Jamhuriyya

Jamhuriyya Domin samun ingantattun kuma sahihan labaran kasa dana ketare hadi da labaran wasanni kasance da jar

Ganduje zai mika mulki ranar Lahadi domin halartar bikin rantsar da zababben shugaban kasa TinubuGwamnan jihar Kano mai ...
28/05/2023

Ganduje zai mika mulki ranar Lahadi domin halartar bikin rantsar da zababben shugaban kasa Tinubu

Gwamnan jihar Kano mai barin gado, Dr. Abdullahi Umar Ganduje zai gudanar da aikin mika ayyukan jihar a hukumance ga zababben gwamnan, Engr. Abba Kabir Yusuf. Inji Muhammad Garba

Malam Garba ya yi nuni da cewa kwamitocin mika mulkin guda biyu sun gana a cikin satin da ya gabata inda aka gabatar da takardar mikawa kwamitin da aka zaba na gwamna tare da aiwatar da ajandar da ta dace kan bikin mika mulki.

Kwamishinan ya bayyana cewa Gwamna Ganduje zai tafi Abuja a matsayin shugaban tawagar Kano don kaddamar da zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a ranar Litinin, 29 ga watan Mayu.

Ya ce tafiyar gwamnan ta kuma zama tilas ne don kaucewa wa’adin rufe filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe Internation Abuja domin bikin rantsuwar.

Sanarwar ta yi kira ga jama’a da su ci gaba da yi wa jihar addu’ar zaman lafiya da ci gaba.

Thiago Silva a kan dalilin da ya sa ya tsawaita kwantiraginsa a watan Fabrairu:  "Ba don kudi ba ne, Saboda soyayyar da ...
28/05/2023

Thiago Silva a kan dalilin da ya sa ya tsawaita kwantiraginsa a watan Fabrairu:

"Ba don kudi ba ne, Saboda soyayyar da nake yi wa kulob din, na yi imanin kulob din yana bukatata a wannan lokacin, a ciki da wajen fili, don sake gina fasalin kulob din, Ina ganin tsantsar soyayyar magoya bayan Chelsea.”

Fagen Wasanni

Yanzu yanzu:Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kara wa'adin ci gaba da amfani da tsaffin kudi har zuwa ranar 10 ga watan ...
16/02/2023

Yanzu yanzu:
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kara wa'adin ci gaba da amfani da tsaffin kudi har zuwa ranar 10 ga watan Afrelu, 2023.

Sai dai, shugaban kasar ya ce iya tsohuwar Naira dari ce ne kawai bankuna za su ci gaba da ba 'yan Nigeria, banda N500 da N1,000.

A Daure Duk Dan Kasuwar Da Ke Shigo Da Tufafi Daga Kasar Waje: DangoteA jawabinsa:“Ga masana’antar saƙar tufafi, na yi i...
10/02/2023

A Daure Duk Dan Kasuwar Da Ke Shigo Da Tufafi Daga Kasar Waje: Dangote

A jawabinsa:

“Ga masana’antar saƙar tufafi, na yi imanin ya k**ata gwamnati ta tsara doka a Majalisar Dokoki ta ƙasa da za ta sa duk wanda ya sayar da kayan saƙar tufafi na ƙasashen ƙetare da aka haramta, dole ne ya fuskanci zaman gidan yari ba tare da ba shi zaɓin biyan tara ba. Don haka za a ɗaure shi ne kawai, ko da na shekara biyu ne kawai.

"Ainihin da ke faruwa a masana'antar saƙar tufafi ba tsadar wutar lantarki ba ne. Harkar saƙar tufafi ba za ta yiwu ba idan kuka ba su wuta mai rahusa amma ana ci gaba da fasa ƙwauri."

"Abin da ke faruwa shi ne, kamfanonin ƙasashen waje suna hankaɗo da kayayyakinsu Najeriya.

"Shi ya sa ba na son shigo da kayayyaki daga kasashen waje. Lokacin da kuke shigo da kaya, kuna shigo da talauci ne tare da fitar da wadata da guraben aikin yi."

Kasashe a duk fadin duniya na aika wa kasar Turkiyya da Syria kayan agaji bayan da s**a fuskanci girgizar kasa mai tsana...
09/02/2023

Kasashe a duk fadin duniya na aika wa kasar Turkiyya da Syria kayan agaji bayan da s**a fuskanci girgizar kasa mai tsanani.

A cikin kayan akwai ruwan sha da barguna da kayan abinci da kayan sawa, da dai sauransu.

Ƙalubalen da ƴaƴa mata suke fuskanta a yayin da suke son ci gaba da karatu a makarantar gaba da sakandare.Wasu daga ciki...
05/02/2023

Ƙalubalen da ƴaƴa mata suke fuskanta a yayin da suke son ci gaba da karatu a makarantar gaba da sakandare.

