Masarautar Jama'are

Masarautar Jama'are Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Masarautar Jama'are, Media, No. 1 Muhammad Wabi Street Jama'are, Jama'are.
(2)

Barka da shan ruwa!Allah Ya karawa mai martaba sarki lafiya da nisan kwana!
29/03/2024

Barka da shan ruwa!

Allah Ya karawa mai martaba sarki lafiya da nisan kwana!

Masarautar Jama'are Jiya da YauMuhammadu Abubakar Sadau (Gabaiman Jama'are II)Muhammadu Wabi I (1811-1824) shi ne Sarkin...
13/02/2024

Masarautar Jama'are Jiya da Yau

Muhammadu Abubakar Sadau (Gabaiman Jama'are II)

Muhammadu Wabi I (1811-1824) shi ne Sarkin Jama'are na farko wanda ya je Sifawa yayi wa Shehu Usman Dan Fodio Mujaddadi mubaya'a ya karbi tutar Jihadi. Bayan Sarakuna biyu sun shude, wato Muhammadu Samboei (1824-1854) da kuma Muhammadu Maudo (1854-1862), sai Dan Muhammadu Wabi I ya zama Sarkin Jama'are na hudu, wato Muhammadu Sambo Gabaima (1862-1886). Muhammadu Sambo Gabaima ya haifi yara hudu wanda tarihi ya kiyaye, wato Muhammadu Wabi II Sarkin Jama'are na biyar (1886-1918), Waziri Saleh, Dada Magajiya da Kuma Muhammadu Sarkin Yaki Gazau.

Muhammadu Sarkin Yaki Gazau shi ne mahaifin Buba Likita da kuma Musa Muhammad, wato (Majidadin Jama'are), Musa Muhammad (Majidadin Jama'are) ya haifi Abubakar, wato Abubakar Musa Sadau. Shi kuma Abubakar ya haifi Muhammadu, wato Muhammadu Abubakar Sadau (Gabaiman Jama'are II). Madalla da wannan nasaba.

Sarautar Gabaima, Sarauta ce da tasamo asalai a Masarautar Jama'are. Sarkin Jama'are na bakwai,wato Muhammadu Wabi III Sarki Alhaji (1928-1966) shi ne Gabaiman Jama'are I. Kusan a iya cewa Sarauta ce ya 'ya'yan Sarki.
Saboda kusacin sa da Sarki, ana yi masa kirari da Gabaima Katangar Sarki, ko kuma Gabaima mai Sarki.

Muna addu'ar Allah Ya jikan magabatan mu. Allah Ya karbi shadar su, Allah Yasa suna tare da Malai'kun Rahama.

AN NAƊA "GABAIMAN JAMA'ARE"Yau Juma'a 09/02/2024 mai martaba sarkin Jama'are Alh. Nuhu Ahmad Wabi mni ya naɗa mai girma ...
09/02/2024

AN NAƊA "GABAIMAN JAMA'ARE"

Yau Juma'a 09/02/2024 mai martaba sarkin Jama'are Alh. Nuhu Ahmad Wabi mni ya naɗa mai girma Alh. Muhammad Abubakar Sadau a matsayin GABAIMAN JAMA'ARE a fadar sa dake Jama'are.

Muna taya mai girma sabon Gabaiman Jama'are murna tare da addu'an Allah ubangiji Ya taya shi riko.

GAYYATA!!! GAYYATA!!! GAYYATA!!! Mai Martaba Sarkin Jama'are Alh Nuhu Ahmad Wabi mni, Yana farin cikin gayytan Al'umma z...
08/02/2024

GAYYATA!!! GAYYATA!!! GAYYATA!!!

Mai Martaba Sarkin Jama'are Alh Nuhu Ahmad Wabi mni, Yana farin cikin gayytan Al'umma zuwa wajen nadin sarautar gargajiya ta Gabaiman Jama'are wanda za a naɗa Alh. Abubakar Sadau.

Za ayi bikin naɗin sarautar a gobe juma'a insha Allah, a fadar mai martaba sarkin Jama'are da misalin karfe 2:00 na rana.

Allah Ya ba da ikon halarta.
Ameen!

