Gaskiya Jari

Gaskiya Jari Gaskiya jari

04/04/2024

Gobnatin jihar Jigawa Ta cikawa Alhazan jihar Naira miliyan daya ga kowannen su sakamakon ƙarin kudin hajjin bana.

Ko sabuwar Gobnatin jihar Jigawa zata sharewa Al'ummar karamar hukumar Taura hawayenta na Rashin wutar lantarki?A baya d...
22/03/2024

Ko sabuwar Gobnatin jihar Jigawa zata sharewa Al'ummar karamar hukumar Taura hawayenta na Rashin wutar lantarki?

A baya dai mun jiyo Al'ummar karamar hukumar Taura suna ta Allah wadai da Gobnatin da ta gabata bayan kammalawarta ba tare da ta cika mata Alkawarin kawo wutar lantarki karamar hukumar ba.

Sadai a wannan karon zamu iya cewa Allah yasa Sabuwar Gobnatin jihar Jigawar kar tabi sahun Gobnatin da ta gabata.

Al'ummar karamar hukumar Taura ko kuna da wani shiri Akan samar da Wutar lantarki?

Alh Nuraa Inuwa Galadima Taura.Na ɗaya daga cikin jagororin siyasar da ake alfahari dasu a jihar Jigawa duba da yadda ya...
22/01/2024

Alh Nuraa Inuwa Galadima Taura.

Na ɗaya daga cikin jagororin siyasar da ake alfahari dasu a jihar Jigawa duba da yadda ya kasance nagartacce mai bawa matasa dama da kuma shiga cikin Al'amuran su.

Nura A Inuwa Taura Wanda da yawa wasu s**a fi kiran shi da Ɗawisun Ɗanmoɗi.

Ya kasance daga cikin zaƙaƙuran matasan da gobanan jihar Jigawa mall Umar Namadi yake Alfahari da su.

𝗜𝗡𝗔 𝗧𝗔𝗞𝗔𝗜𝗖𝗜 𝗞𝗪𝗔𝗥𝗔𝗜 𝗗𝗔 𝗚𝗔𝗦𝗞𝗘 𝗔 𝗕𝗜𝗦𝗔 𝗥𝗔𝗦𝗛𝗜𝗡 𝗦𝗔𝗠𝗔𝗥 𝗗𝗔 𝗦𝗘𝗡𝗜𝗢𝗥 𝗦𝗘𝗖𝗢𝗡𝗗𝗘𝗥𝗬 𝗔 𝗠𝗔𝗭𝗔𝗕𝗔𝗥 𝗖𝗛𝗨𝗞𝗨𝗧𝗢 𝗧𝗔 𝗞𝗔𝗥𝗔𝗠𝗔𝗥 𝗛𝗨𝗞𝗨𝗠𝗔𝗥 𝗧𝗔𝗨𝗥𝗔.A halin y...
24/07/2022

𝗜𝗡𝗔 𝗧𝗔𝗞𝗔𝗜𝗖𝗜 𝗞𝗪𝗔𝗥𝗔𝗜 𝗗𝗔 𝗚𝗔𝗦𝗞𝗘 𝗔 𝗕𝗜𝗦𝗔 𝗥𝗔𝗦𝗛𝗜𝗡 𝗦𝗔𝗠𝗔𝗥 𝗗𝗔 𝗦𝗘𝗡𝗜𝗢𝗥 𝗦𝗘𝗖𝗢𝗡𝗗𝗘𝗥𝗬 𝗔 𝗠𝗔𝗭𝗔𝗕𝗔𝗥 𝗖𝗛𝗨𝗞𝗨𝗧𝗢 𝗧𝗔 𝗞𝗔𝗥𝗔𝗠𝗔𝗥 𝗛𝗨𝗞𝗨𝗠𝗔𝗥 𝗧𝗔𝗨𝗥𝗔.