Wasu daga cikin iyayen su na da dabi'ar nan ta yayansu ci gaba da karatu musamman a yankin arewacin Najeriya, bayan Yara. Sun kammala malarantun sikandire.

Wasu iyayen kan Yi togaciya da cewa aure yaran za su yi, ba karatu ba, Koda kuwa a lokacin yarinya Bata da wani tsayayye.

ƴan mata da yawa na fuskantar barazana a yayin da iyayensu ke dakile musu ci gaba da karatu saboda maganar aure.

Hakan na nufin bayan mace ta gama sakandare sai ta ci gaba da zama a gida babu karatu babu sana'a, kuma suna da burin yin karatu a rayuwar su amma babu hali kasancewar iyayensu basa son karatun.

Hakan na jefa rayuwar matan a cikin garari, saboda saboda zama waje daya, babu wani abin yi ga bukatun rayuwa daban daban babu mai iya daukar nauyin yi su, sanadin hakan ƴan mata dayawa sun zaɓi su bayar da kansu domin abasu kudi su biyawa kansu bukatar gaban su.

Wasu iyayen suna kallo yarinyar su na kashe kashen kudi ko Siyan sutura masu tsada amma ba za su tambayi inda ta samu kudin ba.

Sak**akon rashin sanin makomar su a rayuwa babu tsayayyen saurayi bare suyi tunanin aure,suna da burin suyi karatu mai zurfi domin cimma wani buri da suke son cimma a rayuwa, Hakan ya gagara daga bangaren iyayen su.

Wani Karin ƙalubalen shine yadda wasu daga cikin iyaye s**an hana ƴar su tayi aiki yayin da tayi karatu mai zurfi amma su ce baza tayi aiki ba ta zauna a gida har sai ta samu miji tayi aure, alhalin wasu ko saurayi basu dashi sun gama karatu sun karɓi sak**ako mai kyau amma iyayen su sun hana su suyi aiki gani suke barin Mace tayi aiki k**ar lalacewa za tayi.

Wadannan dama wasu Taron kulabalen na Nan Jingim, Wanda hakan ke bukatar mahukunta su Kara tsayawa a tsaye wajen yaki da wannan matsala.

Za a iya cimma nasara kan hakan ta hanyar tuntubar iyayen cikin harshe na laushi, Wanda watakila a iya jawo hankalin su domin su sauka daga kan wan can ra'ayi nasu na rikau.

Daga salma Hussain Abubakar

Gwamnan CBN Karya Yake Yiwa Shugaba Buhari: Mai Magana Da Yawun Shugaban KasaBabban hadimin shugaban kasa kan lamuran ja...
05/02/2023

Gwamnan CBN Karya Yake Yiwa Shugaba Buhari: Mai Magana Da Yawun Shugaban Kasa

Babban hadimin shugaban kasa kan lamuran jama'a, Ajuri Ngelale, ya bayyana cewa karyar kawai gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele, ya shararawa shugaba Muhammadu Buhari. Ngelale yace maganar cewa akwai isassun kudi a cikin gari babu kamshin gaskiya ciki,

Ya bayyana hakan ne a hirar da ya gabatar a tashar TVC inda yace mutane su daina ganin laifin shugaba Buhari, bayanan da ya samu yake amfani da su.

Ya ce mutane bai zai taba yin abu don tsanantawa jama'a da gayya ba. A cewarsa: "Abinda muke yi shine tabbatar da cewa shugaban kasa na samun labaran gaskiya kuma labarin da CBN ya bada cewa an baiwa bankuna isassun kudi a fadin tarayya karyar banza ne. Wannan ya bayyana yanzu."

"Shugaban kasa na jama'a ne, labaran karya kawai yake samu daga wajen CBN, shi yasa aka kara wa'adin daga Junairu 31 zuwa 10 ga Febrairu."

Daga Salma Hussain Abubakar

Cika baki ba naka bane, ka roki Allah ya yafe maka bala’o’in da ka dirka wa mutanen Kaduna shi ya fi maka – Rundunar Pet...
05/02/2023

Cika baki ba naka bane, ka roki Allah ya yafe maka bala’o’in da ka dirka wa mutanen Kaduna shi ya fi maka – Rundunar Peter Obi ga El-Rufai

Rundunar Kamfen din dan takarar shugaban kasa na Labour Party, Peter Obi sun maida wa gwamnan Kaduna da martani cewa maimakon cika baki da yaki yi a kafafen yada labari, abinda ya fi dace masa shine ya yi gaggawar komawa ga Allah ya nemi gafarar sa kan bala’o’in da ya gallaza wa mutanen Jihar Kaduna.

Idan ba’a manta ba El-Rufai ya bayyana a hira da yayi da talbijin din Channels cewa Peter Obi yan a batya ruwa ne kawai amma ba tsairin da za suyi a zaben shugaban kasa da ya karato a kasar nan.

