Muryar Malamai

Muryar Malamai Tashar Muryar Malamai ita ce Hanya mafi sauki da zaka koyi Addinin ka!

29/01/2023

Sihiri

29/01/2023

A KULA DA MARAYU!

Canjin Kudi: jan Hankali Ga Al’umma Da Shugabannin Bankuna:1. Muna godiya ga Gwamnati da ta saurari kiraye-kirayen al’um...
29/01/2023

Canjin Kudi: jan Hankali Ga Al’umma Da Shugabannin Bankuna:

1. Muna godiya ga Gwamnati da ta saurari kiraye-kirayen al’umma ta kara wa’adin amfani da tsofaffin takardun kudade har zuwa 10 ga February. Allah ya kara masu juriya da hakuri wajen gudanar da mulkinsu.

2. Sannan muna kira ga jama’a lalle su yi amfani da wannan damar, don ganin sun shigar da tsofaffun takardun kudadensu cikin asusuwansu na banki domin guje wa fada wa asara.

3. Muna kuma jan hakanlin shugabannin Bankuna da ma’aikatansu da su taimaka wa jama’a wajen karbar tsofaffin kudadensu idan sun kawo, sannan su ba su sababbi idan sun bukata, kamar yadda doka ta tanada. Su kuma guji karkatar da sababbin takardun kudade zuwa ga wasu masu uwa a gindin murhu, don cim ma wata bukata tasu ta karankansu, ko wata mummunar manufa. Allah yana sane da duka wani mabarnaci, kuma ba zai ga da kyau ba.

4. Hakanan lalle mutane su guji karbar kari wajen canja tsofaffun takardun kudi da sabbbi, domin aikata haka haramun ne, riba ce karara a Musulunci.

5. Allah ka ba mu ikon cinye wannan jarrabawa lafiya. Ka kara wa kasarmu kwanciyar hankali sa zaman lafiya da arzuki mai dorewa. amin.

Muhammad Sani Umar
Doha, Qatar,
January 29th, 2023.

28/01/2023
Canjin Takardun Kudi: Kira Zuwa Ga Hukuma1. Allah (SWT) yakan zo da abubuwa masu dadi da marasa dadi a rayuwa, don su za...
28/01/2023

Canjin Takardun Kudi: Kira Zuwa Ga Hukuma

1. Allah (SWT) yakan zo da abubuwa masu dadi da marasa dadi a rayuwa, don su zamanto jarraba wa ga bayinsa, domin ya bayyana wadanda s**a fi kyautata ayyukansu. Wajibi ne ga duk wani Musulmi ya rika halarto da wannan ma’ana a zuciyarsa duk sanda ya ga an shiga wani yanayi bako a rayuwa. Ya yi kuma kokarin cinye wannan jarrabawa.

2. Hukumar samar da takardun kudade karkashin babban bankin Kasa, tare da sahhalewar Shugaban Kasa sun yi tunanin sake fasalin wasu takardun kudaden Nigeria domin wasu maslahohi da s**a hango da kuma magance wasu matsaloli. Muna musu kyakkyawan zato cikin wannan kuduri nasu, muna kuma fatan a yi nasara cikin hakan.

3. Amma duk da haka, wajen tabbatar da waccan kyakkyawar manufa, talakawa a Nigeria, sun shiga wani mawuyacin hali kuma mai ban tausayi, musamman a kauyukanmu na Arewa. Don haka muna rokon hukumar da wannan abu ya shafa da su duba halin da Jama’a suke ciki, su amsa kiraye-kirayen al’umma na kara wa’adin da s**a saka na dakatar karbar tsofaffin kudi, ko kuma su yi wa tsarin gyaran fuska, don fitar da al’umma daga wannan kangi mawuyaci.

4. Shugabanci na kwarai har koyaushe yana aikata abin da zai saukakewa al’umma rayuwarsu ne ta yau da kullum, da kuma sama musu walawala a harkokinsu, da guje wa jefa su cikin tsanani da wahalhalu.

5. Fatanmu hukuma za ta dubi wannan lamari ta kuma yi abin da ya dace. Allah ya musu kyakkyawan jagoranci, ya ba mu zamanan lafiya da arzuki mai dorewa a Kasarmu. Amin.

Muhammad Sani Umar
Doha- Qatar
January, 28th, 2023.

27/01/2023
10/01/2023

Raddi mai Zafi.

Muhadara!           Muhadara !!    Muhadara!!!In Sha Allahu Yau LAHADI idan Allah Ya kaimu akwai MuhadaraTareda 👇👇Dr. Ja...
08/01/2023

Muhadara! Muhadara !! Muhadara!!!

In Sha Allahu Yau LAHADI idan Allah Ya kaimu akwai Muhadara

Tareda 👇👇

Dr. Jameel Muhammad Sadis Zaria

Dr. Ibrahim Umar Adam Disina(Director Sunna Tv)

Wuri👇👇
Masallacin Indimi Dake kan titin Indimi Anan Garin Maiduguri, Borno State.