A halin yanzu Ina mutukar damuwa da rashin cigaban da wasu daga cikin garuruwan kar-kararmu suke fuskanta a yanki na, na karamar hukumar Taura.

Bari nayi batu na akan mazabar chukuto.Mazabar chukuto ita ce mazaba mafi girman Al-ummah a yankin karamar hukumar Taura, Amma tabbas an barta a baya a bangarori da dama na cigaba,yau kimanin shekara 23 daga mulkin 𝗣𝗗𝗣 16𝗬𝗘𝗔𝗥𝗦 idan muka hada da Milkin 𝗔𝗣𝗖 7𝗬𝗘𝗔𝗥𝗦 duk tsawon wannan lokaci baza ka irga cigaba guda Biyar wannan mazabar ta samu ba.

𝗛𝗮𝗿𝗸𝗼𝗸𝗶𝗻 𝗱𝗮 𝗺𝗮𝘇𝗮𝗯𝗮𝗿 𝗰𝗵𝘂𝗸𝘂𝘁𝗼 𝘁𝗮 𝘇𝗮𝗺𝗮 𝗸𝗼𝗺𝗮 𝗯𝗮𝘆𝗮:

1-Bangaren Illimi:Koda bance wani Abu ba nasan Akwai tausayawa ga Al-ummar da sai sunyi tafiyar sama da kilomiter 4 zuwa biyr zasu sami makarantar da zasu tura "ya yansu.
Suna da ka garuruwa davburtalai sama da goma sha biyar Amma basu da Makarantar gobnati a kusa dasu.

wanda hakan ne yasa s**a zama koma baya a harkar illimi.

2- Rashin kyakykyawar kulawa a fanni lafiya.

3-Basu da hanyoyi koda na burji wanda zasu fito dasu zuwa bakin titti duk da garuruwan da suke cikin lungunan sune mafiya yawa a mazabar.

Akwai Abubuwa masu Dunbin yawa da Aka bar Al-ummar Chukuto ward a baya,Abin tausayi da takaicin shine tsawon wannan lokacin har yanzu da Za'a samar musu da t**i da makarantu ake yaudararsu a yayin yakin neman zabe.

𝘆𝗮 𝘇𝗮𝗺𝗮 𝗱𝗼𝗹𝗲 𝗔𝗹-𝘂𝗺𝗺𝗮𝗿 𝗰𝗵𝘂𝗸𝘂𝘁𝗼 𝘄𝗮𝗿𝗱𝘀 𝘀𝘂 𝗳𝗮𝗿𝗸𝗮 𝗱𝗮𝗴𝗮 𝗱𝗼𝗱𝗼𝗻 𝘀𝘂𝗺𝗮𝗿 𝗱𝗮 𝘀𝘂𝗸𝗮𝘆𝗶.

✍️𝗔𝘂𝘄𝗮𝗹 𝗥𝗮𝗯𝗶𝘂 𝗚𝗮𝗹𝗮𝗱𝗶𝗺𝗮 𝗧𝗮𝘂𝗿𝗮

11/06/2022

Ya kasance Duk Abinda zakayi kayishi cikin gaskiya domin ita Gaskiya jari ce.

Ni Auwalu Rabiu Galadima Taura, Bana Goyon Bayan Wakilin Da ya dauki Rabon kudi A matsayin Abun da zai dogara dashi A ma...
10/04/2022

Ni Auwalu Rabiu Galadima Taura,

Bana Goyon Bayan Wakilin Da ya dauki Rabon kudi A matsayin Abun da zai dogara dashi A matsayin Aikin Al-ummah.
Hasalima Bayyana Tarin makudan kudi kamar haka musamman a social media ina ganin wata hanya ce takara tabarbarewar Tsaro A kasa tare da samun tabarbarewr Tarbiya.

Saboda Ina da tabbacin babu wakilin da yake zuwa yakin Neman Zabe yayiwa Al-ummah Alkawarin Rabon idan ya dare kujera mulki,Ko wanne yana Alkawari ne akan Zai kawo Cigaba A bangare daban na sassan yankin da zai wakilta.

