Fityanul Islam Of Nigeria

Fityanul Islam Of Nigeria Yada Soyayyan Annabi ﷺ Da Salihan Bayin Allah Waliyai Tare Da Fadakarwa Tunatarwa Ga Al'ummar Musulmi Alhamdulillah

Inna'lillah Wa'inna Ilaihir Raji'un Allah Ya Yiwa Sayyada Khadijah (SAYYADA AZUMI) Babbar 'Yar Maulana Sheikh Aliyu Hara...
15/01/2025

Inna'lillah Wa'inna Ilaihir Raji'un

Allah Ya Yiwa Sayyada Khadijah (SAYYADA AZUMI) Babbar 'Yar Maulana Sheikh Aliyu Harazumi Rasuwa.

Sayyada Khadijah Yaya Ga Khalifa Tijjani Sheikh Aliyu Harazumi Kano.

Za'ayi Sallah Jana'zar Sayyada Khadijah Yau (Laraba) Da Misalin Karfe 10:00am A Zawiyyar Sheikh Aliyu Harazumi Hausawa Kano.

Muna Addu'an Allah Ya Jikan Ta Da Rahma Ya Gafarta Mata, Albarkan RASULULLAH (SAW).

GA WATA TUNATARWAWannan karatu ne mai kunshe da dokokin Sallah wanda babban malamin mu Sheikh Ubale Adakawa Kano ya gaba...
14/01/2025

GA WATA TUNATARWA

Wannan karatu ne mai kunshe da dokokin Sallah wanda babban malamin mu Sheikh Ubale Adakawa Kano ya gabatar a cikin tambaya da amsa.

Insha Allahu zai amfani duk wanda ya saurara kuma yayi aiki dashi. Musamman a wannan zamanin namu wanda ayyukan kura-kurai a sallalolin mu munyi yawa sosai.

Don Allah duk wanda ya samu wannan sakon yayi kokari ya rika aikatawa domin samun cin ribar wannan garabasar. Sannan Kayi kokari ka tura ma wasu domin su amfana.

Akwai link na karatun a comment section.

Allah ya saka masa da alkhairi. Amiiiin

INNAL'ILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN Wasu Daga Cikin Ƴan Agajin Mu Fityanul Islam Dake Kudancin Kaduna, Sun Sami Hatsarin...
14/01/2025

INNAL'ILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN

Wasu Daga Cikin Ƴan Agajin Mu Fityanul Islam Dake Kudancin Kaduna, Sun Sami Hatsarin Mota Akan Hanyarsu Ta Komawa Gida Bayan Kammala Taron Agaji Na jihar Kaduna.

Muna Roƙon Allah swt Yabasu Lafiya, Ya Kuma
Yakiyaye Gaba. AMIIN

Daga: Muhammad Bello Agaji

Inna'lillah Wa'inna Ilaihir Raji'unDaya daga cikin almajiran Sheikh Abul Fath RA Malam Hussaini Ibrahim ya rasuwa. Za'ay...
11/01/2025

Inna'lillah Wa'inna Ilaihir Raji'un

Daya daga cikin almajiran Sheikh Abul Fath RA Malam Hussaini Ibrahim ya rasuwa. Za'ayi sallah jana'zar sa da misalin karfe 11:00am dake Masallacin Madinatu Sheikh Ahmad Abulfathi.

Allah ya jikan sa ya gafarta masa. Amiiiin

Babban Limamin Masallacin Juma'a Tudun Wada Zari'a. Khalifa Sheikh Muhammad Dantini Liman, Yayi Gargadi Kan Masu Wasa Da...
11/01/2025

Babban Limamin Masallacin Juma'a Tudun Wada Zari'a. Khalifa Sheikh Muhammad Dantini Liman, Yayi Gargadi Kan Masu Wasa Da Sallah.

Shehin Malamin yayi gargadin ne a wata huduba da ya gabatar a yau Juma'a, a babban Masallacin Juma'a dake Tudun Wada Zari'a.

Ya Kara da cewa, Manzan Allah S.A.W Yace, Me tarukus salati idan yane mi 'yayanku Mata kada ku aura mashi, Kuma kada ku isar mashi da burinshi.

Haka zalika duk garin da ake buqatar albarka ga hatsi da dabbobi da fatauci da 'yayanta to idan akwai me tarukus salati a fiitar dashi daga garin saboda Albarka ta tabbata a Garin.

