GMM News

GMM News Kasance Damu Don Samun Sahihan Labarai, Wasanni da Shirye Shirye.
(1)

Dubunsa Ta Cika Bayan Ya Ķàshè Buduŕwaŕsa A Abuja
14/01/2025

Dubunsa Ta Cika Bayan Ya Ķàshè Buduŕwaŕsa A Abuja

CIKIYA A TAYA MU YADAWA.Ana cikiyar iyayen wannan yarinya da aka tsinta a unguwar Bomala a cikin garin Gombe, Tace sunan...
13/01/2025

CIKIYA A TAYA MU YADAWA.

Ana cikiyar iyayen wannan yarinya da aka tsinta a unguwar Bomala a cikin garin Gombe, Tace sunan mahaifiyarta Sayyada Maryam.

Ana rikon duk Wanda Allah ya sa ya San iyayenta da ya sanar da su suje gidan mai Unguwar Bomala.

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya ƙaddamar da rabon tufafin makaranta ga ɗaliban makarantun firamare dubu 789 a yau a gi...
13/01/2025

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya ƙaddamar da rabon tufafin makaranta ga ɗaliban makarantun firamare dubu 789 a yau a gidan gwamnati.

KAIDIN MATA: Budurwarta Ta Cinye Min Kudi Sama Da Naira Milyan 3.5, Kuma Daga Karshe Ta Ce Ba Ta Sona, Cewar AbdullahiMa...
13/01/2025

KAIDIN MATA: Budurwarta Ta Cinye Min Kudi Sama Da Naira Milyan 3.5, Kuma Daga Karshe Ta Ce Ba Ta Sona, Cewar Abdullahi

Matashin ya bayyana hakan ne a cikin shirin Rayuwata da Tubless Media Concept suke gabatarwa.

Me za ku ce?

Mutune 16, ciki har da ƴan bijilanti sun mutu a harin sama na soji a ZamfaraAkalla mutane16 ake fargabar sun rasa rayuka...
12/01/2025

Mutune 16, ciki har da ƴan bijilanti sun mutu a harin sama na soji a Zamfara

Akalla mutane16 ake fargabar sun rasa rayukansu bayan wani harin sama da sojoji s**a kai a garin Tungar Kara, karamar hukumar Maradun ta jihar Zamfara.

Jaridar TheCable ta samo rahoto daga Zagazola Mak**a, wani masani mai kawo rahotanni kan yaki da ta'addanci a yankin tafkin Chadi, cewa majiyoyin sirri sun bayyana cewa wadanda abin ya shafa sun hada da mambobin Kungiyar Tsaro ta Al’umma ta Zamfara (ZCPG), ƴan sa kai, da mazauna yankin da aka kira don tunkarar harin da ‘yan bindiga s**a kai.

“Sojojin sun zaci ƴan bijilanti din su ne yan bindigars, bayan yan bindigan sun tsere daga wurin,” in ji rahoton.

“a halin yanzu an gano gawarwaki 16, amma adadin wadanda s**a mutu baki daya bai bayyana ba.”

Olusola Akinboyewa, daraktan hulda da jama’a da labarai na hedkwatar Sojojin Sama na Najeriya (NAF), bai maida martani kan tambayoyin TheCable game da lamarin ba.

Shugaban jam'iyyar SDP na ƙasa ya baiyana abinda aka tattauna a ganawar sa da El-Rufai Shugaban jam’iyyar SDP na kasa, S...
12/01/2025

Shugaban jam'iyyar SDP na ƙasa ya baiyana abinda aka tattauna a ganawar sa da El-Rufai

Shugaban jam’iyyar SDP na kasa, Shehu Gabam, ya bayyana sak**akon ganawarsa da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai da wasu manyan shugabannin siy

A yayin wata hira da aka yi da shi a gidan Talabijin na Channels, Gabam ya ce sun yi ganawar ne don tattauna halin da kasar ta tsinci kanta a 2024.

Ya kuma ce jam’iyyar ba ta yi wani laifi ba wajen tattaunawa da El-Rufai, wanda dan jam’iyyar APC ne.

Ya ce: “Mun yi ganawar domin duba ga halin da Nijeriya ta tsinci kan ta a 2024 a matsayin jam’iyya. Mu jam’iyyar adawa ce mai zababbun ‘yan majalisa, majalisun jihohi, da kananan hukumomi.

"Me ya sa hakan zai tada kura akan Malam Nasir El-Rufai? Sun ce ba shi da mahimmanci, ba kome ba ne. Me yasa El-Rufai ya dame su? Me yasa ake damuwa da Segun Sowunmi? Idan suna da mahimmanci, me ya sa gwamnati ba za ta ba su muƙamai da s**a dace da su don inganta aikin gwamnati ba?, ”in ji shi.

Lakurawa sun yi ajalin jami‘ai a wajen sanya   turken sabis a jihar KebbiLamarin ya faru a kauyen Gumki da ke karamar hu...
12/01/2025

Lakurawa sun yi ajalin jami‘ai a wajen sanya turken sabis a jihar Kebbi

Lamarin ya faru a kauyen Gumki da ke karamar hukumar Arewa. Wasu na cewa ma‘aikatan kamfanin airtel ne s**a rasa rayukansu yayin da wasu ke cewa jami‘an hukumar Immigration ne, a cewar jaridar Daily Trust

Na kwashe shekaru ashirin ina fim a Amurka amma har yanzu a talauce na ke - Djimon HounsouShahararren jarumin Hollywood ...
11/01/2025

Na kwashe shekaru ashirin ina fim a Amurka amma har yanzu a talauce na ke - Djimon Hounsou

Shahararren jarumin Hollywood din nan Djimon Hounsou ya bayyana cewa ya na ci gaba da fuskantar matsin tattalin arziki duk da sana'ar fim da ya ke yi sama da shekaru ashirin.

