Duniyar Mu Ayau Hausa News

Duniyar Mu Ayau Hausa News Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Duniyar Mu Ayau Hausa News, Broadcasting & media production company, Kano.

20/11/2023

Bamu Anfani da wanga Shafi kuma ku Nimemu A Wanga sabon Shafinmu Mai Suna 👉 DMA Hausa News

15/11/2023

Kugafarcemu Masoyan mu Muncenza Shafi A Bisa Wata Kuskure Da Muka Sanu A Shafi Kuna Iya Samunmu AWanga Shafi 👉DMA Hausa News

'Yan kasuwa sun kwashe kwanaki 5 suna jiran rakiyar jami'an tsaro zuwa garin su a ZamfaraDaga Belyameen Ahmad MagamiWasu...
14/11/2023

'Yan kasuwa sun kwashe kwanaki 5 suna jiran rakiyar jami'an tsaro zuwa garin su a Zamfara

Daga Belyameen Ahmad Magami

Wasu 'yan kasuwa kenan da s**a kwashe kwanakki 5 suna jiran rakiyar ma'aikatan Soji a hanyar ɗansadau zuwa magami saboda rashin kyau na hanyar duba da ƙaranci rashin tsaro, yau dai sun samu 'yanci na samun jami'an soji ɗin da s**a raka yi masu Rakiya.

Labari a cikin hotuna kalli yanda matasan da s**a kwashe a kwanaki 5 suna jiran rakiyar ma'aikatan sojoji akan hanyar Ɗansadau zuwa magami ta ƙaramar hukumar mulkin Gusau A jihar zamfara.

An kammala wasannin rukuni na baje kolin basirar hazikan Yan Wasan Kwallon kafa da Shugaban Kungiyar Kwallon kafa ta Kat...
14/11/2023

An kammala wasannin rukuni na baje kolin basirar hazikan Yan Wasan Kwallon kafa da Shugaban Kungiyar Kwallon kafa ta Katsina United Fc Alh Kabir Dan'lami Rimi hadin gwiwa da Darakta Janar na Dikko Sports Movement Abubakar Sani s**a shirya

A wasannin da aka fafata a yau Kungiyar Kwallon kafa ta Musa Haro Football Academy ta Sha Kashi hannun takwarar ta ta Durbi Strikers Daci 3-0 ,a yayin da aka tashi canjaras tsakanin Kungiyar Kwallon kafa ta Junior Dan'buran da Kangiwa United,sai Kuma a wasa na uku Kungiyar Kwallon kafa ta KKT STRIKERS tayi nasarar doke takwarar ta ta Eagle Star's Mai'adua daci 3-2

Haka Nan Kuma Kungiyar Kwallon kafa ta Gwagware academy tayi nasarar doke Kungiyar Kwallon kafa ta DUTSINMA PILLARS daci 2-1, sai wasa na karshe da aka fafata tsakanin Kungiyar Kwallon kafa ta Enyimba Katsina da Katsina Football Academy Wanda ya tashi ci 2-1 a ragar Enyimba Katsina.

An ware gobe laraba 15/11/2023 da misalin karfe 3:00pm domin buga Wasan karshe na gasar Wanda za'a kara tsakanin SCOUT SELECTED da KATSINA TEAM a filin wasa na Muhammadu Dikko Stadium dake cikin birnin katsina.

Nasir Gide
SWAN KATSINA.

YANZU-YANZU: Zanga-zanga mai zafi ta barke a hedkwatar hukumar zabe mai zaman kanta na INEC, dake birnin tarayya Abuja, ...
14/11/2023

YANZU-YANZU: Zanga-zanga mai zafi ta barke a hedkwatar hukumar zabe mai zaman kanta na INEC, dake birnin tarayya Abuja,

Magoya bayan dan takarar Gwamna na SDP a jihar Kogi, sun fito kwansu da kwarkwatansu don nuna rashin amincewarsu da zaben da a gabatar a jihar a ranar asabar dinan data gabata.

A halin yanzu sun kulle harabar shiga hukumar ta INEC don nuna rashin jin dadinsu..

Gwamnatin ƙasar ta tabbatar da haramta TiktTok, inda ministar yaɗa labarai na ƙasar, Rekha Sharma, ta ce shafin na yana ...
14/11/2023

Gwamnatin ƙasar ta tabbatar da haramta TiktTok, inda ministar yaɗa labarai na ƙasar, Rekha Sharma, ta ce shafin na yana yaɗa abubuwa marasa kyau.