Yace, Idan me tariku salati ya mutu aka zuba kasa a kabarinsa wuta tana tartsasi a kabarin, Kuma se ya k**a Nishi, Sannan maciji ze zo mishi cikin kabarin Wanda ake cema sadauki, idanun macijin tamakar lagwanin wuta ne dake habarbaka wajen waiqawa k**ar walqiya, muryarshi misalin Kamar tsawa ne me yankewar duk abinda tasamu ko mafi muni ma daga haka.

Kuma ze zo da guduma a hannunsa ta bakin karfe Wanda da anbigi dutse anan duniya duk girman dutsen ze rai raye ya koma k**ar turbaya saboda abinda yake haduwa dashi na azaba.

Ina sarakuna.
Ina wazirai.
na runduna.
Ina mataimaka.
Ina Mai yawan zaluncin talikai.
Ina Mai yawan cin dukiyar marayu.
Ina me yawan sabon Allah.

ko wanne daga cikin wadannan ya shagalta Yana zaton Allah ya manta dashi.

Na rantse da Allah ubangiji be manta ga Barin abinda suke aikawa ba yadai jinkirta musu ne har zuwa ranar alqiyama.

Hadisin ya tabbata daga Manzan Allah cewa, Lallai yin addu'a cikin watan rajab Allah na saurin karba.

MARHABAN DA ZAGAYOWAR WATAN DA AKA HAIFI MAULANMU SHEHU IBRAHIM (R.T.A)ANNABI (S.A.W) Yana cewa "ku saurara hakika watan...
10/01/2025

MARHABAN DA ZAGAYOWAR WATAN DA AKA HAIFI MAULANMU SHEHU IBRAHIM (R.T.A)

ANNABI (S.A.W) Yana cewa "ku saurara hakika watan RAJAB watan Allah ne, hak**a watan SHA'ABAN wata nane, har ila Yau watan RAMADAN watan Al-ummata ne

Wanda yayi wanka Ranar 1 ga watan RAJAB tare da niyyar wannan wata Allah zai kan kare masa zunubansa zai koma k**ar yadda mahaifiyarsa ta haifeshi.

Wanda yayi AZUMI Alhamis ta farkon watan RAJAB Al-Qawarin Allah ya tabbata a kansa na shiga AL- JANNAH.l
FALALAR WATAN RAJAB

(1) Wanda yayi AZUMI Rana ta 1 yaddar Allah ta tabbata gare shi.

(2) Wanda yayi AZUMI Rana ta 2 Allah
zai ninka masa aikinsa na Al-hairi A Ranar lahira adadin duwatsun duniya so 2.

(3) Wanda yayi AZUMI Rana ta 3 Allah zai sanya wata katanga tsakaninsa da wuta wanda tsawanta tafiyar shekara guda ce.

(4) Wanda yayi AZUMI Rana ta 4 Allah zai kiyaye shi daga dukkan bala'i da sharrin Aljanu da kuturta da fitinar dujal.

(5) Wanda yayi AZUMI Rana ta 5 Allah zai Amintar dashi daga azabar Qabari.

(6) Wanda yayi AZUMI Rana ta 6 Allah zai fitar dashi daga Qabarinsa ranar lahira fuskar sa tana haske k**ar wata daren sha 14.

(7) Wanda yayi AZUMI Rana ta 7 Allah zai rufe masa kofofin wutar JAHANNAMA guda 7.

(8) Wanda yayi AZUMI Rana ta 8 Allah zai bude masa kofofin AL-JANNAH guda 8.

(9) Wanda yayi AZUMI Rana ta 9 Allah zai fito dashi daga cikin Qabarinsa ranar lahira yana fadin "LA'ILAHA ILLALLAHU kuma babu abinda fuskar sa zata rinqa hange sai AL-JANNAH.

(10) Wanda yayi AZUMI rana ta goma Allah zai sanya masa shimfida a kan hanyar SIRADI yana takara har ya shige cikin AL- JANNAH.

'YAN-UWAN KUN BIYONI BASHIN SAURAN KWANAKI 20. DA YARDAR ALLAH 9 GA WATAN rajab ZAN KAWO MAKU SAURAN.