El-Rufai ya ce Obi na yin amfani da kabilanci da addini ne a wajen neman jama’a wanda hakan ba zai sa ya samu abinda yake so ba a zabe mai zuwa.

A martani da rundunar s**a maida wa gwamnan, Darekta janar din rundunar Kamfen din Obi Akin Osuntokun ragargaji gwamnan inda yake cewa shine gogarmar nuna kiyayya da kabilanci, domin shine ya fara yin haka a Kaduna inda ya yakice wani bangaren jihar ya kirkiro muslim-muslim.

” Ina so in sanar da El-Rufai, idan aka da sahihin zabe a kasar nan, tabbas Obi na LP ne zai yi nasara, ko shakka babu. Abu daya da na sani shine ko Obi ya yi nasara ko bai yi nasara ba ya kafa tarihi a kasar nan.

DA ƊUMI-ƊUMI: Gwamnan Jigawa ya naɗa sabon Sarkin DutseGwamna Muhammad Badaru Abubakar na jihar Jigawa ya amince da nadi...
05/02/2023

DA ƊUMI-ƊUMI: Gwamnan Jigawa ya naɗa sabon Sarkin Dutse

Gwamna Muhammad Badaru Abubakar na jihar Jigawa ya amince da nadin Muhammad Hameem Sanusi a matsayin sabon Sarkin Dutse daga yau Lahadi.

Hakan ya biyo bayan amincewar kwamitin mutane bakwai na masu naɗa Sarki a masarautar Dutse, inda su ka zaɓi Muhammad Hameem a matsayin sabon Sarkin Dutse da dukka kuri’u bakwai a cikin ‘yan takara uku da ke neman kujerar sarauta.

Nadin dai ya zo ne ƙasa da kwanaki bakwai da rasuwar Sarkin Dutse, Nuhu Muhammadu Sanusi.

An tattaro cewa, daga bisani an mika wannan amincewa ga majalisar Sarakunan Jihar Jigawa, wacce ita ma ta amince da matakin da masu naɗa Sarkin su ka ɗauka.

Sanarwar ta ce Majalisar Sarakunan ta aike da sunan Muhammad Hameem, wanda ɗan marigayi Sarkin Dutse ne, da sauran ’yan takara biyu zuwa wajen neman amincewa.

A cikin sakon fatan alheri ga sabon sarki, Gwamna Badaru ya taya sarkin murna tare da yi masa fatan Allah ya shiryar da shi, da hikima da kuma kariya a tafarkinsa.

🟨 Yalon katin da Vinicius Jr ya samu zai sanya Ba zai buga wasan La Liga na Real Madrid na gaba da Elche CF ba.Daga Fage...
05/02/2023

🟨 Yalon katin da Vinicius Jr ya samu zai sanya Ba zai buga wasan La Liga na Real Madrid na gaba da Elche CF ba.

Daga Fagen wasannin

Atiku Abubakar Ya Samu Kyakkyawar Tarba A Wurin Al-ummar Jihar SokotoA yau Talata mai girma wazirin Adamawa Alhaji Atiku...
01/02/2023

Atiku Abubakar Ya Samu Kyakkyawar Tarba A Wurin Al-ummar Jihar Sokoto

A yau Talata mai girma wazirin Adamawa Alhaji Atiku Abubakar, ya kaddamar da yakin neman zaben shi a jihar Sokoto.

Al-ummar jihar Sokoto sun yiwa Atiku Abubakar Kyakkyawar tarba tare da nuna tsantsar kauna a yayin da ya ziyarci jihar.

A yayin gudanar da taron, al'ummar jihar Sokoto sun yiwa mai girma wazirin Adamawa alkawarin kuri'un su nashi ne.

Insha'Allah Atiku Abubakar zai zama shugaban kasar Najeriya, kawai lokaci muke jira.

Saudiyya ta amincewa Ronaldo yai zaman dadiro da sahibar sa GeorginaRahotanni daga kasar Saudiyya na nuni da cewa Cristi...
08/01/2023

Saudiyya ta amincewa Ronaldo yai zaman dadiro da sahibar sa Georgina

Rahotanni daga kasar Saudiyya na nuni da cewa Cristiano Ronaldo da sahibar sa, Georgina Rodriguez za su sami takardar izinin zama tare, duk kuwa da dokar da ƙasar ta yi mai tsauri a kan zaman dadiro.

Dan wasan mai shekaru 37 ya koma Al-Nassr ta Saudiyya kan kwantiragin shekara biyu da rabi ta kimanin fam miliyan 173 a kakar wasa bayan kwantiraginsa da Manchester United ta rushe.

Sai dai kuma zaman Ronaldo tare da Georgina zai kasance karya dokar auratayya a Saudiyya.

