*RIYADUL JANNAH CHARITY FOUNDATION*
Assalamu Alaikum mun san ana kokari kwarai da gaske. Allah ya cigaba da ninka arziki. Wannan bawan Allah da zamu gani sunansa Mukhtar Muhammad dan shekara 50. Yana zaune ne a unguwar Shago Tara dake Kurna. Allah ya jarrabeshi da larurar karaya a hannu da cinya bayan hadarin mota da sukayi tun a wasu watanni da suka gabataðŸ˜. Bayan wannan hadari sai da yayi wata uku baya hayyacinsa ðŸ˜. Bayan ya dawo hayyacinsa ne aka yi aiki a hannun da cinyar. Bayan aikin kuma da sallamar shi gida, aka sake samun wata karayar a karshen kashin cinyarsa sakamakon karfen da aka saka a aikin farko yayi tsayi ya wuce inda ya kamata ya tsaya. An saka ranar sake aiki tun kimanin wata daya daya gabata. Amma saboda ba halin biyan kudin har lokacin ya wuce yana gida ðŸ˜. Bayan wannan matsalar sunyi iya kokari na su samu kudin biya ayi sabon aiki amma abun ya gagara saboda haka ne suke neman taimakon yan uwa bayin Allah domin ayi masa aikin ya rabu da kwanciyar watanni masu yawa a waje daya hannu da kafa a kakkarye ðŸ˜. Kudin aiki da gwaje gwaje da magunguna (wanda bamu san adadin da za a rubuta ba) sun wuce N240,000. Saboda haka ne muka yanke shawarar hada masa N250,000. Ga mai niyya da ikon bayar da duk abinda Allah ya hore, ga lambar ajiyarmu ta banki:
6849020020
FCMB
Riyadul Jannah Charity Foundation
Ga mai neman karin bayani zai iya tuntubar wannan lambar 07032247837. Allah ya iya mana, yasa mukai ga nasara. Amin ya Allah!
14/12/2021
https://youtu.be/AGpyEfwQGsY
Mata masu Harkar kasuwanchi ku kula dasu a wannan zamanin.. Dr. Abdullah Usman Gadon Kaya.
Subscribe to khairiyyah TV on YouTube
https://youtu.be/1kHUGKDSnBc
Danna subscribe sannan ka dannan kararrawar sanarwa a duk lokacin da muka dora sabon video.
Khairiyyah TV Domin samun sababbin karatukan malaman Sunnah a sauqaqe.
Danna subscribe sannan ka dannan kararrawar sanarwa a duk lokacin da muka dora sabon video.
Khairiyyah TV Domin samun sababbin karatukan malaman Sunnah.
https://youtu.be/1kHUGKDSnBc