ALLAH SWT ya bamu Albarkar dake cikin wannan Wata mai Albarka Bijahi S.A.W. Amiiiin

Sayyida Faɗima ita kaɗaice macen da ta hau matsyin da wata mace bata taɓa hawa ba, wato khilafar Allah a ban ƙasa.Agun s...
22/12/2024

Sayyida Faɗima ita kaɗaice macen da ta hau matsyin da wata mace bata taɓa hawa ba, wato khilafar Allah a ban ƙasa.

Agun shehu Tijjani Sayyida Faɗima tafi duk wani wanda ba Annabi ba, wanda duk sahabbai na bayan ta a ciki har Sayyid Abubakar, b***e kuma mata da basa wuce matsayin siddiƙiyya.

وأما فاطمة فإنها وصلت المرتبة القطبانية العظمى؛ لأنها استمدت الكمالات الإلهية التي تتحمل بها سر الاسم الأعظم، ولا مطمع للنساء في استمداد تلك الكمالات منه إلا فاطمة فقط.
Amma Faɗima ita takai martabar ƙuɗbaniyya mafi girma (gausiyya), domin ta samu k**aloli na ubangiji, wanda da shine take ɗauke da sirrin suna mafi girma, kuma babu matsanmata (hanya) ga wata mace cikin samun wannan madadin daga Annabi ﷺ sai ita kawai.

Babu wanda ze iya mubasharar ɗaukar wannan kujerar bayan Annabi ﷺ sai faɗimar tsokar sa , shiyasa ta cika mai wata 6 Alahassalam.

Tarihi ya tabbatar da wannan shine Masallacin Fasah, Masallacin Fasih, dake Madina, daya daga cikin masallatan Manzon Al...
21/12/2024

Tarihi ya tabbatar da wannan shine Masallacin Fasah, Masallacin Fasih, dake Madina, daya daga cikin masallatan Manzon Allah SAW yayi sallah a cikinsa, Masallacin Madina yana nisa da kilomita 4.5 daga Al- Wannan masallacin na Fassah yana arewacin masallacin Harami kuma yana kusa da makabartar Shahidai.

Allah ya bamu albarkan Annabi ﷺ, ya saka wa iyayen mu da malaman mu da alkhairi. Amiin

Daga: Tijjaniyya Media News

DA ƊUMI-ƊUMI: Gwamnatin Jihar Bauchi Ta Gina Katafariyar Makaranta Tunawa Da Shéikh Dahiru BauchiGwamnatin Jihar Bauchi ...
20/12/2024

DA ƊUMI-ƊUMI: Gwamnatin Jihar Bauchi Ta Gina Katafariyar Makaranta Tunawa Da Shéikh Dahiru Bauchi

Gwamnatin Jihar Bauchi ta kaddamar da makarantar tunawa da Sheikh Dahiru Usman Bauchi, wadda ita ce irinta ta farko a Arewa maso Gabas.

Gwamnan Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya bayyana cewa an shirya gina irin wannan makaranta a dukkan kananan hukumomi 20 na jihar. Makarantar za ta taimaka wajen magance matsalar yara da ba sa zuwa makaranta, tare da samar da yanayi mai kyau domin karatun yara da kuma inganta yanayin aiki ga malamai.

Wannan yunkuri wani muhimmin mataki ne na gwamnatin jihar wajen bunkasa ilimi da kuma karfafa tarbiyya da ci gaban al'umma.

Allah ya saka masa da mafificin alkhairi, ya kara wa Maulana Sheikh lafiya da nisan kwana, albarkan Annabi Muhammadu ﷺ. Amiiiin

NASIHAR Da IMAM ABUL BASHARIYYUN YAYIWA ALMAJINSA SALMAN KENAN Wannan NASIHAR Da Zamu yi Riko ita kuma Zamuyi Amfani da ...
18/12/2024

NASIHAR Da IMAM ABUL BASHARIYYUN YAYIWA ALMAJINSA SALMAN KENAN

Wannan NASIHAR Da Zamu yi Riko ita kuma Zamuyi Amfani da ita da Wallahi mun Zauna Lafiya.

Ga NASIHAR k**ar Haka

Har Kullum Idan Kana so Ka ci Nasara A Rayuwa, ka fara Wanke Zuciyarka Kafin Jikinka Kuma ka wanke Harshenka Kafin Hannunka Sannan Ka kyautata Zato ga mutane.

