01/11/2025
Hutunan Yadda Matar Gwamnan Jihar Katsina Hajiya Fatima Dikko Raɗɗa Ta Jagoranci Bikin Ranar Masu Cutar Kansar Mama Ta Duniya A Katsina
Matar Gwamnan Jihar Katsina, Hajiya Fatima Dikko Umar Radda, wacce aka fi sani da Zinariyar Gwagwaren Katsina, ta jagoranci gagarumin gangamin bikin Ranar Tunawa da Masu Cutar Kansar Mama ta Duniya a jihar Katsina, a wani shiri mai cike da wayar da kan Mata kan ilimantarwa ga Mata da al’umma baki ɗaya.
Taron, wanda ya samu halartar mata daga sassa daban-daban na jihar, ya mayar da hankali kan wayar da kan jama’a musamman mata kan muhimmancin duba lafiyar mama akai-akai, domin gano matsaloli tun kafin su tsananta da kuma kare lafiyarsu daga cutar kansar mama.
A cikin jawabin ta, Hajiya Fatima Dikko Radda ta jaddada cewa,
“Gano cutar tun da wuri na iya ceto rai, kuma hakan yana bukatar ilimi, kulawa da karfafa gwiwar mata su rika zuwa asibiti don binciken lafiyarsu.”
An fara gangamin ne daga Tsohon Gidan Gwamnatin Jihar Katsina, inda aka gudanar da tafiya mai ɗauke da sakonnin wayar da kai, sannan aka kammala taron a Filin Wasannin Muhammadu Dikko, inda daruruwan mata, matasa da kungiyoyi s**a halarta cikin nishadi da sha’awa.
A yayin taron, an gudanar da gwajin cutar kansar mama kyauta ta amfani da na’urori na zamani, tare da bayar da shawarwari daga kwararrun likitoci kan hanyoyin kariya da gano cutar tun da wuri.
Wannan gangami ya gudana ne da haɗin gwiwar Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Katsina, cibiyoyin lafiya masu zaman kansu, da ƙungiyoyi masu rajin kare lafiyar mata, domin ƙara wayar da kai da rage yawan mace-macen da ke da nasaba da kansar mama.
Ranar 15 ga watan Oktoban kowace shekara ne sai, Majalisar Dinkin Duniya ta ware a matsayin Ranar Tunawa da Masu Cutar Kansar Mama ta Duniya, kuma Katsina ta gudanar da nata bikin a ranar Alhamis, 30 ga watan Oktoba, 2025, ƙarƙashin jagorancin Zinariyar Gwagwaren Katsina, wadda take nuna alama ta tausayi, jajircewa da kishin lafiyar mata a jihar.
“Lafiyar mace ginshiƙi ce ta ƙasa. Idan mata sun kasance lafiya, al’umma ma zata kasance lafiya,” in ji Hajiya Fatima Dikko Radda.
Taron ya zama abin yabo da jan hankali ga mata, matasa da kungiyoyin al’umma da dama, inda aka yaba da irin jajircewar matar gwamnan wajen kare lafiyar mata da ƙarfafa su wajen kula da jikinsu.