A cewar jairdar wasanni ta Sport, Ronaldo mai ƴaƴa biyar, da kuma Georgina, wa ce ta haifa masa ƴaƴa biyu, za su samu izinin zaman ne duba da cewa ya na ɗaya daga cikin ƴan wasan da s**a fi kasuwa a duniya.

Rahoton ya ci gaba da ambato wasu lauyoyin Saudiyya biyu, wadanda ke hasashen hukumomi ba za su tsoma baki a kan lamarin ba.

Wani daga cikin lauyoyin ya ce: “Ko da yake har yanzu dokokin sun haramta zaman dadiro a Saudiyya, amma hukumomi sun fara kau da kai kuma ba za su hukunta kowa ba.

"Hakika, ana amfani da waɗannan dokokin ne lokacin da aka samu matsala ko kuma wani laifi."

Lauya na biyu ya kara da cewa: "Kawo yanzu, hukumomin Saudiyya ba su tsoma baki a cikin wannan al'amari ba (wanda ya shafi yan kasashen waje), amma doka ta ci gaba da haramta zaman dadiro a ƙasar," in ji shi.

2023: Zan ɗora a kan nasarorin Buhari -- TinubuDan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar APC, Ahmed Tinubu, ya ce zai do...
15/11/2022

2023: Zan ɗora a kan nasarorin Buhari -- Tinubu

Dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar APC, Ahmed Tinubu, ya ce zai dora kan nasarorin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu a cikin shekaru bakwai da s**a gabata.

Tinubu ya bayyana haka ne a yau Talata a Jos a wurin ƙaddamar da yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC na 2023.

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC ya bayyana cewa Buhari ya taka rawar gani a fannin samar da ababen more rayuwa tare da kafa ginshikin bunkasa noma da sauran fannoni.

“Ba mu da kwanciyar hankali, sai mu ka koma ga Janar Muhammadu Buhari mai ritaya, ya kuma fara farfadowa da kwato Najeriya.

“Ya fara ne da lalata tutocin ƴan ta’adda abisa tsari, dabara da kuma hikima, kuma a yau babu wata tuta a kananan hukumominmu a Nijeriya.

“Najeriya ta fara nutsewa amma sai Buhari ya tsamo mu ya kuma ce Najeriya ba za ta nutse ba a zamaninsa da kuma lokacin APC,” inji shi.

Ya bayyana cewa Buhari ne ya jagoranci gudanar da zaben fidda-gwani na gaskiya da inganci wanda ya samar da shi a matsayin mai rike da tuta.

Yadda tawagar kungiyar kasar Senegal tayi shigar kayan al'ada ta sauka a kasar Qatar domin fara shirye-shiryen Buga gasa...
15/11/2022

Yadda tawagar kungiyar kasar Senegal tayi shigar kayan al'ada ta sauka a kasar Qatar domin fara shirye-shiryen Buga gasar cin kofin Duniya 2022.

[Fagen Wasanni]

Rashin Halartar Taron “Arewa Joint Forum” da Kwankwaso Yayi Shine Abu Mai Kyau.Daga: Ya’u Sule TariwaA taƙaice, an ƙirƙi...
16/10/2022

Rashin Halartar Taron “Arewa Joint Forum” da Kwankwaso Yayi Shine Abu Mai Kyau.

Daga: Ya’u Sule Tariwa

A taƙaice, an ƙirƙiri gamayyar ƙungiyoyin Arewa (Arewa Joint Forum) ne domin haɗa-kan al’ummar Arewa da kuma ƙoƙarin kawo cigaba Arewa ta fuskar ilimin zamani, tsaro, lafiya, noma, da duk wani abu da zai ɗaukaka darajar yankinmu na Arewa. Waɗanda s**a bayarda gudunmawa tare da assasa wannan ƙungiya sune, Sir Ahmadu Bello Sardauna, Sir Abubakar Tafawa Balewa, Malam Aminu Kano, Alhaji Kashin Ibrahim da sauransu.

Kamar yadda na bayyana da farko babban muƙasudin samuwar wannan ƙungiya shine nemawa Arewa mafuta. Sai ga shi kuma muna tsari na siyasa (democracy). Wanda ta hanyar zaɓe ne kawai mutane za su fitar da shugaban da zai jagorance su a matakin ƙasa da sauran matakai daban-daban.

Abin takaici, wannan ƙungiya ta “Arewa Joint Forum” ta fara sauya salo maimakon ta ɗora bisa kan layin da magaban baya s**a kafa ta. Misali, Atiku da Kwankwaso suna neman takar shugabancin Nigeria, yayinda babban alhakin wannnan ƙungiya shine ta haɗa-kan Arewa ta hanyar zaɓo zaƙaƙuri a loƙacin zaɓe wanda zai kawo cigaba a Arewa dama Nigeria baki dɗaya.