KUNGIYAR MATASA INA MAFITA FOUNDATION (MIMF).A yau Asabar ne wannan kungiya mai suna a sama shiyar karamar hukumar Taura...
20/02/2022

KUNGIYAR MATASA INA MAFITA FOUNDATION (MIMF).

A yau Asabar ne wannan kungiya mai suna a sama shiyar karamar hukumar Taura,tayi taron baje kolin kaddamar da Sanao'i da wasu matasa na karamar hukumar Taura, Wanda s**a mori tsarin.
Taron ya samu halartar mutane da dama daga cikinsu Akwai:
Mai Bawa mai taimakin Governor jihar Jigawa Shawara a harkokin yau da kullum,
Mai girma shugaban karamar hukumar Taura Hon Baffah Yahaya,
Mai girma Sarkin Taura Alh Rabiu Ali Sa'ad Taura,
Mai Girma Kaigaman Ringim Na I Alh Nasiru Ali Sa'ad Taura,
Mai girma Sardaunan Taura Alh Mahdi Aminu Taura,
Mai Girma councillor na mazabar Taura Hon Abdurrashid Zubairu Taura,
Shuwagabannin kungiyoyin Dalibai na karamar hukumar Taura,
Mamallaki Shafukan Sadarwa na Taura Writer's da Gaskiya jari, Auwal Rabiu Galadima Taura,
Dadai sauran many an baki.
Kungiyar matasan tasamu yabo daga bakin wakilin matemakin governor jihar jigawa da Shugaban karamar hukumar Taura Hon Baffah Yahaya Taura.
A jawabin Shugaban kungiyar comrd Saleh Nasir ya mika sakon godiya ga Shugaban karamar hukumar Taura Hon Baffah Yahaya Taura da kuma Sardaunan Taura Alh Mahdi Aminu, dama wasu manyan mutane Wanda s**a bawa tafiyar goyon baya tun daga kafuwarta har izuwa wannan Rana,ya kuma ja hankalin matasan da s**aci gajiyar shirin da suyi kokari wajen yin Amfani da hakan na samun madogara.

Gaskiya Jari news.

AKWAI GAZAWA KAKARA GA GOBNATIN KANO  KO MUCE MASU RUWA DA TSAKI KAN GYARA KANANAN TITUNA NA CIKIN GARI.A halin yanzu Al...
04/02/2022

AKWAI GAZAWA KAKARA GA GOBNATIN KANO KO MUCE MASU RUWA DA TSAKI KAN GYARA KANANAN TITUNA NA CIKIN GARI.

A halin yanzu Al-ummah da dama suna Allah wadai da halin ko in kula da gobnati takeyi, nayin Biris da Tituna wadanda s**a lalace a cikin Garin kano.
Ga tarin Manya manya flyover wadanda s**a lakume makudan kudade Amma Titunan da Al-ummar cikin garin sukebi yau da gobe yazama t**in Barin ciki ga mata masu nakuda da kuma saka Amai saboda Kwazazzabo.
Misali: Titin Bagobiri ko nace t**in kwanar yan Ghana ko yan Tifa tabbas Mai tsohon ciki zata iya zubarwa Idan har Tabi Titinann na Dan Lokaci.

Muna Kira Da babbar Murya Gobnatin Jihar Kano Ta Duba Yiyuwar Gyara Irin wadanan Tituna wadanda Al-umma Cikin gari suke bi Yau da Kullum.

Daga Bakin Mazauna Kano.

04/02/2022
LOKACIN DA NIGERIA TAYI RASHI NASARA A GASAR KOLLON KAFA NA NAHIYAR AFRICA KOWA YAYI CAA ANA TA FADAR MAGANGANU TARE DA ...
26/01/2022

LOKACIN DA NIGERIA TAYI RASHI NASARA A GASAR KOLLON KAFA NA NAHIYAR AFRICA KOWA YAYI CAA ANA TA FADAR MAGANGANU TARE DA NUNA ALHININ AKAN RASHIN NASARAR.