Allahu AkbarA irin wannan rana ta 06th February, shekara ta 2022 Allah ubangiji Ya karbi ran marigayi mai martaba sarkin...
06/02/2024

Allahu Akbar

A irin wannan rana ta 06th February, shekara ta 2022 Allah ubangiji Ya karbi ran marigayi mai martaba sarkin Jama'are na tara Alh. Dr Ahmadu Muhammadu Wabi lll OON.

A cikin wannan rana ta yau 06th February 2024 marigayi mai martaba sarki yake cika shekara biyu da rasuwa.

Muna Addu'ar Allah ubangiji Ya jikan mai martaba sarki Ya kuma sa Aljannatul Firdaus itace makoma, Ya kuma ci gaba da bamu hakurin jure wannan babban rashin.

Majallisar Masarautar Jama'are Karkashin Jagorancin, Mai Martaba Sarkin Jama'are HRH Alhaji Nuhu Ahmad Wabi, mni.Ta Karr...
22/01/2024

Majallisar Masarautar Jama'are Karkashin Jagorancin, Mai Martaba Sarkin Jama'are HRH Alhaji Nuhu Ahmad Wabi, mni.

Ta Karrama Mai Girma Gwamnan Jahar Bauchi Sen. Bala Abdulkadir Mohammed Kauran Bauchi, Da Sabuwar Sarautar Sadaukin Jama'are na Farko A Wannan Rana Mai Albarka Ta Litinin 22/01/2024.

Muna Addu'ar Allah Yaja Zamanin Mai Martaba Sarki Yasa Agama Da Duniya Lafiya.

Inna Lillahi Wa Inna ilaihi Raji'un.Allah Yayi wa Mohammed Baba Gidado(Jarman Jama'are) Rasuwa. Allah Ya jiqan sa da rah...
25/12/2023

Inna Lillahi Wa Inna ilaihi Raji'un.

Allah Yayi wa Mohammed Baba Gidado(Jarman Jama'are) Rasuwa. Allah Ya jiqan sa da rahama

Jana'iza 3:45pm a Masallacin JIBWIS Gwallaga, Bauchi

Kowacce al'umma tana alfahari da shugaban ta, wanda ya ke shugabanci bisa tsari da karantarwar magabata. Shi ne Sarkin J...
15/12/2023

Kowacce al'umma tana alfahari da shugaban ta, wanda ya ke shugabanci bisa tsari da karantarwar magabata.

Shi ne Sarkin Jama'are na goma, Nuhu jikan Nuhu, dan Sarkin Jama'are na tara, Alhaji Ahmadu Muhammadu Wabi III oon (1970-2022), jikan Sarkin Jama'are na bakwai, Alhaji Muhammadu Wabi III (1928-1966), dan Sarkin Jama'are na shida, Muhammadu Goje Maje Bauchi (1918-1928), dan Sarkin Jama'are na biyar, Muhammadu Wabi II (1886-1918), dan Sarkin Jama'are na hudu, Muhammadu Sambo Gabaima (1862-1886) dan Sarkin Jama'are na farko, Muhammadu Wabi I (1811-1824) wanda yayi Shehu Mujaddadi Mubaya'a, yakarbo tutar jugadi a farkon karni na goma shatara.

A daya bangaren kuma, Sarkin Kano Ibrahim Dabo (Chigari) shine mahaifin Sarkin Kano Abadullahi Maje Karofi, Abdullahi Maje Karofi ya haifi ya haifi Sarkin Kano Usman II (Usman Dan Tsoho), Usman Dan Tsoho ya haifi Abdullahi Wambai (Maibindiga), Wambai Abdullahi ya haifi Hauwa'u (Goggon Marai), ita ce matar Sarkin Jama'are na shida wato Muhammadu Goje, Hauwa'u ta haifi Mairama Zainabu (Goggo Danejo), Danejo ta haifi Hajiya Amina, ita kuma ta haifi Maimartaba Sarkin Jama'are na gomae, Alhaji Nuhu Ahmad Wabi mni. Ransarki Yadade!!!. Madalla da wannan nasaba.

Allah Yataimaki Sarki, Allah Yaja Zamanin Sarki.
Juma'at Mubarak.