A wannan karon sun nuna rashin adalci da rashin kishin Arewa. Domin, mun samu bayanai ta ɓangarori daban-daban cewa Atiku za su goyawa baya. Ni kuma a lissafi na, duk mutumin da yake kishin Arewa, cigaban Arewa da al’ummar Arewa bisa irin halin da s**a shiga, ba zai bar Kwankwaso ya ɗauki Atiku ba. Saboda Kwankwaso shine na talakawa, a koda yaushe yana kusa da talakawa, kuma yana da “vast experience” akan halin da talakawa musamman na Arewa s**a shiga.

Wannan shine dalilin da ya sanya Kwankwaso ya bayyana cewa ba zai halarci taron ba, k**ar yadda mai magana da yawunsa Hon. Abdulmumin Jibril ya bayyana. Akwai dalilai masu yawa, amma ya k**ata mutane su fahimci cewa rashin zuwan Kwankwaso, yana da nasaba da yunƙurin da wannan ƙungiya take wajen raina wayon ƴan-Arewa ta hanyar goyon bayan Atiku, wanda bai damu da damuwar talakawan Arewa ba.

Kwankwaso shine cikakken masoyin Arewa da yan Arewa. Domin ƙafa da ƙafa jaye Ogun loƙacin rikicin Ile-ife, ya nuna soyayya ga ƴan Arewa ta hanyar nemo musu ƴan-ci tare da basu tallafi. Yaje manyan kasuwanni biyu a Jihar Legas, Mile-12 da Alabarago, ya karɓo ma ƴan Arewa masu neman abinci a wuraren yan-ci. Me Atiku ya taɓa yi mak**ancin wannan?

Don haka Kwankwaso shine masoyinmu, kuma na tabbata yana kishinmu. Al’ummar Arewa sun haska, sun kuma fahimci alkhairin da yake tattare da Alhaji Rabiu Musa Kwankwaso, don haka babu wata ƙungiya da zata raina musu hankali akan cewa su zaɓi Atiku. Ƴan Arewa sun waye. Kuma rashin zuwan Kwankwaso taron ba zai hana al’ummar Arewa bashi miliyoyin ƙuri’u a ranar zaɓe ba. Insha Allah.

16|10|2022

Maza Sun Fi Mata Yaudara Hasalima Tushen Yaudara Daga Maza NeDaga Ramaz AzareZuciyar mace k**ar kitse take wanda maza ke...
16/10/2022

Maza Sun Fi Mata Yaudara Hasalima Tushen Yaudara Daga Maza Ne

Daga Ramaz Azare

Zuciyar mace k**ar kitse take wanda maza ke amfani da zafafan kalamai su narkar da ita har su sauya mata RA'AYI.

Duk wata shahararriyar yaudara da mace tayi ta yaudari namiji, a siyasa, kasuwanci, ko zaman aure in ka bi diddigi zaka samu namiji Dan Uwansa ne bindiga da harsashin da shirya wannan yaudarar amma yayi amfani da mace a matsayin kunamar da ta tashi harbin yaudarar

Misali Boka da Malaman tsubbu a gidan aure suke gina mata su ingiza su akan kowacce yaudara

Hatta shirin film da aka fi zagin mata namiji ne yake rubuta salon kowacce yaudara ya bada umarni a mace ya kwatanta mata yadda zata yaudari Maza

A bayan can Mata ne ke yiwa Mata dinki shiyasa ake yin burma-burman kayan sawa a rufe a suturta jiki amma Oga namiji sai ya ce baku iya ba kawo ku ga yadda ake fidda kugu da hantsar mama da illahirin surar kirji don a yaudari maza

Anan social media ma dai Maza ne ke amfani da sunan Mata su yaudari maza

Duk wata rawa da ka ga mace ta na yi tana yaudarar maza da surarta zaka samu namiji ne yake mata kida

Maza suna amfani da tarihin da yake cewa Shaidan ma ya sarawa yaudarar mata saboda yadda wata budurwa ta yaudare shi tasa ya wanke allon makircin da ya rubuta na mata akan zata ba shi sabon markici na zamani kuma ta gudu ta bar shi

Kafin faruwar haka kuma Shaidan din ne dai mayaudari na farko daya yaudari Annabi Adam (A.S) da Nana Hauwa agidan Aljanna har aka fiddo da su duniya

Inda zaka samu Ango da Amarya dari ka dora musu bandiga kace daga farkon balagarsu kawo aurensu kowanne Ango ya fadi adadin yan matan da ya taba yi su ma Amare su fadi adadin Samarin da s**a taba yi na tabba mazan da za'a kashe su za su fi rinjaye

Kamammiyar mace da ta bariki duk wadda tace Kai take so da gaske to bata sake kula wani amma namiji har a satin daurin aurensa ma zai iya yin budurwa

Namiji zai durkusa ya roke ki, ya rantse miki yace ya daina, wani har yayi kuka don ki yarda da shi amma fa duk acikin salon lale katin yaudara ne

Mace idan ta Kai shekara 60 da doriya ta sallamawa kowacce yaudara amma namiji Mai shakaru 70 yana iya yaudarar 'yar shekaru 5 yayi lalata da ita (fyade).

