Gombawa

Gombawa Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Gombawa, Media/News Company, JMG Plaza, opposite Immagration Office, Gombe.

Gombawa TV is a digital television platform that broadcasts a wide range of content, including news, entertainment, and cultural programs, with a focus on Northern Nigeria.

Zamu Sauya Filin Jirgin Sama Na Jihar Legos Ya Dawo Na Zamani, Inji GandujeShugaban kwamitin Daraktoci na Hukumar Kula d...
20/02/2025

Zamu Sauya Filin Jirgin Sama Na Jihar Legos Ya Dawo Na Zamani, Inji Ganduje

Shugaban kwamitin Daraktoci na Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama ta Ƙasa (FAAN), Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya jaddada bukatar gyara na gaggawa a filin jirgin sama na Murtala Muhammed (MMIA) saboda a cewar sa, ya fara zama tsohon yayi.

Daily Trust ta rawaito cewa a yayin ziyarar gani-da-ido ta farko da ya kai MMIA, tare da rakiyar Manajan Daraktan FAAN, Misis Olubunmi Kuku, Ganduje ya tabbatar da cewa yawancin kayan aikin filin jirgin saman sun tsifa wasu kuma sun lalace.

Ya kuma bai wa masu ruwa da tsaki tabbacin cewa kwamitin zai hada kai da hukumar ta FAAN domin gyara filin jirgin da zamanantar da shi ya yi daidai da yadda filayen jiragen sama su ke a faɗin duniya.

20/02/2025

YANZU-YANZU: Wasu Shaguna Sun K**a Da Wuta A Palluja Kusa Da Jimeta Modern Market Dake Jihar Adamawa

19/02/2025

RAHOTO: An bayyana muhimman cin sanya matasa wajen samar da tsaro a kasa, a yayin rantsar da jagororin kwamitin kyautata alaqa tsakanin al'umma da hukumar 'yan sanda a jihar Gombe.

Majalisa Ta Gayyaci Nuhu Ribadu Da Ya Gaggauta Hallara A Gabanta, Bisa Kan Zargin Da Ake Yiwa Hukumar USAID Da DIA, NIA
19/02/2025

Majalisa Ta Gayyaci Nuhu Ribadu Da Ya Gaggauta Hallara A Gabanta, Bisa Kan Zargin Da Ake Yiwa Hukumar USAID Da DIA, NIA

Karyewar Kayan Abinci "Riba ko Faɗuwa Ga Manoman Arewa?Daga Abubakar Shehu Dokoki Babban Burina da Addu'ata Shine Allah ...
19/02/2025

Karyewar Kayan Abinci "Riba ko Faɗuwa Ga Manoman Arewa?

Daga Abubakar Shehu Dokoki

Babban Burina da Addu'ata Shine Allah Yasa Gwamnatin Tinibu tafi ta Buhari zama Alkairi ga Talakawa, bana addu'ar kullum ace gwara gwamnatin baya, (Allah Yakiyaye).

Duk mutum mai tausayi da son cigaban Talaka zaiso kayan abinci yayi sauƙi, koba komai talakawa zasu samu sauƙi, kuma ayi rayuwa mai rangwame.

Amma ya dace mu duba ɓangaren Kayan talaka kaɗai? Ina nufin iya ɓangaren Kayan noma? Misali idan gwamnati tayi amfani da wasu dabaru wajen karya amfanin gona, kuma wanne mataki ta ɗauka wajen karya farashin man fetur? Da sauran kayan da ba talaka ne yake samar dasu ba?

Misali Talaka ya sayi Taki da tsada, kayan feshi da tsada, kuma ya noma ya sayar Araha alokacin da kuɗinsa ma bai dawo ba, shin kana ganin hakan shi zai samar da sauƙi? Idan Kayan talaka yana Araha kuma dala, da fetur suna tsada? Ni a Tunanina ya dace gwamnati ta samar da wasu hanyoyin da sauran kayan Noma zasu sauƙo, kuma su rage farashi, da haka za'a samu sauƙi sosai.

Yana da kyau gwamnati ta rage farashin man fetur, domin shi kaɗaine abinda kana taɓashi zai zagaya ko'ina, shi kaɗai ake taɓawa ya shafi kowanne talaka cikin ƙanƙanin lokaci komai nisan gurin da mutum yake.