Ran sarki ya Dade✊
17/10/2023

Ran sarki ya Dade✊

MAZAN JIYA MAJIDADI Alhaji Musa Muhammadu Gazau jikan sarkin jama'are Muhammadu Sambo Gabaima. (Majidadin Jama'are,Hakim...
12/10/2023

MAZAN JIYA MAJIDADI

Alhaji Musa Muhammadu Gazau jikan sarkin jama'are Muhammadu Sambo Gabaima. (Majidadin Jama'are,Hakimin Jama'are)

Allah yakyauta makwancin Hakimi yamasa rahama.

Kasar Jama'are Jiya Da Yau.

Marigayi Maimartaba Sarkin Jama'are na tara (9), Alhaji Ahmadu Muhammadu Wabi III oon (1970-2022). Ya ga ji dan'uwansa S...
10/10/2023

Marigayi Maimartaba Sarkin Jama'are na tara (9), Alhaji Ahmadu Muhammadu Wabi III oon (1970-2022). Ya ga ji dan'uwansa Sarki Muhammadu Sabo Sarkin Jama'are na takwas (1966-1970), wanda shi kuma ya gaji mahaifinsu Sarkin Jama'are na bakwai wato, Muhammadu Wabi III (1928-1966). Dattijon basarake mai cikkakiyar nasaba da haiba. Mahdi mai dogon zamani ( shekaru hamsin da biyu miladiyya ko hamsin da hudu hijiriyya a gadon sarauta. Damo sarkin hakuri. Yana da kawaici da sanin yakamata, sabodahaka burin sa yazama kadan. Yarasu ya bar matan aure biyu, da 'ya'ya ka na da jikanu da tattaba kunne.

Allah Ya jikan Sarki Ahmadu, Allah Ya karbi Shahadar sa. Allah Yasa yana tare da Mala'ikun Rahama.

GWAMNATIN JIHAR BAUCHI TAWARE NAIRA MILIYAN 499 DOMIN SAKE FASALIN MASARAUTAR JAMA'ARE.mai girma gwamnan jihar Bauchi Se...
26/09/2023

GWAMNATIN JIHAR BAUCHI TAWARE NAIRA MILIYAN 499 DOMIN SAKE FASALIN MASARAUTAR JAMA'ARE.

mai girma gwamnan jihar Bauchi Senator Bala A. Mohammed CON (Kauran Bauchi Jagaban Katagum) yabada damar sake gyara da tsarin fasalin masarautar jama'are wadda gwamnatinsa taware makudan kudade har naira miliyan dari hudu da casa'in da tara 499M wadda tuni aka bada wannan kudi ga yan kwangila domin fara wannan aiki, ta bakin kwamishinan ma'aikatar kananan hukumomi da masarautu ta jihar Bauchi Alhaji Ahmed Aliyu Jalam ya bayyana a yayin ziyarar gani da ido dayakawo masarautar jama'are domin gani da ido, a jawabin mai martaba sarkin jama'are Alhaji Nuhu Ahmad Wabi, mni ya godewa mai girma zababben gwamnan jihar Bauchi Senator Bala A. Mohammed CON bisa wannan namijin kokari yayi nasake farfado da bangaren masarautu a fadin jihar yayi jan hankali da yan kwangila domin suyi ingantaccen aiki bisa aminci da inganci.

Engr Mahmoud Ibrahim Jama'are
Chief Media Press to the Emirate Council.

DAGA MAIDUGURI BIRNIN SHEHU A yau mai martaba sarkin jama'are Alhaji Nuhu Ahmad Wabi mni, tare da yan tawagarsa s**a sau...
18/09/2023

DAGA MAIDUGURI BIRNIN SHEHU

A yau mai martaba sarkin jama'are Alhaji Nuhu Ahmad Wabi mni, tare da yan tawagarsa s**a sauka birnin maiduguri dake jihar Borno bisa ziyarar kwana uku dazasu gabatar a masarautun daular Borno Empires wadda s**a samu kyakkyawan tarba daga mai martaba Shehun Borno His Highness Alhaji Dr. Abubakar Umar Ibn Garbai El-kanemi II CFR, tare da yan majalisarsa muna addu'ar Allah yadawo da sarki gida lapiya Aamin.