Sir Alex Ferguson ya ba Cristiano Ronaldo kyautarsa ​​saboda ya ci kwallonsa ta 700 a kulab a Manchester United.
16/10/2022

Sir Alex Ferguson ya ba Cristiano Ronaldo kyautarsa ​​saboda ya ci kwallonsa ta 700 a kulab a Manchester United.

16/10/2022

Jerin 'yan wasan farko XI na Real Madrid da zasu fafata da Barcelona a El-Clasico....3:15pm

Real Madrid XI: Lunin, Carvajal, Militao, Alaba, Mendy, Tchouameni, Kroos, Modric, Valverde, Vinicius, Benzema.

16/10/2022

Jerin 'yan wasan farko XI na FC Barcelona da zasu fafata da Real Madrid a El-Clasico....@3:15pm

Barcelona XI:
Ter Stegen; Sergi Roberto, Koundé, Garcia, Balde; Busquets, Frenkie de Jong, Pedri; Dembélé, Lewandowski, Raphinha.

Komai yayi daidai an tabbatar da Ousmane Dembélé bashi da rauni. - [][Daga Fagen Wasanni]
29/09/2022

Komai yayi daidai an tabbatar da Ousmane Dembélé bashi da rauni. - []

[Daga Fagen Wasanni]

Wannan   da Za ku gani a gaban Arrow k**ar   dake cikin wannan Hoto, ba Kwayar Sugar bane,Shine Duniyar da muke ciki a y...
29/09/2022

Wannan da Za ku gani a gaban Arrow k**ar dake cikin wannan Hoto, ba Kwayar Sugar bane,
Shine Duniyar da muke ciki a yanzu haka, wato duniyar Daga Nisan tafiyar Kilometers , a Sararin Samaniya.

Daga Adamu Ya'u Dan America

Na'urar Binciken Sararin Samaniya mai suna 🛰 na Hukumar dake Kasar America ita ce ta Dauki wannan hoton a ranar (14/02/1990) yanzu shekaru 31 har da watanni 7 kenan.

Daga lokacin da aka Harba Na'urar Voyager 1 🛰 zuwa yanzu shekaru 44 da kwanaki 21 kuma har yanzu tana cigaba da Bincike a sararin samaniya.

A lokacin da wannan na'urar ta dauki Hoton duniyar mu ta Earth a 1990 lokacin na'urar tsakanin ta da duniyar mu ta Earth kilometers Biliyon 6,

Yanzu haka na'urar Voyager 1 🛰 yana wani waje da ake kira a Sararin Samaniya mai nisan tafiyar Kilometers Biliyon 19 da digo 111 tsakanin sa da duniyar mu ta Earth, Hakan na nuna cewa wannan na'urar ta fita daga cikin duniyoyin dake cikin .

Misalin da ace akwai Hanyan da mutun zai je da , sannan a Kure gudun Mota ayi tafiyar Kilometers (220 PER HOUR) babu tsayawa, sai an shafe shekaru dubu 3,235, da watanni kusan 8 Kafin ya isa inda wannan na'urar Voyager 1 🛰 ta dauki Wannan Hoton.

Amma ita wannan na'urar Voyager 1 🛰 ta isa wajen a cikin Shekaru 13, bayan an Harba ta daga nan duniyar a 1977.

Thanks from

Hotona daga taron sa hannun yan takarar shugaban kasa a zaben 2023 kan zaman lafiya
29/09/2022

Hotona daga taron sa hannun yan takarar shugaban kasa a zaben 2023 kan zaman lafiya

Tinubu bai halarci taron rattafa hannu na "Yan takaran Shugaban kasa Kan Zaman lafiya baTinubu Bai Kasance ba Yayin Da ‘...
29/09/2022

Tinubu bai halarci taron rattafa hannu na "Yan takaran Shugaban kasa Kan Zaman lafiya ba

Tinubu Bai Kasance ba Yayin Da ‘Yan Takarar Shugaban Kasa ke Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Zaman Lafiya.

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress, APC Bola Tinubu, bai halarci taron ba a ranar Alhamis yayin da ‘yan takarar shugaban kasa na sauran jam’iyyun siyasa s**a hallara a jiki don rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da aka saba a yanzu.

Sai dai abokin takarar Tinubu, Kashim Shettima, ya halarci rattaba hannun, Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP, Peter Obi na jam’iyyar Labour Party (LP) Rabiu Kwankwaso na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) da sauransu.

