![Shugaban Kwamitin Sojojin Najeriya na Majalisar Dattawa Ya Jagoranci Kare Kasafin Kuɗin RundunarShugaban Kwamitin Sojoji...](https://img5.medioq.com/861/216/1035419078612167.jpg)
14/01/2025
Shugaban Kwamitin Sojojin Najeriya na Majalisar Dattawa Ya Jagoranci Kare Kasafin Kuɗin Rundunar
Shugaban Kwamitin Sojojin Najeriya na Majalisar Dattawa, Sanata Abdul'aziz Musa Yar'adua ya jagoranci aikin kare kasafin kuɗin Rundunar Sojojin Najeriya na Dokar Kasafin Kuɗi ta 2025.
Wannan aiki ya gudana ne domin tabbatar da cewa an yi la’akari da buƙatun rundunar a cikin kasafin kuɗin ƙasar.
A yayin kare kasafin kudin, Sanatan da sauran abokan aiki sa a cikin kwamitin sun yi jinjina ga Rundunar Sojojin Najeriya bisa yadda ta yi aiki tuƙuru a cikin shekarar da ta gabata domin tabbatar da tsaron ƙasarmu.
Haka kuma sun jajirce wajen ware kuɗi masu yawa domin tabbatar da cewa Rundunar ta samu kayan aikin da s**a dace domin ci gaba da kare ƙasar Najeriya.