![Arewa Ba Mu Shirya Wa Goben Mu Ba, Duk Abinda Zai Amfane Mu Ba Shi Muke Sawa A Gaba BaDaga Nafi'u Dawaki Bari ku ji....F...](https://img3.medioq.com/060/970/621699760609704.jpg)
03/02/2025
Arewa Ba Mu Shirya Wa Goben Mu Ba, Duk Abinda Zai Amfane Mu Ba Shi Muke Sawa A Gaba Ba
Daga Nafi'u Dawaki
Bari ku ji....
Farfesa Usman Yusuf, ya gina rayuwa mai matuƙar kyau cikin daraja da kare mutuncin kai, ya yi rayuwar karatu da aiki a sassa mai yawa na duniya, daga baya an nemi ya dawo gida domin bada gunmawa, ya dawo ya tsaya tsayin daka domin kare mutuncin al'ummar Arewa. Wannan ya ja masa baƙin jini a wajen masu mulki, ƙarshe s**a k**a shi s**a ɗaure bisa zalunci.
A gefe kuma 'yan TikTok da ba su tsinanawa rayuwarku komai ba ballantana rayuwar wasunsu, saboda kawai sun gama shiriritarsu ƙarshe sun dawo sunyi aure, maganar sai yawo take, ko ina ka duba sai tattaunawa ake k**ar wani abu mai muhimmanci.
Shin da wannan shirmen, rashin wayewa da rashin sanin mutuncin kai muke tunanin samun nasara?
Su fa yanzu su Sowore IG na 'yan sanda s**a sako a gaba kuma suke burin sai sun kai shi ƙasa, amma mu an bar mu da labaran su G-fresh, Murja Kunya da sauran shiririya. Arewa kenan!
Allah yasa mu gane.