12/01/2024
Shari'o'in zaɓe da Kotun Ƙolin Najeriya za ta gama da su a Juma'ar nan
Alƙalan Kotun Ƙolin Najeriya a Juma'ar nan suna da jan aiki a gabansu, saboda hukunce-hukunce da dama da za su yanke, na shari'o'in zaɓukan gwamna da aka ɗaukaka daga faɗin ƙasar.
Wata majiyar Kotun Ƙoli ta tabbatarwa da BBC cewa shari'o'in zaɓe bakwai, ake sa ran alƙalan za su yanke hukuncinsu.
Hukunce-hukuncen na da matuƙar muhimmanci ga jihohin da abin ya shafa da kuma siyasar Najeriya.
Matakin kuma shi ne na ƙarshe ga fafutukar mulki ta hanyar shari'a. tsakanin 'yan siyasa da jam'iyyunsu, tun bayan zaɓukan 2023.
Hukunce-hukuncen shari'o'in zaɓen gwamna da ƙananan kotuna s**a yanke a baya, ba su iya kawo ƙarshen ja-in-jar da ake ta bugawa ba.
Sai dai yanzu, an zo magaryar tiƙewa. Kotun da ake kira 'Daga Ke Sai Allah Ya Isa', za ta yi fashin baƙin dokoki, sannan ta zartar hukunci.
Ga jerin shari'o'in da kotun za ta yanke hukuncinsu ranar Juma'a:
Gawuna da Abba
Ɗaya daga cikin shari'o'in zaɓen gwamna mafi zafi da kotun ƙolin Najeriya za ta yanke hukunci, ita ce ta Gwamna Abba Kabir Yusuf da Nasiru Yusuf Gawuna.
Shi dai Abba Kabir yana ƙalubalantar soke nasarar zaɓensa ne da ƙananan kotuna s**a yi a baya.
Tun da farko, kotun zaɓen gwamnan Kano a watan Satumban 2023 ce ta soke ƙuri'a 165,633 wadda in ji ta, aka yi wa ɗan takarar na jam'iyyar NNPP aringizo, bayan hukumar zaɓe a watan Maris, ta ce ya samu ƙuri'a 1,019, 602.
Kuma ta umarci hukumar Inec ta ƙwace shaidar cin zaɓen da ta bai wa Abba, sannan ta bai wa ɗan takarar jam'iyyar APC, Nasir Yusuf Gawuna shaidar zama zaɓaɓɓen gwamna.
Gwamna Abba dai bai gamsu da hukuncin ba, don haka ya wuce zuwa kotun ɗaukaka ƙara.
Sai dai, ita ma kotun ɗaukaka ƙarar ta bai wa jam'iyyar APC nasara bisa hujjar cewa Abba ba ɗan jam'iyyar NNPP ba ne lokacin da aka tsayar da shi takara, don haka ta nemi a rantsar da ɗan takararta Nasiru Gawuna.
Nasiru Yusuf wanda ya samu adadin ƙuri'a 890,705 a watan Maris, kotuna baya sun ce shi ne ya ci halastaccen wanda ya ci zaɓen gwamnan Kano, sai dai Abba Kabir ya ce ba gaskiya ba ne
Hukuncin dai ya zo da kwan gaba-kwan baya, inda wani ɓangare ya nuna cewa Gwamna Abba ne ya samu nasara, ragowar hukuncin kuma ya bai wa APC da ɗan takararta nasara. Daga bisani, kotun ta ce abin da ya faru tuntuɓen alƙalami ne, amma hukuncinta APC ya bai wa gaskiya.
A wannan ƙara, Kotun Ƙolin ana hasashen cikin biyu, za ta yi ɗaya, ko dai ta tabbatar da hukunce-hukuncen kotuna baya, ta jaddada nasarar da s**a bai wa Nasiru Gawuna, ko kuma ta rushe matsayarsu, ta bai wa Abba Kabir Yusuf gaskiya.