Barazanar Ƴan Ta'addar Daji Yasa Mutane Girbe Dawa Da Wake A Jihar Katsina....Manoma a ƙaramar hukumar Sabuwa ta jihar K...
14/11/2023

Barazanar Ƴan Ta'addar Daji Yasa Mutane Girbe Dawa Da Wake A Jihar Katsina....

Manoma a ƙaramar hukumar Sabuwa ta jihar Katsina sun fatsama gonakin su domin girbe amfanin gonakin su bisa barazanar ƴan ta'addar daji dake kora masu shanu suna cinye amfanin Gonar.

Da tsakar ranar yau dai ɓarayin s**a kora shanun su gonar wani Alh. Umar Gaskora inda shi kuma ya ƙalubalance su akan mi zasu tura mashi shanu su cinye mashi amfanin gona, ƴan ta'addar basuyi wata wata ba s**a halaka shi akan wannan yanzu haka yana Asibiti inda Likitoci s**a tabbatar da Mutuwar shi.

Al'ummomin yankin Dankolo da Dugun Mu'azu dai suna cikin sun tashin hankali sun zama abin tausayi ganin cewa hatta da jami'an tsaro sojoji dake yankin sun kasa tabuka komai ganin cewa da inda ƴan ta'addar suke da kuma Inda ɓarayin suke cinyewa mutane amfanin gona baida wani nisa.

Waɗanda ɓarayin dai ba ƙaramar barazana bane a wannan yankin domin sun tarwatsa kasuwamcin yankin Sun tarwatsa kiwon yankin shima noman da kadai aka dogara dashi a yankin shima sun sako shi gaba, suna bin gonaki sua dibarwa mutane buhunnan amfanin gona yanzu Kuma sun koma suna cinyewa mutane dawa da farin wake.

Lamarin nan yafi ƙarfin jama'a su zuba Idanuwa ba tare da yin wani yunƙuri ba, muna kira gare su da su ci gaba da yin Addu'oen neman agajin gaugawa daga wurin Allah akan wannan Lamarin, Allah zai basu mahita kuma yayi masu maganin duk masu hannu akan wannan Ibtila'in.

Muhammadu Aminu Kabir

Gamayyar ƙungiyar ƙwadago a Najeriya NLC tace babu gudu baja da baya kan yajin aiki da zata fara daga yau talataA wata s...
14/11/2023

Gamayyar ƙungiyar ƙwadago a Najeriya NLC tace babu gudu baja da baya kan yajin aiki da zata fara daga yau talata

A wata sanarwa da NLC da takwararta ta TUC s**a fitar, tace an baiwa dukkanin rassanta da kuma mambobin dake faɗin jihohi umarnin shiga yajin aikin.

Ƙungiyar tace zata cigaba da yin yajin aikin har sai gwamnatoci a dukkanin matakai sunyi abinda ya dace

Yaya kuka Kalli wannan mataki na ƙungiyar kwadago duk da matsin tattalin arziki da al'umma ke fama dashi?

Wacce hanya za'abi na ganin an kawo karshen yajin aikin?

YANZU-YANZU: Ƴan Sanda Sun K**a Wani Matashi Da Ake Zargi Da Kashe Wani Mutum Ta Hanyar Caka Masa Wuka A Ƙirji.A Safiyar...
14/11/2023

YANZU-YANZU: Ƴan Sanda Sun K**a Wani Matashi Da Ake Zargi Da Kashe Wani Mutum Ta Hanyar Caka Masa Wuka A Ƙirji.

A Safiyar yau Litinin aka k**a wani Matashi da ake zargi da kisan kai a garin Burga ta Jahar Bauchi.

A ranar Asabar din da ta gabata dai ne ake zargin matashi da yin faɗa da mai gidansa a cikin mahauta a ya yin da suna cikin faɗan ne ya caka masa wuka a kirji kuma har ya samu ya tsire daga garin na Burga.

Wanda ake zargin ya amsa laifinsa inda ya ce ya zo ne don ya bayar da hakuri ga matar mamacin, akan laifin da ya aikata, nan take matar ta nemi taimakon wasu matasa akan su k**ashi ga abun da ya aikata mata lokacin ne jama'a dayawa s**a bishi aka k**ashi a daidai Games Village na cikin garin Bauchi.

