabka da Masu.
Shaidun gani da ido sun ce mazauna da dama sun tsere daga gidajensu zuwa garuruwan makwabta don tsira da rayuka, yayin da waɗanda aka yi garkuwa da su s**a haɗa da maza, mata, da yara kanana.
Duk da yawaitar irin waɗannan hare-hare a yankin Arewa maso Yamma, musamman Zamfara, jama’a na ci gaba da bayyana damuwa kan yadda gwamnati ke tafiyar da batun tsaro. Masu sharhi sun nuna cewa duk da ƙoƙarin da ake cewa ana yi, ‘yan bindiga na ci gaba da cin karensu babu babbaka, lamarin da ke nuna akwai gibi tsakanin tsarin tsaro da aiwatar da shi a zahiri.
Wasu na ganin cewa dole ne gwamnati ta sauya salo, ta zuba ƙarin jami’an tsaro a yankunan karkara, tare da amfani da fasahar zamani wajen gano maboyar masu garkuwa da mutane. Har ila yau, ana kira da a karfafa haɗin gwiwa tsakanin jihohi da al’ummomi wajen bada bayanan sirri don magance barazanar tsaro a yankin.
Zamfara Circle Community Initiative ta roƙi gwamnati da hukumomin tsaro da su ɗauki matakan gaggawa wajen ceto waɗanda ke hannun ‘yan bindiga, tare da tabbatar da tsaron mazauna yankunan da abin ya shafa.