Zinariya

Zinariya Jaridar Zinariya jarida ce mai tsage gaskiya komai ɗacinta ga al'umma da kuma kawo ingantattun labari

CIKIYA CIKIYA CIKIYA CIKIYAAna  cikiyar yarinyar nan Mai suna  Nana KHADIJA.Ta bar GIDA Anguwar Rogo, a Jos jiya  karfe ...
21/12/2024

CIKIYA CIKIYA CIKIYA CIKIYA

Ana cikiyar yarinyar nan Mai suna Nana KHADIJA.

Ta bar GIDA Anguwar Rogo, a Jos jiya karfe 5 Na yamma tana sanye da doguwar riga yellow da blue din wando.

Duk wanda Allah yasa ya ganta yakira wannan number 08038524629 Allah ya baiyyana ta.

21/12/2024

Yau Asabar, azumi saura kwanaki 71 da yardar Allah.
Allah nuna mana watan Ramadan da rai imani.

"Da malamai za su kare mutuncinsu, su ƙauracewa kwaɗayi, maula da kujerar Umara da abubuwa sun gyaru a ƙasar nan." Sheik...
20/12/2024

"Da malamai za su kare mutuncinsu, su ƙauracewa kwaɗayi, maula da kujerar Umara da abubuwa sun gyaru a ƙasar nan."

Sheikh Abdulwahab Abdallah

Zinariya

20/12/2024

Labaran Zinariya TV na yau

IDAN BA MUTUWA AKWAI TSUFAWannan baiwar Allahn ita ce Hajiya Indo Musawa Wacce Mamman  Shata  ya yi wa waƙa. A cikin waƙ...
20/12/2024

IDAN BA MUTUWA AKWAI TSUFA

Wannan baiwar Allahn ita ce Hajiya Indo Musawa Wacce Mamman Shata ya yi wa waƙa.

A cikin waƙar yana cewa, "wata 'yar yarinya, mai kyan diri da kyan tsari, mai kyan zama da kyan tafiya ga alkawari kamar tawada, ga dadin riko kamar chasbi Indon Musawa."

Ance a lokacin su, duk garin Musawa babu mai kyan ta.

Daga Muktar Maigamo

Mai martaba Sarki, na saurari bayanin mutane da dama akanka, jama'a gabadaya sunyi tarayya akan cewa " KAI MUTUMIN KIRKI...
20/12/2024

Mai martaba Sarki, na saurari bayanin mutane da dama akanka, jama'a gabadaya sunyi tarayya akan cewa " KAI MUTUMIN KIRKI NE". A don haka ina maka nasiha akan kada ka sauya daga wannan tafarkin da mutane s**a shedeka akai har ka koma ga Allah.

- Inji Sheikh Abdulwahab Abdallah.

20/12/2024

Yau Jumma'a, azumi saura kwanaki 72 da yardar Allah.
Allah nuna mana watan Ramadan da rai imani.

"Bana goyon bayan dukan yara idan s**a yi laifi. Idan yarona yayi fushi duk abinda yake kusa da shi yake fasawa. Yanzu h...
20/12/2024

"Bana goyon bayan dukan yara idan s**a yi laifi. Idan yarona yayi fushi duk abinda yake kusa da shi yake fasawa. Yanzu haka ya fasa talabijin uku saboda na ɓata mishi rai."

Don haka iyaye ku daina dukan Ƴaƴanku saboda sun yi muku laifi" Cewar Bovi

Shin iyaye me za ku ce?

"Ya Kamata 'Yan Nijeriya Su Yi Koyi Da Halayen Buhari Saboda Abin Duniya Bai Dame Shi Ba" Garba Shehu A lokacin da aka k...
19/12/2024

"Ya Kamata 'Yan Nijeriya Su Yi Koyi Da Halayen Buhari Saboda Abin Duniya Bai Dame Shi Ba" Garba Shehu

A lokacin da aka kawo mishi fom ya cike na kyautar fili a Abuja lokacin yana kan mulki, shi mayar da fom ɗin shi yayi ya ce yana da fili wanda aka bashi bayan ya gama aikin soja. Don haka a ba waɗanda basu da shi.