Zuwa yanzu yana hanun hukuma don faɗaɗa bincike

Daga: Humaid Alhaji Lawal
📷 Mujahid Saleh Saad - Dan maliki Mujahid Saleh Saad

Daliban Makarantar Justice Fati lami Abubakar, ba'a barsu s**a shiga makarantar ba sak**akon Yajin aikin da Kungiyar ta ...
14/11/2023

Daliban Makarantar Justice Fati lami Abubakar, ba'a barsu s**a shiga makarantar ba sak**akon Yajin aikin da Kungiyar ta kwadago ta shiga Ayau Talata.

Daga Walikinmu Abubakar Na (Kaulaha) DMA Hausa News

DA ƊUMI-ƊUMI: Hukumar Hizba ta jihar Kano, ta yi nasarar cafke wasu mutane da ke ciko Motoci da Giya zuwa jihar Kano.
13/11/2023

DA ƊUMI-ƊUMI:
Hukumar Hizba ta jihar Kano, ta yi nasarar cafke wasu mutane da ke ciko Motoci da Giya zuwa jihar Kano.

Abin akwai sosa zuciya: 'Yan uwa a sa ta cikin addu'a Allah Ya bata lafiyaWannan ita ce yar gwagwarmaya a shafukan sada ...
13/11/2023

Abin akwai sosa zuciya: 'Yan uwa a sa ta cikin addu'a Allah Ya bata lafiya

Wannan ita ce yar gwagwarmaya a shafukan sada zumunta mai suna Rufatu Shuaibu yar asalin garin Sheme mazauna Funtua da Allah Ya jarabce ta da kansar mama (Breast Cancer), kuma cikin ikon Allah, yau mai girma gwamna Dikko Raɗɗa ya bayar da umurnin a ɗauke ta zuwa asibitin koyarwa na Jami'ar Maiduguri, domin nema mata lafiya

Duk wanda ya san Rufatu a wannan kafar sadarwar zai santa da juriya da kuma jajircewa, a kan hidimar da ta tasa gaba, ba tare da cin mutuncin kowa ba, ta dauki tsawon lokaci kwance duk abin da iyayenta s**a tara ya kare wajen nema mata magani, har Allah Ya sa Gwamna Dikko Radda ya ji labarin halin da take ciki, ya bayar da umurnin a kai ta asibiti

Muna rokon Allah Ya bata lafiya Amin

📸 Funtua Online Media Reporters

13/11/2023

Ya kuka ji da dawo da bashin da MTN s**a yi?

13/11/2023

Jama,a Kudu Ba SIM Card MTN Nako Ko An Dawo Maku Da Bas**anku Saboda Akwai Wanda Yace Andawo Mashi Da Nashi Bashin

AN KASHE KWAMANDAN "COMMUNITY WATCH" A SAFANADaga Muhammad Bello @ Katsina Times. Yan ta adda sun kashe wani kwamandan s...
13/11/2023

AN KASHE KWAMANDAN "COMMUNITY WATCH" A SAFANA

Daga Muhammad Bello @ Katsina Times.

Yan ta adda sun kashe wani kwamandan sabuwar rundunar nan ta Katsina Community Watch mai kula da garin Zakka ta karamar hukumar Safana.

Kwamandan Wanda yake kula da yankin Zakka mai suna Mujitaba Salisu an kashe shi ne tare da wani Dan sandan Mobayil (Mobile Police).

Wani a garin Zakka ya fada ma jaridun Katsina Times cewar, a jiya lahadi 12 ga watan Nawumba, 'Yan ta addar s**a fito daga daji s**a tunkaro Zakka.

Ganin sun nufo garin yan sanda da Hadin gwaiwar yan Katsina Community Watch dake garin na zakka s**a fuskance su inda akayi fadan gaba da gaba.

A wannan bata kashin ne aka kashe Mujtaba da Dansanda daya. Suma barayin anyi masu Barna sosai amma sun tafi da gawarwakin mutanen su.

Wata majiya tace, Barayin Sun yi yunkurin yin gangami domin karasa ta addacin da s**a shirya, amma sai sojan sama s**a kawo dauki Wanda wannan ya tsorata barayin s**a koma daji.