A YANZU KUMA NIGERIA TASAMU NASARAR A GASAR KARATUN AL-KUARA'ANI MAI GIRMA NA NAHIYAR AFRICA AMMA SHIRU KAKEJI.

MAFI AKASARI BAMA YAYATA ALKHAIRI SAI AKASIN HAKA.

LABARAN KOLLON KAFA GIDA DA KASASHEN KETARE:AN DAGA WASAN LIVERPOOL DA ARSENAL NA GOBE.GARKI ACADEMIC SUNYI RASHIN NASAR...
05/01/2022

LABARAN KOLLON KAFA GIDA DA KASASHEN KETARE:

AN DAGA WASAN LIVERPOOL DA ARSENAL NA GOBE.

GARKI ACADEMIC SUNYI RASHIN NASARA A HANNUN TAKWARARSU TA JAHUN ACADEMIC.

MOUNTINHO YA BUGA BALL BAYAN TA SHIGA RAGA TA DAWO TA TUBE TUBARON COACH DIN MANCHESTER UNITED A DAREN LITININ DIN DA TA GABATA.

DAGA WASAN ARSENAL DA LIVERPOOL:

Kungiyar kollon kafa ta Arsenal ta zargi ta kwararta ta liverpool da kitsa Dadai da badai ba, Ciki harda Dorawa Kansu jinya ta Covid 19, Domin A Fasa wasansu Da Arsenal, Sun tura da takardar Neman a daga musu da wasan Tun Ranar Talata, wadda FIFA Wacce ta tsani Arsenal ta karbi kokensu.

RA'AYOYIN YAN KALLO DAGA NAN TAURA:

Wani mai goyon bayan Arsenal ya bayyana hakan a matsayin Neman mafaka Sabo da Yadda tauraruwar Arsenal take haskawa a yanzu.

Wani Kuma ya bayyana Hakan A matsayin Ba Abun dazaayi mamaki bane duba ya yadda FIFA take treating din kungiyar Arsenal din A yanzu kamar Abun da yafaru a wasan kungiyar Arsenal din da Man city, Yace Kuma tabbas babu makawa Muddun Aka buga wasanan gobe Kungiyarsa ta Arsenal ce zatayi nasara Akan Liverpool din.

Wani mai goyon bayan Liverpool yace Wannan Wani dogon lokaci aka karawa Arsenal din na kwanaki a cikin kofin domin Tabbas Aka buga Saidai Arsenal ta mayar da hankalinta a sauran kofunan,Domin Ko A mafarki Arsenal bazatayi nasara akan Liverpool ba Duk da Rashin yan wasa da Liverpool din take dashi a yanzu.

Labarai daga ART.

Allah ya jikan Dan gwargwarmaya Alh Bashir Tofa.
04/01/2022

Allah ya jikan Dan gwargwarmaya Alh Bashir Tofa.

02/01/2022

BARKA DA SABUWAR SHEKAR MILADIYA 2022.

09/12/2021

WAI INA MANYAN MUNAFUKAN SANATOCI DA YAN MAJALISSUN DA SUKAYI GUM DA BAKINSU KO DAMAN ZAMN CINIKIN RAYUKANMU SUKEYI?

ABIN TAKAICI DA ALLAH WADAI BAZAI KAREBA A NIGERIA.Daga: Auwal Rabiu galadima Taura.Nigeria Ita ce kasar da Dan Ta'adda ...
08/12/2021

ABIN TAKAICI DA ALLAH WADAI BAZAI KAREBA A NIGERIA.

Daga: Auwal Rabiu galadima Taura.

Nigeria Ita ce kasar da Dan Ta'adda zai kashe Rayuka sama da dubu Amma Idan ya miqa wuya ayi mishi goma ta Arziqi.