Mutfwang da Goshwe
Shari'ar Caleb Mutfwang da Nentawe Goshwe daga jihar Filato, na ɗaya daga cikin shari'o'i masu zafi, da ake sa ran kotun ƙolin a Juma'ar nan, za ta yanke hukunci a kai.
Gwamna Mutfwang ya garzaya gaban kotun ne bayan kotun ɗaukaka ƙara a watan Nuwamba ta rusa zaɓensa, inda ta umarci Inec ta bai wa abokin shari'arsa shaidar cin zaɓen watan Maris.
Yana roƙon kotun ta tabbatar da hukuncin kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamna ta jihar Filato, kuma ta jingine hukuncin kotun ɗaukaka ƙara, saboda a cewarsa, masu ƙarar ba su da 'yancin ƙalubalantar yadda wata jam'iyya ta zaɓi shugabanninta na jiha.
Yayin da Nentewe Goshwe na jam'iyyar APC yake fatan kotun ƙoli za ta jaddada hukuncin kotun ɗaukaka ƙara da ya ba shi nasara.
Kowanne a cikin ɓangarorin biyu, yana bayyana ƙwarin gwiwar cewa hukuncin na Juma'a, shi zai bai wa nasara.
Matawalle da Dauda
Tamkar APC ta Bello Matawalle, Gwamna Dauda Lawal Dare ya ɗaukaka ƙara zuwa kotun ƙoli yana neman ta tabbatar da nasararsa, wadda kotun baya ta soke, har ma ta ba da umarnin a yi sabon zaɓe cikin wasu ƙananan hukumomi.
Alƙalan kotun ɗaukaka ƙarar sun ce za a gudanar da zaɓen ne a ƙananan hukumomin Birnin-Magaji Bukkuyum da kuma Maradun, saboda a watan Maris ɗin 2023, ko dai ba a yi zaɓe a wuraren ba, ko kuma an yi zaɓen amma ba a ƙidaya sakamakonsu ba.
Hukumar zaɓe dai a lokacin ta ayyana ɗan takarar babbar jam'iyyar adawa ta PDP, Dauda Lawal a matsayin wanda ya yi nasara da ƙuri'a 377, 726, inda a wani lamari mai cike da ban mamaki, ya kayar da gwamna mai ci Bello Matawalle.
Sai dai ɗan takarar na APC, Bello Matawalle wanda yanzu shi ne ƙaramin ministan tsaron Najeriya, ya zargi Inec da kassara nasarar da ya samu, saboda ta gaza haɗawa da sakamakon wasu mazaɓu.
Kotun sauraron ƙarar gwamnan Zamfara a ranar 18 ga watan Satumba ta yanke hukunci a kan shari'ar, amma ba ta ba shi gaskiya ba, a cewarta ƙarar da ya shigar gabanta, ba ta da tushe. Kuma ta tabbatar da zaɓen Gwamna Dare.
Lamarin da ya sanya Matawalle garzayawa kotun ɗaukaka ƙara, wadda ita kuma ta ba shi nasara. Sai dai Dauda Lawal Dare ya ce bai yarda ba.
Yanzu dai, ɓangarorin biyu za su zuba ido su gani, ko kotun ƙoli za ta tabbatar da hukuncin da ya ce zaɓen gwamnan Zamfara bai kammala ba, ko kuma za ta tabbatar da nasarar Dauda Lawal Dare, ko ma ɗungurungum ta fitar da wani sabon hukunci da ya saɓa da duka biyu na baya.
Bala da Saddiq
A nan ɗan takarar jam'iyyar APC a zaɓen gwamnan jihar Bauchi na 2023, Saddique Abubakar ya sake maka Gwamna Bala Mohammed na PDP, ƙara a gaban kotun ƙoli.
Tun da farko, kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamna ta jihar Bauchi da kotun ɗaukaka ƙara duk sun kori ƙararsa, suna cewa ba ta da tushe.