A Kullum A Rayuwa Ka kasance Mai Kyakkyawar Zuciya Da Ikhlasi, kada ka Bayyanawa Duniya Aibun Wani don Mayar Da Kanka Tsarkakakke,

Kada ka Kushe Wani Don Samun Yabo, Kada ka Sayi Farin Jini Ta Hanyar Dorawa Wani Bakin Jini

Allah Ya Sa Mu Dace Albarkan ANNABI SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA. Amiin

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima tare da rakiyar gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum, da Engr Ibrah...
17/12/2024

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima tare da rakiyar gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum, da Engr Ibrahim Umar na Hukumar Tashoshin Ruwa ta Najeriya; da jami’an Ofishin Jakadancin Najeriya a Saudiyya sun Ziyarci Raudah Manzon Allah SAW dake MADINA a kasar Saudia Arabia.

Allah ya karbi ibada ya dawo dasu lafiya. Amiin

Wannan shine shahararren mai Da'awah kuma babban malamin Addinin Musulunci a Africa Sheikh Muhammadu Sabihu Gwammaja.She...
17/12/2024

Wannan shine shahararren mai Da'awah kuma babban malamin Addinin Musulunci a Africa Sheikh Muhammadu Sabihu Gwammaja.

Shehin malamin ya karar da rayuwar sa wurin wa'azantar da al'ummar musulmai da tsoratar da al'umma azabar da Allah zaima wanda ya saba masa a lahira tare da zamantakewar sure.

Yayi rayuwa a tsakanin jihar Kano da Borno, da wasu jihohin arewacin Najeriya. Kafin rasuwar sa ya hadu da makiya wurin wa'azin sa.

Allah ubangiji madaukakin sarki ya jikan sa da rahma ya yafe masa kura-kuran sa. Amiin

Daga: Babangida A. Maina
Tijjaniyya Media News

YANZU -YANZU: Mun samu labarin rasuwar Gwani Lawi Gwani Ɗan Zarga, bayan fama da jinya yau talata.Za'ayi sallah jana'iza...
17/12/2024

YANZU -YANZU: Mun samu labarin rasuwar Gwani Lawi Gwani Ɗan Zarga, bayan fama da jinya yau talata.

Za'ayi sallah jana'iza Karfe 4:00pm na yamma.

Muna rokon Allah ya jikan sa ya gafarta masa ya sanya ALKUR'ANI ya cece shi tare da mu ya jikan iyayen mu da malaman mu baki daya Amiiiin Yaa ALLAH

Daga: Mu Koma Tsangaya

JANA'IZA CIKIN HOTUNAN: Dubban jama'a ne s**a halarci jana'izar Sayyadi Aliyu Harazumi dan Khalifa Sheikh Muhammad Fatih...
17/12/2024

JANA'IZA CIKIN HOTUNAN: Dubban jama'a ne s**a halarci jana'izar Sayyadi Aliyu Harazumi dan Khalifa Sheikh Muhammad Fatihu Gibrima Ra a Masallacin sa dake karamar hukumar Nguru jihar Yobe.

Allah ya sadashi da Manzon Allah SAW ya jikan sa ya gafarta masa. Amiiiin Yaa ALLAH

Hoto: Muftahu Yahaya Mai Dandarani

Inna'lillah Wa'inna Ilaihir Raji'un Allah ya yiwa dan Khalifa Sheikh Sheikh Fatihu Ngibirima wato Sayyadi Aliyu Harazimi...
16/12/2024

Inna'lillah Wa'inna Ilaihir Raji'un

Allah ya yiwa dan Khalifa Sheikh Sheikh Fatihu Ngibirima wato Sayyadi Aliyu Harazimi rasuwa

Za'ayi gudanar da Sallah gobe Talata da misalin karfe 10:00am, a Zawiyyar Sheikh Muhammadu Gibrima, dake Nguru Yobe.

Allah ya jikan sa ya gafarta masa. Amiiiin

Daga: Muhyiddeen Fatihu

TARIHIN SHEIKH MODIBBO JAILANI YOLAAn haife shi garin Kafin Iya karamar hukumar Kirfi cikin jihar Bauchi a shekarar 1298...
14/12/2024

TARIHIN SHEIKH MODIBBO JAILANI YOLA

An haife shi garin Kafin Iya karamar hukumar Kirfi cikin jihar Bauchi a shekarar 1298 Hijira dai-dai 1903 miladiyya.