Marigayi Alhaji Umar Abubakar Umar (Chiroman Gombe) Yayin Wani Meeting A Garin Lagos, Lokacin Yana Director Na Railway 🚂...
26/08/2023

Marigayi Alhaji Umar Abubakar Umar (Chiroman Gombe) Yayin Wani Meeting A Garin Lagos, Lokacin Yana Director Na Railway 🚂 Wadda Ya Samu Rakiyar Amininsa Marigayi Alhaji Ahmadu Malle (Dan Iyan Jama'are) Tare da Marigayi Alhaji Muhammadu Saje Bingel Dada (Danruwatau Chiroman Gombe) Anyi Hoton Cikin Shekarar 1972.

Allah Ya Jikansu da Rahama, Yasa Aljannar Firdausi Tazama Makomarsu

Jiya asabar maimartaba sarki ya samu halartar bikin kaddamar da daliban farko na kwalejin tarayya ta ilimi dake Jama'are...
23/07/2023

Jiya asabar maimartaba sarki ya samu halartar bikin kaddamar da daliban farko na kwalejin tarayya ta ilimi dake Jama'are (Federal College of Education Jama'are)

Sanarwa--- Sanarwa---- Sanarwa daga Fadar uban kasa mai martaba sarkin jama'are HRH Alhaji Nuhu Ahmad Wabi, mni Ana sana...
18/07/2023

Sanarwa--- Sanarwa---- Sanarwa daga Fadar uban kasa mai martaba sarkin jama'are HRH Alhaji Nuhu Ahmad Wabi, mni

Ana sanar da daukacin Al,ummar masarautar jama'are cewa idan Allah ya kaimu gobe za,a gabatar da sallar Rokon Ruwa a daukacin masallatan idi na masarautar jama'are dama daukacin garuruwan masu girma hakimai dake daukacin karamar hukumar jama'are da misalin karfe 8:00 na safe, idan Allah ya kaimu.

Sanarwar ta kara da cewa idan kuma Allah Yasa an samu Ruwan cikin Daren Nan to ba sai Al,umma sun fita domin gabatar da sallar ba, muna addu'ar ya ubangiji Allah madaukakin sarki ya bamu damu mai albarka, ya ubangiji ya bada ikon halartar ameen ya rabbi.

Engr Mahmood Ibrahim Jama'are chief media to the jama'are emirate council

17/07/2023

SANARWA!

Gobe Talata Insha Allah za'a fita Sallah rokon ruwa da karfe 8:00am a dukkan masallatan Idi na Masarautar Jama'are.

Mai Girma Hakimin Galdimari Kuma Santurakin Jama'are Alh. Adamu Ahmad Wabi yayin hawan bikin Sallah na Bana!ALLAH Ya kar...
05/07/2023

Mai Girma Hakimin Galdimari Kuma Santurakin Jama'are Alh. Adamu Ahmad Wabi yayin hawan bikin Sallah na Bana!

ALLAH Ya karawa rayuwa Albarka Santuraki!

Barkanmu da Sallah Amanan Mai martaba Sarki!Allah Ya fissheku kin kunyar Mai martaba sarki. AMEEN!
29/06/2023

Barkanmu da Sallah Amanan Mai martaba Sarki!

Allah Ya fissheku kin kunyar Mai martaba sarki. AMEEN!

Barka Da Sallah Daga Masarautar Jama'are !Mai martaba sarkin Jama'are Alh. Nuhu Ahmad Wabi Mni yayin hawan bikin Sallah ...
28/06/2023

Barka Da Sallah Daga Masarautar Jama'are !

Mai martaba sarkin Jama'are Alh. Nuhu Ahmad Wabi Mni yayin hawan bikin Sallah Babba na wannan shekaran 1444AH/2023.

Allah Ya karawa Mai martaba sarki lfy da Nisan Kwana!

28/06/2023

Barka Da Sallah! ALLAH Ya karbi ibadun mu, Ya Kuma maimaita Mana!