Saddiqu Abubakar dai yana tunƙahon cewa takardun zaɓe masu yawa da aka yi amfani da su, ba a cike su yadda ya kamata ba. Sannan ya yi zargin cewa ba a yi biyayya ga kundin dokokin zaɓe a lokacin kaɗa ƙuri'ar zaɓen gwamna a Bauchi ba.
Sai dai, kotun ɗaukaka ƙara ta ce ɗan takarar na APC ya gaza gabatar da gamsassun hujjoji da shaidu da za su tallafi zarge-zargensa.
Duk da haka, bai yi ƙasa a gwiwa ba, a Juma'ar nan Saddique Abubakar yana fatan kotun ƙoli za ta yi hujjojin da ya gabatar duban basira, kuma ta ba shi gaskiya, yayin da abokin takararsa na PDP ke fatan alƙalan kotun kamar takwarorinsu na kotunan baya, su kori wannan ƙara.
Jandor da Sanwo-Olu da GRV
Daga jihar Lagos, ɗan takarar gwamna a jam'iyyar Labour, Gbadebo Rhodes-vivour wanda a taƙaice ake kira GRV ne da takwaransa na PDP, Abdulazeez Adeniran s**a sake shigar da ƙarar Gwamna Babajide Sanwo-Olu.
Kafin sannan, kotun ɗaukaka ƙara ta yi watsi da shari'o'insu, saboda a cewarta ba su da tushe.
Sun garzaya gaban kotu ne tun da farko bayan a watan Maris, hukumar zaɓe ta ayyana cewa Gwamna Sanwo-Olu ya lashe rinjayen ƙuri'un da aka kaɗa da 762,134.
Sai dai, kotun farko da ta biyu duka sun bai wa ɗan takarar na jam'iyyar APC nasara, suna cewa ya lashe zaɓen da ya ba shi damar samun wa'adin mulki na biyu.
Suna dai kafa hujja da shigar da takardun jabu, kuma suna iƙirarin cewa Sanwo-Olu da mataimakinsa Obafemi Hamzat ba su cancanci tsayawa takara ba.
Nwifuru da Odii
Ebonyi na cikin jihohin da ake lissafawa a jerin waɗanda hukuncin ƙarshe na shari'ar zaɓen gwamnansu mai yiwuwa zai fito daga kotun ƙolin Najeriya a yau.
Ranar Litinin ɗin da ta wuce ne, kotun ta kammala sauraron bahasin duka ɓangaren da ke cikin shari'ar wadda ɗan takarar jam'iyyar PDP a zaɓen gwamnan jihar da ya wuce, Chukwuma Ifeanyi Odii ya ɗaukaka.
Alƙalan kotun ɗaukaka ƙara sun yanke hukunci a watan Nuwamban bara PDP da ɗan takararta ba su da hujja bisa doka ta yin katsalandan cikin harkar jam'iyyar APC wajen fitar da gwanin da zai yi mata takara.
Onor da Otu
Daga jihar Cross River ma, ɗan takarar jam'iyyar PDP, Sanata Sandy Onor ne ya ɗaukaka ƙara zuwa kotun ƙoli, inda yake ci gaba da ƙalubalantar zaɓen Gwamna Bassey Otu na APC.
A Alhamis ɗin nan, kotun ta kammala sauraron bahasi daga lauyoyin ɓangarorin biyu, kuma kafofin yaɗa labaran Najeriya kamar Daily Trust na ambato majiya daga kotun da ke tabbatar da cewa a washe gari Juma'a ne ita ma za a ji hukuncin shari'ar.
PDP da ɗan takararta suna ƙalubalantar Gwamna Otu ne da gabatar da takardun jabu ga hukumar zaɓe, sannan sun yi iƙirarin cewa ba a tsayar da shi takara ta sahihiyar hanya ba.
Zarge-zargen da lauyoyinsa s**a ce ba gaskiya ba ne, kuma masu ƙara sun gaza tabbatar da hujjar iƙirarin da s**a yi.