Mahaifin sa Malam Muhammad Modibbo, mahaifiyar sa Malama Fatima. Ya taso cikin kulawa da tarbiyya a mahaifa tun yana karami.

Tun yana shekara ashirin da uku (23) Sheikh Modibbo Jailani Yola ya wallafa Littafai da dama k**ar haka.

- Arumu Bila Dulil Mada
- Khaliphatil Khatamil Awliya'i Jarri
- Minka Nazzaratun Ala Gasul Baraya

Ya fara karatu a wurin mahaifin Malam Modibbo Muhammad, daga baya ya tura shi kasar Nafada wurin Malam Modibbo Garba Nafada da Alkali Abubakar a Gombe.

Yayi karatu a wurin manyan malaman Addinin Musulunci k**ar Sheikh Modibbo Muhammad limamin Bauchi, Sheikh Sani Zaria, Sarkin malaman Kano dake Mandawari da Sheikh Salga Malam Sani Abdulhamid Kano.

Sheikh Modibbo Jailani ya hidimtawa addinin Musulunci da yada darikar Tijaniyya a Arewacin maso gabashin Najeriya a harshen fulatanci tare da ilmantar da al'ummar musulmai.

Wasu daga cikin manyan almajiran sa Modibbo Hamma Adama Jada, Modibbo Muhammad Jawai, Modibbo Dahiru Ganye, Modibbo Muhammadu Jalingo, Modibbo Malam Ibrahim Daware, da sauran almajirai da dama.

Ya ziyarci garuruwa da kasashe da dama yana kuma cikin wanda s**a wakilci Najeriya a taron OIC zamanin shugaban kasa General Ibrahim Badamasi Babangida tare da wasu manyan malaman Nigeria.

Ya rasu yana da shekaru 82 a duniya, an masa makwanci a gidan sa kusa da Masallacin Juma'a dake garin Yola jihar Adamawa a arewa masu gabas a Nigeria.

Allah ubangiji madaukakin sarki ya jikan sa da rahma ya gafarta masa Allah ya bamu albarkan su. Amiin Yaa ALLAH

Babangida Alhaji Maina
Tijjaniyya Media News

Wani tsohon hoton Sheikh Muhammadu Gibrima dan Mallam Muhammadu Badagire Mutumin Dagira, dake karamar hukumar Nguru dake...
13/12/2024

Wani tsohon hoton Sheikh Muhammadu Gibrima dan Mallam Muhammadu Badagire Mutumin Dagira, dake karamar hukumar Nguru dake jihar jihar Yobe. Allah ya jikan iyayenmu da magabatan mu Allah ya kyautata karshen mu. Amiin Yaa ALLAH

FALALAR RANAR JUMA'A YAU 13/12/2024Ranar juma'a rana ce da Allah Madukakin Sarki ya kebe ta da wasu abubuwa na falala ak...
13/12/2024

FALALAR RANAR JUMA'A YAU 13/12/2024

Ranar juma'a rana ce da Allah Madukakin Sarki ya kebe ta da wasu abubuwa na falala akan ragowar kwanukan yini, ga su k**ar haka:

1- Juma'a rana ce da ta fi. dukkan rana ku Alkhairi da falala.

2- Rana ce da dukkan musulmi suke taruwa a guri daya domin yin wata babbar ibada.

3- Akwai wani lokaci a cikin ta wanda babu abinda zaka roki Allah Madukakin Sarki face sai ya amsa maka addu'ar ka.

4- Rana ce da Allah Madukakin Sarki ya ke gafartawa bayinsa zunubansu amma fa ga wanda ya kiyaye ladubban wannan rana mai alfarma.

5- Bayar da sadaka a wannan rana ya fi falala akan sauran ranaku.

6- Ranar idi ce ga dukkan musulmi.

7- Duk wanda ya mutu a wannan ranar to Allah Madukakin Sarki zai kare shi daga fitinar kabari.

Ya Allah ka Sadamu da Rahamarka Duniya da Lahira Albarkan ANNABI SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA Ameeeen.

Address

Pantami
Gombe
760242

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Fityanul Islam Of Nigeria posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Videos

Share