Me za ku ce?

Zinariya

LABARI CIKIN HOTUNA: Mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima ya gudanar da Umrah a yau Alhamis a ƙasa mai tsarki. ...
19/12/2024

LABARI CIKIN HOTUNA: Mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima ya gudanar da Umrah a yau Alhamis a ƙasa mai tsarki.

Shettima ya samu kyakkyawar tarba daga manyan jami'an gwamnatin Saudiyya kafin daga bisani ya wuce Makkah domin yin ɗawafi.

Ya kuma yi wa Najeriya addu'a a lokacin Umrah ɗin.

📸 - Ofishin mataimakin shugaban Najeriya

19/12/2024

Yau Alhamis, azumi saura kwanaki 73 da yardar Allah.
Allah nuna mana watan Ramadan da rai imani.

Mai Martaba Sarkin Gombe Alh (Dr.) Abubakar Shehu Abubakar lll CFR Ya Cika Shekaru 47 Cif da Aihuwa.Wanne fata zaku mish...
18/12/2024

Mai Martaba Sarkin Gombe Alh (Dr.) Abubakar Shehu Abubakar lll CFR Ya Cika Shekaru 47 Cif da Aihuwa.

Wanne fata zaku mishi?

Mun daina rusau sai dai mu kai mutum kurkurku kai-tsaye - Gwamnatin Kano Hukumar Tsara Birane ta Jihar Kano, KNUPDA ta c...
18/12/2024

Mun daina rusau sai dai mu kai mutum kurkurku kai-tsaye - Gwamnatin Kano

Hukumar Tsara Birane ta Jihar Kano, KNUPDA ta ce daga yanzu ta daina rusa gine-gine da aka yi ba bisa ƙa'ida ba, sai dai kawai ta aika wanda ya karya dokar zuwa gidan yari kai tsaye.

Da ya ke zantawa da manema labarai a ofishin sa, shugaban hukumar, Arc. Ibrahim Yakubu Adamu ya ce sashe na 11 da na 12 da na 13 da na 14 da na 15 na dokar da ta kafa KNUPDA sun tanadi hukuncin gidan yarin na shekara ɗaya, har ma da cin tara ga wanda ya karya dokar hukumar.

Daily Nigerian

18/12/2024

Yau Laraba, azumi saura kwanaki 74 da yardar Allah.
Allah nuna mana watan Ramadan da rai imani da lafiya.

LABARI DAGA DAURA: Tsohon shugaban ƙasar Najeriya Muhammadu Buhari ya karɓi baƙuncin ƴan kasuwa, sarakunan yankin Yarbaw...
17/12/2024

LABARI DAGA DAURA: Tsohon shugaban ƙasar Najeriya Muhammadu Buhari ya karɓi baƙuncin ƴan kasuwa, sarakunan yankin Yarbawa da manyan jami'an gwamnati a yayin da yake bikin cika shekaru 82 da aihuwa

Vinicius Jr. Ne Gwarzon dan Wasan FIFA na 2024.Vinicius Jr ya yi fin tin kau, A tsakanin ƴan wasa 10 da s**a haɗa da Rod...
17/12/2024

Vinicius Jr. Ne Gwarzon dan Wasan FIFA na 2024.

Vinicius Jr ya yi fin tin kau, A tsakanin ƴan wasa 10 da s**a haɗa da Rodri da Bellingham da Messi.

Vinicius ya lashe kofin Champions League, da La Liga, da UEFA Super Cup, da Spanish Super Cup duk a sekarar 2024.

Zinariya

17/12/2024

Yau Talata, azumi saura kwanaki 75 da yardar Allah.
Allah nuna mana watan Ramadan da rai imani da lafiya.

Address

Abuja
Anglo Jos
80073

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Zinariya posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Videos

Share