Hausa Print

Hausa Print Gaskiya da gaskiya a fannin labaran gida da na ƙasashen waje cikin harshen Hausa zalla.

04/04/2023

Kotu ta umarci a yanka wani Zakara a Kano

Kotun Majistiri da ke gidan Murtala a Kano ta umarci wani mutum Isyaku Shu'aibu da ke unguwar Ja'en ya yanka Zakaransa.

Maƙocinsa Malam Yusuf Muhammad Ja'en ne ya shigar da ƙara Kotun kan cewa Zakaran yana shiga haƙƙinsa ta hanyar hana shi barci da yawan Cara.

Amma koda aka karantowa wanda ake ƙara ya ce, gaskiya ne Zakaran na yawan yin Cara kuma zai yanka shi ne a bikin "Good Friday" don haka ya roƙi Kotun da ta sahale masa zuwa ranar.

Mai shari'a Halima Wali ta amince inda ta umarci ya killace Zakaran kuma ya yanka shi a Jumu'a mai zuwa wato ranar "Good Friday" ɗin.

04/04/2023

Mu na farawa da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai

Bismillahir Rahmanir Raheem......Daga wannan kafa ta sada zumunta, wannan Jarida mai suna Hausa Print za ta dinga kawo m...
23/02/2020

Bismillahir Rahmanir Raheem......

Daga wannan kafa ta sada zumunta, wannan Jarida mai suna Hausa Print za ta dinga kawo mu ku labarai iri daban daban, na cikin Gida da Ƙasashen waje tare kuma da nishaɗantar da ku awa 24.

Mun gode👍

23/02/2020

Address

Kinshasa Road Ungowan Rimi Kaduna
Kaduna

Telephone

+2348098592323

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Hausa Print posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category


Other Publishers in Kaduna

Show All