Domin idan duk zamu tuna, da zarar gwamnati tace ta ƙara kuɗin nan fetur, shikenan k**ar An bawa ƴan ƙasa makamin azabtar da kansu, nan da nan zakaga anƙarawa komai kuɗi, k**a daga abinci, da tafiye-tafiye, da duk wani abu dayafi kusa da talaka. Kanayin magana za'a ce anƙara kuɗin man fetur.

Muna maraba da saukar kayan abinci, amma muna fatan za'a kawo hanyar da za'a rage kuɗin man fetur dakuma dala, domin da Hakane kowanne ɓangare zai samu rangwame.

Idan ba haka ba, ankashe macijine ba'a sare kansa ba.

DA ƊUMI-ƊUMI: Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, Ya Rushe Dukkanin Tsofaffin Hakimai Da Digacai Na JiharKo mey...
19/02/2025

DA ƊUMI-ƊUMI: Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, Ya Rushe Dukkanin Tsofaffin Hakimai Da Digacai Na Jihar

Ko meye zafi haka ?

Daga Muhammad Kwairi Waziri

19/02/2025

RAHOTO: Sanata mai wakiltar mazabar Gombe ta Arewa, Sanata Ibrahim Hassan Dankwambo, ya kaddamar da shirin bayar da magani da kula da marasa lafiya kyauta a asibitin kwararru na Jihar Gombe.

Ga rahoton Gombawa TV

TAIMAKON AL'UMMA: Wani bawan Allah yabada kyautar dubu dari biyar 500k domin tallafawa yara da kayan karatun yaran tare ...
19/02/2025

TAIMAKON AL'UMMA: Wani bawan Allah yabada kyautar dubu dari biyar 500k domin tallafawa yara da kayan karatun yaran tare da bada 200k don ciyar dasu.

Rabon Abincin ya gudana ne a ranar 17/2/25 da kuma 18/2/25 a makarantar Jakara Special Primary School da kuma Dala Special Primary School, inda aka raba musu kayan karatu, k**a daga littattafai, fensir, kilina, shafana da takalma.

Daga Sir Captain

WATA SABUWA: Yanzu A Kira Ka A Waya A Ce Daga Ofishin 'Yan Hisba Ne, An K**a Abokinka; Wane Abokinka Za Ka Fara Kawo Wa ...
19/02/2025

WATA SABUWA: Yanzu A Kira Ka A Waya A Ce Daga Ofishin 'Yan Hisba Ne, An K**a Abokinka; Wane Abokinka Za Ka Fara Kawo Wa A Ranka Cewa Shi Aka K**a?

Yi mana 'mentioning' dinsa a comment kawai ka fece.

TALLAH: Domin samun data mai inganci kuyi downloading application din "CAP DATA SUB" ga sauki ga rahusa ga kuma ƙarfin network.

https://play.google.com/store/apps/details?id=triplestack.capdatasub.com

Domin ƙarin bayani zaku iya tuntubar Customer care a WhatsApp ta wannan lambobin:

09027173561
09033297378

An k**a wani saurayi a makabarta yana tonon ƙwaranagwal na kayukan mutane a kudancin Najeriya.Inda ƴan jarida suke tamba...
18/02/2025

An k**a wani saurayi a makabarta yana tonon ƙwaranagwal na kayukan mutane a kudancin Najeriya.

Inda ƴan jarida suke tambayarshi me yake da wannan abun yace akwai masu kudi da ƴan siyasa da ke neman irin waɗannan abubuwan domin bunkasa arzikin su., amma anyi iya tambayarshi akan ya bada sunan wadanda suke sayen wannan abu yaki yace a hukuntashi iya shi kaɗai.

Allah ka mana kekkyawar ƙarshe Amin Summa Amin

Muhammad Sale......✍️

Ministan Tsaro Ya Kai Ziyarar Ban Kwana Ga Shugaba Tinubu a Addis AbabaMinistan Tsaro na Najeriya, Mai Girma Mohammed Ba...
18/02/2025

Ministan Tsaro Ya Kai Ziyarar Ban Kwana Ga Shugaba Tinubu a Addis Ababa

Ministan Tsaro na Najeriya, Mai Girma Mohammed Badaru Abubakar CON mni, a ranar Litinin 17/02/2025, ya kai ziyarar ban kwana ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu CGFR a birnin Addis Ababa na ƙasar Habasha, jim kaɗan kafin shugaban ya baro ƙasar zuwa Najeriya.

Shugaba Tinubu yana Habasha ne domin halartar taron koli na Ƙungiyar Tarayyar Afirka (AU) karo na 38, wanda aka gudanar a Addis Ababa.