Lokaci:👇👇
Sakanin Magariba Zuwa Isha'i

Date:Lahadi 8-1-2023=15-6-1444
Allah yabada ikon Zuwa
Sai kunzooo

https://youtu.be/MOp2niLevEc
02/01/2023

https://youtu.be/MOp2niLevEc

Samu karatuttuka da za su taimake ka wajen inganta rayuwa da gyara alaqar ka da Allah s.w.t ta hanyar wannan tasha tamu mai Albarka MURYAR MALAMAI.kayi subsc...

https://youtu.be/aGbIurip4Ko
30/12/2022

https://youtu.be/aGbIurip4Ko

Samu karatuttuka da za su taimake ka wajen inganta rayuwa da gyara alaqar ka da Allah s.w.t ta hanyar wannan tasha tamu mai Albarka MURYAR MALAMAI.kayi subsc...

https://youtu.be/Bj5j85Rx8Xg
27/12/2022

https://youtu.be/Bj5j85Rx8Xg

Samu karatuttuka da za su taimake ka wajen inganta rayuwa da gyara alaqar ka da Allah s.w.t ta hanyar wannan tasha tamu mai Albarka MURYAR MALAMAI.kayi subsc...

27/12/2022

Kayi kokari kaci Halal - Dr. Abdallah Gadon Kaya

https://youtu.be/aej317BZSqQ
26/12/2022

https://youtu.be/aej317BZSqQ

Samu karatuttuka da za su taimake ka wajen inganta rayuwa da gyara alaqar ka da Allah s.w.t ta hanyar wannan tasha tamu mai Albarka MURYAR MALAMAI.kayi subsc...

26/12/2022

Dole ne mu yabi Kwankwaso da Ganduje || Sheikh. Kabiru Haruna Gombe (H)

26/12/2022

Labarin Wani Matashi mai ban mamaki

BIKIN KIRSOMETI: BIDI'A KO MAGUZANCI? Daga Shiekh (Dr.) Muhammad Sani Umar R/Lemu.KIRSIMETI shi ne bikin haihuwar Annabi...
25/12/2022

BIKIN KIRSOMETI: BIDI'A KO MAGUZANCI?

Daga Shiekh (Dr.) Muhammad Sani Umar R/Lemu.

KIRSIMETI shi ne bikin haihuwar Annabi Isa (AS) a wajen kiristoci, kuma shi ne na biyu bayan bikin Easter. Yana farawa 24 December cikin dare, da kuma Ranar 25, a lissafin kalandar Gregory (Gregorian Calendar). Amma a lissafi (Julian Calendar) yana kamawa ne daidai da 6 da 7 watan January.

Littafin Bible bai ambaci ranar haihuwar Annabi ISA ba, b***e ma ya yi maganar biki a wannan ranar. Malaman kiristoci ne s**a yi taro a shekara ta 325 (Midiyya) s**a kirkiro shi don ya zama addini a gurinsu.

Masana Tarihi suna cewa ranar 25 December rana ce da maguzawan Rumawa suke bikin bautar rana a cikinta, don haka Malaman kirista s**a zabe ta don ta zama ranar haihuwar Annabi Isa (AS) kuma su rike ta ranar biki, domin suna cewa shi ma Annabi Isa (AS) wani Haske ne sabo da ya zo Duniya mai K**a da hasken rana.

Daga nan za ka fahimci cewa shi wannan bikin na KIRSIMETI bidi'a ce a shi Kansa addinin na kiristoci, kuma asalinsa maguzanci ne a ka sa masa rigar addini.
To idan ya kasance bidi'ar da take cikin musulunci bai halatta ga musulmi ya girmama ta ba, ko ya taya mai yin ta murna yayin da yake aikata ta, to ina kuma ga bidi'ar da take cikin wani jirkitaccen addini, wacce kuma ta samo a sali daga Maguzancin Rumawan farko?! Allah ya ganar da mu. Ameen.

24/12/2022

Gare ku masu kare Prof. Maqari daga bakin Dr. Idris Abdulazeez

21/12/2022

IYAYE MAZA KU JI TSORON ALLAH

Allah ka shiya mana.
17/12/2022

Allah ka shiya mana.

14/12/2022

HATTARA KADA KA ZAMA CIKINSU

Address

Kano

Opening Hours

Monday 09:00 - 17:00
Tuesday 09:00 - 17:00
Wednesday 09:00 - 17:00
Thursday 09:00 - 17:00
Friday 09:00 - 17:00
Saturday 09:00 - 17:00
Sunday 09:00 - 17:00

Telephone

+2348028390142

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Muryar Malamai posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Muryar Malamai:

Videos

Share

Category


Other Media Agencies in Kano

Show All

You may also like