05/08/2024
๐๐๐ฅ๐๐ฒ๐ฒ๐๐ซ ๐๐ฎ๐ญ๐๐ง๐ ๐๐ ๐ค๐จ ๐๐๐ฅ๐๐ฒ๐ฒ๐๐ซ๐ฆ๐ฎ ๐๐๐ง ๐๐๐ฃ๐๐ซ๐ข๐ฒ๐?
Abinda nake lura da shi a yau, duk wanda ya zo maka da wata buฦata sai ka ฦoฦarta ka biya masa, daga nan sai ya ษauka shi fa ya zama ษaya daga cikin iyalanka ta yadda duk wata matsalarsa da ta taso kai ne mai warware ta. Idan abinci ne misali ka ba shi to da ya ฦare zai dawo maka. Idan magani ne ka saya masa yana shanyewa zai sake neman ka. In kuma ka taimaka masa ne wajen aurar da 'yarsa to da ta haifu ka jira zai ฦwanฦwasa maka.
Ko kun lura da e-begging wanda ya zama ruwan dare a yau? A kullum na wayi gari saฦonni suke shigowa ratata a cikin wayata daga mutanen da ban sani ba, kowa da irin kokensa haษe da lambar akawun ษinsa.
Akwai kuma ฦaruwar bara a cikin ฦananan yara waษanda ba su ko fara bambance dama daga hagunsu ba.
Kuna ganin wannan tasirin tsananin da muka ฦara shiga a ciki ne? Ko mutuwar zuciya ne? Ko kuma halayya ce daman ta 'yan Adam, ko tamu' yan Najeriya?
Babu shakka muna cikin lokacin da duk wanda Allah ya yi masa buษi ko kaษan ne ya kamata ya tausaya ma mutane ya taimake su, amma kuma komai yana da ma'auni.
Allah ya taimake mu, ya yaye mana talauci, mutuwar zuciya da sauran musibun rayuwa.
Prof. Mansur Sokoto, mniProf. Mansur Sokoto, mniProf. Mansur Sokoto, mniProf. Mansur Sokoto, mniProf. Mansur Sokoto, mniProf. Mansur Sokoto, mniProf. Mansur Sokoto, mni