Katsina Times
@ www.katsinatimes.com
Jaridar Taskar labarai
Www.jaridartaskarlabarai.com
07043777779 08057777762.

Miye Zaku Iya Siya Kuci Ku Koshi Da Naira 50?
13/11/2023

Miye Zaku Iya Siya Kuci Ku Koshi Da Naira 50?

Bayan fitowa daga Kotu, lauyan mai kara Barista M.A Barde ya bayyana cewa, Kotu ta umurci a sake mannawa Dauda Kahutu Ra...
13/11/2023

Bayan fitowa daga Kotu, lauyan mai kara Barista M.A Barde ya bayyana cewa, Kotu ta umurci a sake mannawa Dauda Kahutu Rarara sammaci a dukkan gidajensa dake kafatanin Najeriya, sak**akon rashin samunsa da wakilin kotu bayyiba,

Kotu ta bayar da ranar 4 ga watan Disamba a matsayin ranar da za'a cigaba da sauraren karar,

Wakilin Jaridar ATP Hausa ya tuntuɓi Dauda Kahutu Rarara ta wayar tarho don jin ta bakinsa, inda ya bayyanawa wakilinmu cewa, takardar kara bata riske shi ba. Amma zai sanar daa lauyansa ya bincika.

Hatsarin Mota: Hukumar Shiga da Fice sun Rasu a Hanyar Kano zuwa Abuja wayandas**arasu Allah yajikansu wayanda s**asamu ...
13/11/2023

Hatsarin Mota:
Hukumar Shiga da Fice sun Rasu a Hanyar Kano zuwa Abuja wayandas**arasu Allah yajikansu wayanda s**asamu raunika Allah yabasu lfy

IKON ALLAH: Wani masoyin Buhari ya yi ma wanda ya maka Dauda Kahutu Rarara  a kotu kyautar mota ta miliyan 20.“Ruhoton n...
13/11/2023

IKON ALLAH: Wani masoyin Buhari ya yi ma wanda ya maka Dauda Kahutu Rarara a kotu kyautar mota ta miliyan 20.

“Ruhoton na cewa wani masoyin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, yayi kyautar motar miliyan 20 ga Alhaji Sani Ahmad Zangina wanda ya maka Dauda Kahutu Rarara a kotu, “inda yake zargin mawaƙin da cin zarafin tsohon shugaban kasar.”

A gobe litinin ne akesa ran fara sauraren karar da aka shigar da mawakin siyasar Dauda Kahutu Rarara a gaban kotu.

An Gano Gawarwaki wasu makiyaya ukku da ake zargin 'Yan Banga s**a kashe, acikin Daji dake Washa, Beji. Karamar hukumar ...
12/11/2023

An Gano Gawarwaki wasu makiyaya ukku da ake zargin 'Yan Banga s**a kashe, acikin Daji dake Washa, Beji. Karamar hukumar Shiroro Jahar Naija.

Gawarwakin da ake Zargin Wasu 'Yan Banga ne s**a kashe su, Biyo bayan dukan su da kuma Yankan Rago da s**ayi masu.

'Yan Bangan dai sun taradda Auwal, Hussaini, da Ibrahim acikin dakin su, suna hutawa yayin da s**a Gama aikin Cire Borkonu, inda s**a k**asu s**a wuce da su cikin daji da duka a daure daga bisani s**a yanka su.

Inda akayi Sallar Jana'iza k**ar yadda addinin musulunci ya tanada, izuwa Hada wannan Labari Gwamnati bata ce uffan ba.

Daga Abubakar Na (Kaulaha)
DMA Hausa News 📷

Madarasatul Adabi Wa`zharul Islam (Mawis) Genera M I Wushishi Estate Eastern Bye-Pass Minna Ta Gudanar Da Taron Walima K...
12/11/2023

Madarasatul Adabi Wa`zharul Islam (Mawis) Genera M I Wushishi Estate Eastern Bye-Pass Minna Ta Gudanar Da Taron Walima Karo Na Bakwai Ga Dalibai Sittin Ayau Lahadi

Daga Hadiza Muhamnad

Makarantar Islamiyar Madarasatul Adabi Wa`izaharul Islam (Mawis) M I Wushishi Estate, Bye- Pass Cikin Garin Minna Jahar Neja Ta Gudanar Da Taron Walima Karo Na Bakwai Ga Dalibai Sitin Ayau Lahadi , Taron Yasamu Halartan Malamai Da Iyaye Maza Da Mata Da Sauran Alumma Daga Sassan Anguwani Na Cikin Gari Baki Daya.