Nigeria ita ce kasar da Ansan muhallin yan Ta'adda Amma Ake zuwa Neman sulhu gurinsu.

Nigeria ita ce kasar da Dan Ta'adda Zaiyi furucin cewa koda za'a rufe ko ina a kasar bazasu dena Samun Makamai ba.

Nigeria ita ce kasar da Dan Ta'adda Zaiyi Ta'addanci na Awanni Amma ba tare da hukuma tazo gurin ba.

Nigeria ita ce kasar da Duk Shekara Kasafin kudin tsaro yake zarta na komai Amma yan Ta'addan kasar sunfi jami'an Tsaron kasar kayan Aiki.

Nigeria ita ce kasar da Shugabbaninta suke guduwa da iyalansu don kada Ta'addanci ya shafesu.

Nigeria ita ce kasar Talaka yake Ta'addanci don ya kashe Dan uwansa talaka mai Neman Abinci.

Nigeria ita ce kasar Da bata Taba ware Ranar Bakin cikin Salwantar Rayuka ba.

Nigeria ita ce kasar da Dan kasar yake kare Azzaluman Shugabanni.

Nigeria ita ce kasar Da Marar lefi yake karyar shi Dan Ta'adda ne Don ya samu irin Tagomashin da ake bawa yan Ta'adda idan sun miqa wuya,Wannaan Tafaru a kano Sati daya zuwa biyu da ya gabata.

Nigeria ita ce kasar Da kullum talaka yake tafiya da extra money idan zashi Siyyaya Don gujewar karuwar farashin kayayyaki kamar yadda s**a zama Ruwan dare.

Nigeria ita ce kasar da Talaka bashi da kyashi sai Akan Dan uwansa Talaka.

Nigeria Allah Ka gyara mana,Allah ka shiga Lamarinmu Allah kazaba mana shugabbani na gari masu Tausayinmu.

NAGARTAR DAN TAKARAR SHUGABAN MATASA A KARKASHIN INUWAR JAM'IYAR APC.Hazikin Dan Takarar Shugaban matasa a karkashin tut...
06/12/2021

NAGARTAR DAN TAKARAR SHUGABAN MATASA A KARKASHIN INUWAR JAM'IYAR APC.

Hazikin Dan Takarar Shugaban matasa a karkashin tutar Jam'iyar APC kenann Wanda Akafi Sani da Ahmad Abba (Gata).
Wanda Binkkice ya Tabbatar Da cewa Haqiqa matasa Zasu Dama A karkashin Jagorancinsa,Duba da yadda ya riqe mukamai Daban Daban A baya kamar Shugaban Sashin karatu na tsangayar karantar Harshe A makarantar Jscoe gumel daga 2015-2017,Ya kuma Riqe Mai temakawa Na musamman Ga Daliban Jihar jigawa A Jimi'ar ABU Zaria Dake Kaduna.

Wacce Bajinta Ahmad Dan Gata yayi A loakcin Dalibtarsa?

Ahmad Abba (Gata) Ya wallafa Littatafai Na koyon Yaren Turanci Wanda yasamu Sahalewar kwarrarun Malamai A ciki da wajen Kasarnan.

Daga Ina ya futo?

Ya futo Daga Jihar Jigawa karamar Hukumar Garki. Tsohon Shugaban matasa Na Jam'iyar APC a karamar Hukumar,Kuma Wanda ya Temakawa Gobnan Jihar jigawa a lokacin yaain Neman Zaben A Shekara 2015.

Tabbas Ahamad Abba (Gata) Ana Zata mishi Alkhairi Idan Allah ya kaishi Ga Nasara.

12/11/2021

Mai girma governor Al-kawarin security light a Sabon bypass na Taura.Hakan zai taimaka wajen inganta tsaro.

Address

Jigawa

Telephone

+2349066118142

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Gaskiya Jari posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Gaskiya Jari:

Videos

Share