22/07/2022
Assalamu Alaikum barkanmu da asubahin Juma'atu babbar rana, ashirin da uku ga watan Zulhaj, shekarar 1443 bayan hijirar cik**akin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S. A. W. Daidai da ashirin da biyu ga watan Yuli, shekarar 2022.
Da yake yau Juma'a an jima da safe, sai a nemi jaridar Leadership Hausa da za ta fita an jima domin duba shafina. Ko a nemeta a dandalinta na Intanet. Har ila yau a dandalin na Intanet, za a iya lalubar DCL Hausa, da Kainuwa, da AREWA Daily-Post, da Taskira, da Muryar 'Yanci da sauran jaridu na Intanet da ke wallafa rubutuna kullum da asubah don karanta rubutun nawa. Akwai kuma dandali daban-daban na wasaf da fesbuk da akan tura rubutun ko shiyarin a kullum.
1. Gwamnatin Tarayya tana duba yiwuwar hana sana'ar acaba da babur, da aikace-aikace na haƙar ma'adina a faɗin ƙasar nan saboda matsalar tsaro.
2. Fadar Shugaban Ƙasa ta ce babu gaskiya a labarin da ake yaɗawa cewa Shugaban Ƙasa Buhari ya ba ministan ilimi Adamu Adamu mako biyu don sasantawa da malaman jami'a da ke yajin aiki.
3. Shugaban Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa Ayuba Wabba, ya mayar wa da Lai Mohammed ministan labaru, martanin zanga-zangar da s**a shirya yi ranar Talata da Laraba tana nan daram ba fashi, ba gudu ba ja da baya. Ƙungiyar ɗaliban jami'a ma ta yi kira ga ɗaliban su fito don rufa wa ƙungiyar ƙwadago baya a ranakun. Ma'aikatan sufurin jiragen sama, da na bankuna da sauran cibiyoyin kuɗi duk sun ce za su mara wa NLC baya. Shi dai Lai Mohammed cewa ya yi zanga-zangar da ƙungiyar ƙwadago ta shirya don tilasta wa gwamnati sasantawa da malaman jami'a haramtacciya ce.
4. Kamfanin Dakon Wutar Lantarki TCN, ya ce an gyara wutar Nijeriya da ta yi targaɗe shekaranjiya.
5. Hukumar shirya jarabawar samun shiga manyan makarantu JAMB, ta fitar da yawan makin da take buƙata mutum ya ci a jarabawarta ta shekarar 2022 don samun shiga manyan makarantun. Jami'a maki 140, foliteknik 120, kwalejojin ilimi 100.
6. Jam'iyyar APC ta ce shugabannin c
Send a message to learn more