Daga Bakin Daya Daga Cikin Mayan Iyayen Taro Kuma Malami Sheikh Muhammad Ibrahim Gaba Limanin Gaba Yace Dalilin Taron Shine Nuna Godiya Ga Allah Da Ya Baiwa Wayanan Yaya Babbar Rabo Na Samu Saukar Karatun Al,Qurani Mai Girma Domin Kuwa Ribace Ga Dukan Dan Musulmi Daga Nan Duniya Dama Lahira Baki Daya , inda Yaja Hakalin Dalibai Cikin Nasiha Cewa Dalibai S**asance Masu Roko Da Al,Qurani Da Niman Sauran Ilimai Na Hadisan Manzon Allah S a w Bayan Walimarsu, Kada Suyi Watsa Da Dukan Abin Da Yashafi Lamarin Adinin Musuluci Bayan Walimarsu Kuma Su Kasance Masu Kaucewa Dukan Lamarin Rodin Zamani Da Hudar Da Babu Lamarin Allah Da Manzo S a w Acikinta. inda Shahin Malamin Yakara Jan Hakalin Iyaye Maza Da Mata Wajan Sanyawa Yaransu Ido Akan Tarbiyarsu Bayan Walimar Da Kuma Abin Da Yashefi Rayiwar Daliban Akan Ilimin Adinin Musulunci Da Kuma Tarbiyarsu.

Daga Karshe Yayiwa Daliban Fata Alhairi Garesu Da Rakon Allah Yasanyamasu Albarka Acikin Karatunsu Dama Rayiwarsu Baki Daya .

Daga DMA Hausa News 📷

IN NAYI RANTSUWA BAZANYI KAFFARA BA.......  DAGA     MUHAMMAD AHMAD AISAMI NI DAI   Kalli Don Allah Yadda Jami'an Tsaron...
12/11/2023

IN NAYI RANTSUWA BAZANYI KAFFARA BA.......

DAGA
MUHAMMAD AHMAD AISAMI NI DAI

Kalli Don Allah Yadda Jami'an Tsaron Mu S**a Siyar Da Rayuwar Wajan Dakale Siyan Kuru'un Mutane Suke K**a Irin Wadan Nan 6ata Garin Wajan Gyaran Kasar Mu Nigeria Amman Wallahi Bazaka Bini Bashin Rantsuwa Ba Wadan Nan Mutanan Babu Wanda Za'ah Yiwa Tsatstsauran Hukunci Wanda Zaisa Wani Yayi Sha'awar Kwatanta Hakan Nan Gaba......

Don Allah Kalli Idanun Su Don Allah Akwai Alamun Tsoro Ko Nadama Don Allah Sun San Cewa Nan Da A Hours 24 Za'ah Sake Su Sabida 'Yan Siyasar Mu S**a Basu Aikin Shekkenan Kuma Sai Tashin Zance.....

Indai Har 'Yan Siyasar Kasar Mu Nigeria Suna Nan Allah Baza'ah Ta6a Samar Da Tsaro Ba Sabida In Yaran Su S**ai Laifi Sai Su Kirawa Waya Suna Zage-Zage A Sakar Masu Yaran Su In Jami'an Tsaron Sunki Sai A Changer Maka Gun Aiki Kaji Fa.....

Indai Iya Social Media Wannan Hukunchin Zai Tsaya Gwara A Sake Su A Basu Hakuri Tunda Dama Mun Saba Jin Irin Wadan Nan Batutuwan Ko.........

Ya Allah Kai Mana Tsari Da Sharrin Duk Wani Makiyin Kasar Mu Nigeria Ya Allah Ka Daukaka Kasar Mu Nigeria

Zaɓen Gwamnan jihar Kogi bai yiwa Dino Melaye armashi ba, inda ya ce dole a soke zaɓen a canza wani. Ko meye dalili?Ku b...
12/11/2023

Zaɓen Gwamnan jihar Kogi bai yiwa Dino Melaye armashi ba, inda ya ce dole a soke zaɓen a canza wani. Ko meye dalili?