SANARWA!!!Iyalan ALH. YA'U KUMO dana  ALH. MUSA YA'U na gayyatar yan uwa da abokan arziki zuwa shaida addu'ar daurin aur...
18/02/2025

SANARWA!!!

Iyalan ALH. YA'U KUMO dana ALH. MUSA YA'U na gayyatar yan uwa da abokan arziki zuwa shaida addu'ar daurin auren yayansu, Ango HON. DR. AUWAL YA'U KUMO (Kyauaren Gabas Akko) da Amaryarsa AMB. ZAINAB MUSA YA'U (Gimbiya/Giwar Matan Gona)

Date: 21st February, 2025
Time: 01:00 PM
Venue: Orji Quarters Jumma'at Mosque, Gombe

Allah yabada ikon halarta 🤲

Yadda Motocin Gomnatin Jihar Adamawa S**a Yi Jerin Gwano Yayin Tafiya Karamar Hukumar Madagali Domin Nadin Sabon Sarki
18/02/2025

Yadda Motocin Gomnatin Jihar Adamawa S**a Yi Jerin Gwano Yayin Tafiya Karamar Hukumar Madagali Domin Nadin Sabon Sarki

Ganduje ya k**a aiki a Sabon Ofishin da Shugaba Tinubu ya bashi.Shugaban rangadin kula jirgin saman tarayya na Najeriya,...
18/02/2025

Ganduje ya k**a aiki a Sabon Ofishin da Shugaba Tinubu ya bashi.

Shugaban rangadin kula jirgin saman tarayya na Najeriya, Dakta Abdullahi Umar Ganduje da Shugaba Tinubu ya nada ga Ma'aikatar jiragen sama (FAAN) ya ziyarci Ma'aikatar a karon farko tun bayan nadin nasa.

Shugabar Ma'aikatar Mrs. Olubunmi Kuku ta Tarbi shugaban kwamitin Ganduje ta kuma bashi cikakken taƙaitaccen jawabin tsarin ayyukan na hukumar.

18/02/2025

RAHOTO: Kungiyar 'yan jaridu ta shirya taron lifayar taya murna ga sabon shugaban kungiyar 'yan jaridun na Najeriya Comr. Alhassan Yahaya Abdullahi a jihar Gombe.

Ga cikakken rahoton daga GOMBAWA TV.

DA ƊUMI-ƊUMI: 'Yan Bîndígâ Sun Yi Garkuwa Da Ma’aikacin Asibitin Koyarwa Na Jami’ar Modibbo Adama Daga Muhammad Kwairi W...
18/02/2025

DA ƊUMI-ƊUMI: 'Yan Bîndígâ Sun Yi Garkuwa Da Ma’aikacin Asibitin Koyarwa Na Jami’ar Modibbo Adama

Daga Muhammad Kwairi Waziri


Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa, karkashin jagorancin CP Dankombo Morris, psc(+), ta yi kakkausar s**a ga wannan mummunan labarin 'yan ta'adda dauke da muggan mak**ai, da s**a yi garkuwa da mutane a kauyen Mayokila, gundumar Mapeo, a karamar hukumar Jada.

Da sanyin safiyar ranar 17 ga watan Fabrairun 2025, Inda wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne s**a abkawa al’umma, inda s**a yi ta harbe-harbe.

Zuwa yanzu sun yi awon gaba da da wani ma'aikaci Abubakar Sadiq Umar (a.k.a. Haske) dake aiki a asibitin koyarwa na Jami’ar Modibbo Adama Yola da wasu mutane uku.

Bayan samun kiran gaggawa kwamishinan ‘yan sandan ya tura jami’an rundunar domin dakile wannan harin da maharan s**a kawo.

A yayin da rundunar ta ke ba da tabbacin ta na ci gaba da kokarin kubutar da wadanda abin ya shafa ba tare da an samu rauni ba tare da gurfanar da wadanda s**a aikata laifin a gaban kotu.

Rundunar ta bukaci jama’a musamman mazauna karamar hukumar Jada da su hada kai da jami’an tsaro da aka tura domin tabbatar da an dawo da wadanda aka yi garkuwa da su lafiya.

Shugaban ‘yan sandan, ya bukaci al’umma da su kasance cikin shiri tare da kai rahoton duk wani abu da ya shafi ‘yan sanda.

Address

JMG Plaza, Opposite Immagration Office
Gombe
741212

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Gombawa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Gombawa:

Videos

Share