08/01/2025
AMFANIN DA DIWANIN SHEHU YAYI GA HALITTA. Daga: Gana Borno state
GABATARWA
Shi Diwani wani irin Littafi ne wanda ya ban banta da sauran Littafai da Shehu yayi, saboda Shehu yana gaya mana a Diwani na 4:
فإن مديحي للأمين طريقة # لإدراك فيض دونه كل سابق*
In kuma muka kula da yadda Shehu ya tsara Diwani ta wajen suna, zamuga konan ma ya ishi ya amfani duk wani mai neman Tsira.
Duk mutumin da yake neman saduwa da Hadaran Allah, sai Shehu ya tanadar mishi Diwani na Daya (1) wato:
تيسير الوصول إلي حضرة الرسول
Ma'ana SAUQAQE SADUWA ZUWA HADARAR MA'AIKI. (S,A,W)
Bayan mutum ya samu isa zai so ace yasamu abubuwan da suke tabbatar mar da Sirrika, sai Shehu ya bamu Diwani na Biyu (2) wato:
إكسير السعادات في مدح سيد السادات
Ma'ana SINADARIN ARZIQI A CIKIN YABON SHUGABA. (S,A,W)
In mutum ya samu haka, sai ya fara shiga hali da Damuwa akan abinda yake fuskanta daga masu adawa dashi, sai Shehu ya tanadar mar Diwani na Uku (3) wato:
سلوة الشجون
Ma'ana SINCE BAKKAN CIKI DA DAMUWA A YABON SHUGABA. (S,A,W)
Daga ya samu dauki daga Masoyinshi, sai ya fara neman inda zai rike yayi rinjaye kan Makiyanshi, sai Shehu ya tanadar mar da Diwani na Hudu (4) wato:
أوثق العري في مدح خير الورى
Ma'ana AMINCIN IGIYA CIKIN YABON FIYEYYEN TALIKAI. (S,A,W)
Sai Hadara ta amince dashi, tafara bashi wakilci, da nauyin Bayi, shi kuma sai ya fara shiga hali na Rashin lafiya da harara, sai Shehu ya tanadar mar da Diwani na Biyar (5) wato:
شفاء الأسقام في مدح خير الأنام
Ma'ana WARAKA DAGA CUTUTTUKA CIKIN YABON FIYAYYEN TALIKAI. (S,A,W)
Sai bawa ya samu waraka, sakamakon wannan Diwani da ya karanta, daga nan sai Hali na gaba cikin Soyayya da Amincewa da wanda ake so, sai ya fara neman ya zaiyi, sai Shehu ya tanadar mar da Diwani na Shida (6) wato:
مناسك أهل الوداد في خير العباد
Ma'ana AIKIN HAJIN MA'ABOTA SOYAYYA CIKIN YABON FIYAYYEN BAYI. (S,A,W)
Yanzu ya samu nutsuwa da komai yakeyi cikin Soyayya yakeyi, daga haka ta samu, sai Shehu ya tanadar mar Diwani na Bakwai (7) wato:
نور الحق في مدح الذي جاء بالصدق
Ma'ana HASKEN ALLAH CIKIN WANDA YAZO DA GASKIYA. (S,A,W)
Sai yayi Fana'i cikin Masoyin QAD AHBABTUHU HATTAA ARANIYA KUNTUHU # WA RABBIYA LAM YAKHULUQ MAKAANAN WALA WAQTA.
Daga nan sai Kamala, shi ne Shehu ya tanadar da
سير القلب
Kaga zuciya ta cika, Kamala kenan, wannan haka Shehu ya tsara Diwani ko ta suna ma ya wadatar.
Mustapha Kamkaye Nguru
Abba Ahlan Wa Sahlan
Idris Dahiru Idris
Abba Shuaibu Attijjaniy
Aliyu Dayyabu Daibah
Muhammad Harees Hamza Harazimi