Ku bayyana mana ra'ayoyinku?

TUATARWA:Wannan wata Sabuwar hanyar safarar mak**ai daya k**ata Jami'an tsaro su sani
11/11/2023

TUATARWA:
Wannan wata Sabuwar hanyar safarar mak**ai daya k**ata Jami'an tsaro su sani

Yan banga sun kashe masu garkuwa da mutane 3 a karamar hukumar Ngaski, jihar KebbiYan banga a karamar hukumar Ngaski a j...
11/11/2023

Yan banga sun kashe masu garkuwa da mutane 3 a karamar hukumar Ngaski, jihar Kebbi

Yan banga a karamar hukumar Ngaski a jihar Kebbi sun yi nasarar kashe wasu masu garkuwa da mutane uku da s**a addabi yankin.

Nasarar aikin a cewar ‘yan banga a yankin Makurdi da ke Ngaski ya biyo bayan kame masu ba da labarinsu ne da s**a hada kai wajen bankado maboyar masu garkuwa da mutane a dajin.

Daraktan tsaro na ofishin majalisar zartarwa na Birnin Kebbi, Malam Abdulrahman ne ya bayyanawa manema labarai hakan.

Ya bayyana cewa bayan bayanan sirri da s**a kai ga cafke mai ba da labarin ‘yan fashin, mai bayanin ya amince da kai ‘yan banga zuwa maboyar ‘yan bindigar da ke cikin dajin wadanda s**a yi artabu da ‘yan bangan a musayar wuta.

'Rahotan tsaro da muka samu daga unguwar Makurdi da ke karamar hukumar Ngaski da jami'an 'yan banga s**a yi a jiya ya kai ga k**a wani ma'aikacin da ya yi alkawarin kai mutanen mu maboyar masu garkuwa da mutane.

Ya bayyana cewa, ‘yan banga na yankin sun kwana har zuwa da safe tsakanin karfe 3:30 na safe - 4:30 na safe inda s**a yi nasarar fatattakar ‘yan ta’addan a sak**akon musayar wuta da s**a yi tare da kashe ‘yan fashin uku .

Cikin farin ciki ya ce ‘yan banga sun dawo gida lafiya ba tare da sun samu rauni ba.

AbdulRahman ya yaba da irin namijin kokarin da ’yan banga na yankin ke yi wanda a cewarsa suna yaba kokarin sauran jami’an tsaro wajen yakar matsalar ‘yan fashi da s**a taru.

Ya kuma ce nasarorin da aka samu wajen magance matsalolin tsaro a jihar ba su rasa nasaba da tallafin da gwamnatin Kauran Gwandu ke baiwa jami’an tsaro a jihar bisa tsarin manufofinsa na baiwa tsaro fifiko a jihar.

📷 Mujahid Saleh Saad - Dan maliki Mujahid Saleh Saad

Da Dumi-Dumi: An Harbe Barawon Akwatin Zabe Har Lahira A Jihar KogiRahotanni sun bayyana cewa an harbe wani matashi mai ...
11/11/2023

Da Dumi-Dumi: An Harbe Barawon Akwatin Zabe Har Lahira A Jihar Kogi

Rahotanni sun bayyana cewa an harbe wani matashi mai suna Umoru Iduh a mazabar Agala-Ogane da ke cikin babban birnin Anyigba a karamar hukumar Dekina ta Kogi saboda yunkurin sace kayan zabe.

Majiyar Daily Hausa News ta gano cewa an harbe Iduh ne da misalin karfe 10 na safe yayin da ake shirin fara kada kuri’a a rumfar zabe da ke yankin.

A cewar wani ganau, da ya zanta da wakilin Daily Trust, Marigayi Umoru ya kutsa rumfar zabe da karfin Tuwo inda ya dauki Na'urar tantance masu zabe wato BVAS ya farfasa ta a kasa domin a daina kada kuri’a a rumfar zaben.

"Wani mutum da ake zargin dan banga ne nan take ya fito daga cikin jama’a ya harbe shi, inda nan take ya kashe shi,” in ji Abdullahi Danjuma wanda ya yi ikirarin cewa ya wajan kada kuri’a a lokacin da lamarin ya faru.

Address

Kano

Telephone

+2349046599842

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Duniyar Mu Ayau Hausa News posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share


Other Broadcasting & media production in Kano

Show All