Sanarwa--- Sanarwa ----Sanarwa ----SanarwaKai Tsaye Daga Fadar Uban Kasa Mai Martaba Sarkin Jama'are HRH Alhaji Nuhu Ahm...
28/06/2023

Sanarwa--- Sanarwa ----Sanarwa ----Sanarwa

Kai Tsaye Daga Fadar Uban Kasa Mai Martaba Sarkin Jama'are HRH Alhaji Nuhu Ahmad Wabi, mni.

Ana sanar da daukacin Al,ummar Musulmai na masarautar jama'are, cewa cikin ikon Allah da yardar sa uban kasa mai martaba sarki zai kasance a babban masallacin Idi dake unguwar kofar Kudu a cikin garin jama'are, da misalin karfe 8:30 na safe idan Allah ya kaimu domin gabatar da sallar wannan shekarar, Sanarwa ta kara da cewa idan kuma an samu Ruwan sama kafin Lokacin za,a gudanar da sallar a babban masallacin juma'a na kofar fadar mai martaba sarki dake cikin garin jama'are, muna addu'ar ya ubangiji yasa a hau idi lafiya a sauko Lafiya.

Engr Mahmood Ibrahim Jama'are chief media na fadar uban kasa mai martaba sarkin jama'are HRH Alhaji Nuhu Ahmad Wabi, mni.
09/Zhul'hajj/1444hjr.
27/06/2023

19/06/2023

HAKIMIN CIKIN GARIN JAMA'ARE

Mai girma Wamban Jama'are Alhaji Abubakar Mohammed Wabi, Bauchi State Chairman local government service commission muna addu'ar Allah yaka girma da daukaka daraja da kariya a gidan duniya da gobe kiyama rankai dade.✊🏻✊😍

08/06/2023

Kidan Ganga kura tare da Algaita da kakaki!

Ana gudanar da irin wannan kida ne a irin Wannan dare na daren Juma'a a al'adar Masarautar Jama'are !

Dattijon Basarake ga Hakuri da Dattaku!!Marigayi Mai martaba sarkin Jama'are Alh Dr Ahmadu Muhammad Waɓi III OON        ...
08/06/2023

Dattijon Basarake ga Hakuri da Dattaku!!
Marigayi Mai martaba sarkin Jama'are
Alh Dr Ahmadu Muhammad Waɓi III OON
{Emir of Jama'are}

Allahu Akbar!A wannan rana ta 01/05/2023 Marigayi Shamakin Jama'are Mal. Yalwaji Musa yake cika Shekara Daya da komawa g...
01/05/2023

Allahu Akbar!

A wannan rana ta 01/05/2023 Marigayi Shamakin Jama'are Mal. Yalwaji Musa yake cika Shekara Daya da komawa ga mahaliccin sa.

Tabbas Masarautar Jama'are tayi rashin jajircecce wajen cigaban Masarautar Jama'are da Al'ummar Masarautar, Kuma tarihi bazai manta da shi ba.

Muna Masa Addu'a Allah Ubangiji Ya jikan sa da rahama, Ya kuma Albarkaci bayan sa. Ameen!

Tawagan mai girma Santurakin Jama'are Alh.  Adamu Ahmad wabi (Hakimin Galdimari) yayin bikin hawan Sallah na bana 1444AH...
26/04/2023

Tawagan mai girma Santurakin Jama'are Alh. Adamu Ahmad wabi (Hakimin Galdimari) yayin bikin hawan Sallah na bana 1444AH/2023.

Hawa yayi kyau Mai Girma Santuraki. Allah Ya fissheka jin kunyar Sarki✊

Tawagan mai girma Wakilin Wajen Jama'are Alh. Abdullahi Sa'adu Chalawa yayin bikin hawan Sallah na bana 1444AH/2023.Hawa...
26/04/2023

Tawagan mai girma Wakilin Wajen Jama'are Alh. Abdullahi Sa'adu Chalawa yayin bikin hawan Sallah na bana 1444AH/2023.

Hawa yayi kyau Mai Girma wakilin waje. Allah Ya fissheka jin kunyar Sarki✊

21/04/2023

Address

No. 1 Muhammad Wabi Street Jama'are
Jama'are

Telephone

+2349069167936

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Masarautar Jama'are posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Videos

Share

Category


Other Media in Jama'are

Show All