24/01/2022
Mutumin da ake zargi da kisan Hanifa zai gurfana a kotu a yau
Nan gaba a yau Litinin za a gurfanar da mutumin da ake zargi da kisan Hanifa mai shekara biyar, a kotu a birnin Kano.
Hukumomi a Kano da ke arewacin Najeriya za su gurfanar da Abdulmalik Muhammad Tanko ne a Kotun Majistire ta 12 Gidan Murtala.
Ana zargin sa da kashe Hanifa Abubakar mai shekara biyar bayan ya sace ta a watan Disamba.
Za mu kawo muku ƙarin bayani da zarar mun samu...
Ranar Lahadi da dare wasu fusatattun matasa s**a ƙona makarantar da Hanifa ke zuwa kafin rasuwarta, inda a nan ne wanda ake zargin ya ce ya binne gawarta bayan ya kashe ta. Kazalika shi ne mai makarantar.
Kisan Hanifa ya harzuƙa 'yan Najeriya a ƙarshen makon da ya gabata, inda wasu ke ta kiran da a gaggauta yanke masa hukunci bayan ya amsa laifinsa a hannun 'yan sanda cikin wani bidiyo da 'yan sandan Kano s**a wallafa a Facebook.