Daga Halayen Manzon Allah -SAW

Daga Halayen Manzon Allah -SAW Wannan wani kafa ne da zai riqa kawo maku ingantattun labarai daga kyawawan halayen Manzon Allah SAW

23/03/2024

Tafsirin Dr. Jameel Muhammad Sadis Zaria HafizahullAh

14/10/2023
09/04/2023

Ya ku yan uwa ku aikata Alkhairi da abinda Allah ya danka a hannayen ku kamin lokacin cizon yatsa😭😭😭

09/04/2023

Thanks for being top engagers and making it onto our weekly engagement list! 🎉 Faruq Umar Alabani, Hauwa Musa, Ummu Tasnim, Aisha Alhasan, Salaha Baba, Abdullahi Hanafi, Abdulrahaman Shehu, Ummulkhairi Isah, Ali Yunusa, Hauwa San. To all our followers, we sincerely appreciate your engagement and we wish you will do more as we endeavor to feed you with authentic narrations from the prophetic attributes. JazaakumullAhu Khairan ❤️❤️❤️.

Tunatarwa Ga Masu Ruwa Da Tsaki A Lamarin Al’umma. BismillAhUwar Muminai Aisha RA ta rawaito cewa ta ji Manzon Allah SAW...
09/04/2023

Tunatarwa Ga Masu Ruwa Da Tsaki A Lamarin Al’umma.

BismillAh
Uwar Muminai Aisha RA ta rawaito cewa ta ji Manzon Allah SAW yana cewa;
”Ya Allah duk wanda aka bashi wani nauyi na jibintar ko tafiyar da Al’amuran mutane daga Al’umma ta sai ya tsananta ya kuntata masu, yaa Allah ka kuntata masa! Kuma duk wanda aka bashi ragamar shugabanci a Al’umma ta sai ya tausaya ya tausasa masu, yaa Allah ka tausaya masa”.

Sahihu Muslim 1828

05/04/2023

In kunne ya ji…

Daga Halayen Manzon Allah SAW (002)Bismillah. 1. An tambayi uwar muminai Aish RA yaya halin Manzon Allah SAW yake? sai t...
05/04/2023

Daga Halayen Manzon Allah SAW (002)

Bismillah.

1. An tambayi uwar muminai Aish RA yaya halin Manzon Allah SAW yake? sai tace;
“Halin sa ya kasance Alqur’ani”.
Abin da take nufi shine ya kasance duk abin da Alqu’ani yayi umarni dashi sune dabi’un sa.
Sahihul Jami’ 4811

2. A suratul ahzaab Aya ta 21 Allah madaukakin sarki yace;
“Hakika abin koyi mai kyau ya kasance cikin rayuwar Manzon Allah SAW ga duk wanda yake fatan haduwar sa da Allah da tsayuwa ranar kiyama tayi kyau kuma ya ambaci Allah da yawa”.

3. Usman Bin Affan RA ya rawaito Manzon Allah SAW yace;
“Mafi Alkhairi daga cikin ku shine wanda ya koyi Alqur’ani kuma yake karantar dashi”.
Sahihul Bukhari 5027

Ya Allah kasa Alqur’ani ya cece mu.

05/04/2023
05/04/2023

Allah ya kara yarda da Sahabban Manzon Allah SAW.

Taswirar ginin masallacin Manzon Allah SAW a farkon gina shi da yanda yake a yanzu. Allah ya azurta yan uwa da zuwa wann...
04/04/2023

Taswirar ginin masallacin Manzon Allah SAW a farkon gina shi da yanda yake a yanzu.

Allah ya azurta yan uwa da zuwa wannan wuri mai Albarka.

Daga Halayen Manzon Allah SAW (001)Bismillah!1. A Suratu Ali Imran aya ta 59 Allah madaukakin sarki yake yabon halin Man...
03/04/2023

Daga Halayen Manzon Allah SAW (001)

Bismillah!

1. A Suratu Ali Imran aya ta 59 Allah madaukakin sarki yake yabon halin Manzon Allah SAW da cewa
”Domin rahmar Allah gareka ya sanya ka zamto mai taushin mu’amala ga sahabbai, da ka kasance mai kaushin dabi’a, mai zafin hali da duk sun watse daga gareka”.

2. A Sahihul Bukhari 2038, Anas dan Malik, wanda yake hadimin Manzon Allah SAW ne yake cewa
“Na hidimtawa Manzon Allah SAW tsawon shekaru goma, amma bai taba ce dani tir akan wani abu da nayi ba, bai taba ce dani me yasa kayi kaza ko me yasa baka yi kaza ba?”.

3. A Sahihul Bukhari 4971, Anas dan Malik ya rawaito cewa
“Manzon Allah SAW ya kasance yakan zo inda muke domin ya duba mu. Anas yace ni kuma ina da wani kani karami da ake yiwa alkunya da Abu Umair, shi kuma yana da wani karamin tsuntsu (kanari) da yake wasa dashi. Kwatsam sai tsuntsun nan ya mutu! Yaro ya shiga damuwa har ya dena fita. Wata rana Manzon Allah SAW bai ganshi ba sai ya tambaya ina wannan yaro, sai aka ce dashi ai ya dena fita domin tsuntsun shi ya mutu😭. Manzon Allah SAW yace da sahabbai ku tashi muje mu yiwa yaron nan ta’aziyyar tsuntsun shi. Suna shiga s**a same shi ya bata rai, sai Manzon Allah SAW yace dashi ya Abu Umair me ya faru da Nughair?” Manzon Allah SAW ya kira tsuntsun da nughair ne saboda yayi masa raha ya rage masa radadin abin dake damun sa.

Ya ku yan uwa, wannan fa shine Annabin mu. Tambayar ita ce;
To mu a ina muka samo halayen da muke dasu a yau?

Wassalaamu Alaykum.

26/10/2022

Haqiqa manzo yazo muku daga cikin ku. Duk abin da zai wahalar daku yana daga masa hankali, mai tsananin kwadayin rahama gare ku. Mai kuma tausayi ne da jin qai ga muminai.

Taubah-128

Address

Kaduna
08060343738

Telephone

+2348060343738

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Daga Halayen Manzon Allah -SAW posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Daga Halayen Manzon Allah -SAW:

Videos

Share

Category