Arsenal ta tabbatar da cewa an yi wa Emile Smith Rowe tiyata a makwancinsa kuma ana sa ran zai yi jinyar akalla watanni ...
29/09/2022

Arsenal ta tabbatar da cewa an yi wa Emile Smith Rowe tiyata a makwancinsa kuma ana sa ran zai yi jinyar akalla watanni biyu. [Daga Fagen Wasanni]

Jumullar tawagogin kungiyoyin Real Madrid C.F. a kakar bana:🌟 Kungiyar kwallon kafa ta Maza: Wasanni 9, Nasara 9.🌟 Kungi...
29/09/2022

Jumullar tawagogin kungiyoyin Real Madrid C.F. a kakar bana:

🌟 Kungiyar kwallon kafa ta Maza: Wasanni 9, Nasara 9.
🌟 Kungiyar kwallon kafa ta Mata: Wasanni 5, Nasara 5.
🌟 Kungiyar kwallon kwando: Wasanni 3, Nasara 3.

[Daga Fagen Wasanni]

Binciken Kimiyya samuwar tsatson jiniin Hausawa shekaru dubu ɗari da arba'in da su  wuce~Fassarar Google Translate.BAYAN...
29/09/2022

Binciken Kimiyya samuwar tsatson jiniin Hausawa shekaru dubu ɗari da arba'in da su wuce~Fassarar Google Translate.
BAYANIN SANIN GASKIYA GAME DA HAUSA

Y chromosomal haplogroups su ne gwajin DNA waɗanda ke wucewa tare da Y chromosomes don haka yana yaɗuwa ne daga uba namiji zuwa ɗa ...

Ana iya amfani da shi don gano asalin zuriyar wani a kan dubban ƙabilu dake faɗin duniya ...

Hausawa dai na daya daga cikin manyan kabilun Najeriya da yammacin Afirka baki daya, sun fi yawa a Arewacin Najeriya, Jamhuriyar Nijar, Arewacin Benin, wasu sassan Chadi Sudan da Kamaru.

Hausawa suna magana da yaren Afroasiatic na reshen Chadic wanda babban dangi ne na harsuna ciki har da Semitic (Ibrananci, Larabci, Amharic) Berber (Amazigh) Ancient Egypt/Coptic, Cush*tic (Somali and Oromo)

Harshen Hausa shi ne yaren da ya fi yaɗuwa a yammacin Afirka, yana da matsayin Swahili na zamantakewa a gabashin Afirka

Wani abu mai ban sha'awa game da Hausawa shine cewa sama da kashi 40 cikin 100 na mazajen Hausawa suna ɗauke da Y chromosomal haplogroup R1b, R1b shine babban Y chromosomal haplogroup a Yammacin Turai wanda ya kai mafi girma a Ireland (95%)
Hakanan R1b yana faruwa a cikin manyan mitoci a Kurdistan da Kudancin Anatoliya da Kazakhstan ta Yamma da kuma yankunan ƙasar Egypt misra.. masu bincike sun tabbatar da jiniin wannan dangi daya yaɗu a Duniya ya samo asali ne tun fiye da shekaru dubu ɗari da arba'in ko dubu saba'in da biyar dasu ka gabata k**ar yadda zaku gani a ɗaya daga cikin photunan da muka saka a cikin post dake ƙasa 👇

Kusan kashi 23% na ɗauke da E1b1a/E3a babban haplogroup daga kabilun dake Yammacin Afirka inda binciken ya tabbatar da kaso fiye da arba'in na Hausawa da akai gwajin kansu suna dauke da jinin wanda ya ya tabbatar da sunfito zuri'a ɗaya ne da mutanen Kazasthan, Ireland da kuma wasu sassan kasar Misira.

LITTLE KNOWN FACTS ABOUT THE HAUSA

Y chromosomal haplogroups are DNA fragments that are passed along Y chromosomes thus can only be passed from father to son...
It can be used to geneticaly trace someone's patrilineal line of descent over thousands of generations...

The Hausas are one of the largest ethnic groups in Nigeria and in West Africa as a whole, they are predominant in Northern Nigeria, Niger Republic, Northern Benin, parts of Chad Sudan and Cameroon.

The Hausa speak an Afroasiatic language of the Chadic branch which is a broad family of languages including Semitic(Hebrew, Arabic, Amharic) Berber(Amazigh) Ancient Egyptian/Coptic, Cush*tic (Somali and Oromo)

The Hausa language is the most widespread language in West Africa, it has the social status of Swahili in East Africa

One intriguing fact about the Hausa is that over 40% of Hausa males carry Y chromosomal haplogroup R1b, R1b is the dominant Y chromosomal haplogroup in Western Europe reaching the highest frequencies in Ireland(95%)
R1b also occurs in high frequencies in Kurdistan and Southern Anatolia and Western Kazakhstan. There are still many theories about how R1b originated and spread.
About 23% carry E1b1a/E3a the dominant haplogroup in West Africa.

Possible time of origin : 70,000-75,000 or already 141,000

Sam Gwamnatin Buhari Ba Ta Muntunta Ilimi, Cewar Muhammadu Sanusi IISarkin Kano na 14, Muhamadu Sunusi II, ya yi kakkaus...
29/09/2022

Sam Gwamnatin Buhari Ba Ta Muntunta Ilimi, Cewar Muhammadu Sanusi II

Sarkin Kano na 14, Muhamadu Sunusi II, ya yi kakkausar s**a ga gwamnati mai ci ta jam’iyyar APC da cewa sam ba ta martaba ilimi ba.

Sanusi ya yi wannan s**ar ce a yayin jawabinsa a taron Majalisar Dinkin Duniya kan batun ilimi wanda aka yi a birnin New York na Amurka a makon da ya gabata.

Taron na kwanaki uku ya mayar da hankali ne kan neman mafita domin sauya ilimi daga tushe domin ci gaba.

Sanusi, wanda kuma shi ne Kalifan darikar Tijjaniyya a Najeriya ya ce gwamnatin APC karkashin Shugaban Kasa Muhammdu Buhari ba ta martaba ilimin ne ganin yadda ta ke tafiyar da batun yajin aikin malaman jami’o’i, wanda hakan ya sa aka rufe jami’oi tun watan Fabrairu.

“Abin da ke faruwa shi ne an yi rashin sa’ar samun wadanda ba sa martaba ilimi da kuma ba shi muhimmanci a madafun iko, wanda hakan ya sa ba a ganin girman [ilimi da kuma] malamai”.

“Yawancin malaman nan na da zabin aikin yi, amma s**a zabi su ilimantar da ‘ya’yanmmu saboda su taimaka wa al’umma,” inji Kalifan.

Sanusi ya kuma koka da yadda ake tafiyar da tsarin ilimi da albashi da kuma walwalar malamai baki daya, yana mai cewa abin takaici ne da ke bukatar gyara.

MÚHAWARA: Shìn A Nàgeria Mazan Waccé Jìha Ne Sukafí San Fararen Mata Wanda Hakan Ya Jefa Mata Da Yawa Harkar Shafe - Sha...
29/09/2022

MÚHAWARA: Shìn A Nàgeria Mazan Waccé Jìha Ne Sukafí San Fararen Mata Wanda Hakan Ya Jefa Mata Da Yawa Harkar Shafe - Shafe Domin Ƙara Farí ?

Hanyàr Pandógari Zúwa Alàwa Daké Kàramar Húkúmar Shíróró A Jìhar Néja Ta DamalmaléKu dubi yadda al'umma ke fama da hanya...
28/09/2022

Hanyàr Pandógari Zúwa Alàwa Daké Kàramar Húkúmar Shíróró A Jìhar Néja Ta Damalmalé

Ku dubi yadda al'umma ke fama da hanyar Pandogari zuwa Alawa har Bassa da ma sauran yankunan dake yankin.

DAGA Nuruddeen Isyaku Daza

Gorin rashin haihuwa ne ya sanya na saci jariri, in ji ɓarauniyar da ta yi sata a asibitin BauchiJami’an tsaro sun k**a ...
28/09/2022

Gorin rashin haihuwa ne ya sanya na saci jariri, in ji ɓarauniyar da ta yi sata a asibitin Bauchi

Jami’an tsaro sun k**a wata mata da ake zargin ta saci jariri sabuwar haihuwa, Ibrahim Khalid a asibitin koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi.

Jaridar Punch ta ce jaririn wanda ɗan tagwaye ne, an sace shi ne ranar Talatar makon jiya a dakin asibiti, kafin a gano tare da mayar da shi hannun mahafiyarsa.

Ana zargin wacce ta saci jaririn da yin shiga k**ar ma’aikaciyar jinya a asibitin kuma ta lallaba ta zari yaron ba tare da an k**a ta ba.

Bayanai sun ce wadda ake zargin ta sace jaririn ne saboda damuwar da ta shiga sak**akon yawan gorin da dangin miji ke yi mata na rashin haihuwa.

Wadda zargin ta kai jaririn kauyensu na Dull a cikin karamar hukumar Tafawa Balewa tana cewa dan da ta haifa ne.

Da a ke tuhumar ta, sai matar ta kada baki ta ce ta na shan horon rashin haihuwa ne shi ya sanya ta aikata wannan aika-aika.

Address

No 98
Kaduna

Telephone

+2348106949003

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Jamhuriyya posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Jamhuriyya:

Videos

Share

Nearby media companies


Other Media/News Companies in Kaduna

Show All

You may also like