A wata hira da CNN a wani shirin su na matasan Afirka, a yau Asabar, Hounsou ya bayyana cewa ya na ganin cewa ana yi masa ƙwange a albashi kuma har yanzu ya na fama da talauci.

"Har yanzu ina fama yanayi a rayuwa. Na kasance cikin harkar shirya fina-finai sama da shekaru ashirin, tare da lashe lambobin girma na Oscar guda biyu da fina-finai da yawa, amma duk da haka, har yanzu ina fama da rashin kuɗi. Babu shakka ƙwangen albashi ake yi min," inji shi.

Wannan tonon silili ya ba wa mutane da yawa mamaki, ganin irin nasarorin da ya samu, gami da lashe lambar yabo ta Academy sak**akon kwazon saba fim din 'Blood Diamond' da 'In America'.

Karuwanci na ƙaruwa tsakanin tsofaffin k**ammun Boko Haram - Kwamishina Lawan Wakilbe, kwamishinan ilimi, da kimiyya da ...
11/01/2025

Karuwanci na ƙaruwa tsakanin tsofaffin k**ammun Boko Haram - Kwamishina

Lawan Wakilbe, kwamishinan ilimi, da kimiyya da fasaha, da kirkire-kirkire a Jihar Borno, ya yi gargadi kan yawaitar karuwanci tsakanin tsofaffin wadanda kungiyar Boko Haram ta sace.

TheCable ta rawaito cewa Kwamishinan ya bayyana hakan ne yayin wata ziyarar ban girma da Hamsatu Allamin, shugabar cibiyar Allamin Foundation for Peace, ta kai masa a jiya Juma’a a Maiduguri.

Wakilbe ya ce an fi samun irin waɗannan matsalolin a ƙananan hukumomin Bama, Banki, da Gwoza.

Ya kara da cewa wasu daga cikin wadanda Boko Haram din su ka saki na fuskantar cin zarafi ta hanyar lalata da su saboda sun fuskanci hakan tun a lokacin da raunin da su ke hannun ƴan ta’addan.

Ya yi kira ga haɗa hannu waje ɗaya domin ceto ire-iren yaran.

Hukumar zabe a Nijeriya INEC na bukatar kashe sama da Naira biliyan 126 a shekarar 2025
11/01/2025

Hukumar zabe a Nijeriya INEC na bukatar kashe sama da Naira biliyan 126 a shekarar 2025

11/01/2025
Jami’an Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta’annati (EFCC) sun k**a mutane 105 da s**a haɗa da ƴan ƙasar China...
11/01/2025

Jami’an Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta’annati (EFCC) sun k**a mutane 105 da s**a haɗa da ƴan ƙasar China huɗu a wata harabar kasuwanci da ke unguwar Gudu a Abuja.

Shugaban sashen yaɗa labarai na EFCC, Dele Oyewale, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a.

Yace “A ci gaba da ƙoƙarin da take yi na tsaftace al’ummar ƙasar daga damfarar intanet da sauran ayyukan cin hanci da rashawa, jami’an Hukumar Yaƙi da Masu yi wa Tattalin Arzikin Ƙasa Zagon Ƙasa, (EFCC) sun k**a wasu ƴan China huɗu da ƴan Najeriya 101 a wata harabar kasuwanci da ke unguwar Gudu a Abuja, cewar Hukumar.

Oyewale ya ce, an k**a waɗanda ake zargin ne a ranar Alhamis, 9 ga watan Janairu 2025 inda ya ce sun haɗa da maza 67 tare da ƴan ƙasar China da ake zargi da kuma mata 38.

Asusun kula da ƙananan yara na majalisar ɗinkin duniya UNICEF ya ce akwai ƙananan yara akalla miliyan 3 da ke fama fama ...
10/01/2025

Asusun kula da ƙananan yara na majalisar ɗinkin duniya UNICEF ya ce akwai ƙananan yara akalla miliyan 3 da ke fama fama da matsananciyar yunwa a Sudan saboda yadda yaki ya ɗaiɗaitata.

Khalifa Aminu, fasihin yaron nan dan jihar Kano mai ƙere-ƙere, ya ƙirƙiri wata sabuwar na'ura mai nuna yanayin jini da j...
10/01/2025

Khalifa Aminu, fasihin yaron nan dan jihar Kano mai ƙere-ƙere, ya ƙirƙiri wata sabuwar na'ura mai nuna yanayin jini da jikin ɗan adam.

Ga bayanin na'urar nan da ya wallafa a shafin sa na Facebook.

" Wannan shine sabon 'project' dina mai ban mamaki da ban al ajabi wato 'Scan blood🩸& temperature🌡️device'.

"Wato na'urar mai gano bugun jini da yanayin jiki. Wannan na'urar za ta iya temaka wa mutane da dama wajan kare lafiyar jikinsu.

"Ita dai wannan na'urar ana saka ta a hannu ne. Bayan ka saka ta a hannu to duk inda ka shiga idan zafi yai yawa a wajen ko sanyi ko yanayin iskar da ka ke shaƙa to za tayi scaning din jikin ka ta ga yanayin 'temperature' din da jikin ka ya ke bukata idan wannan yanayin iskar ko zafi ko sanyi su kai yawa nan take za ta sanar da kai kabar wajen idan ba haka ba zaka iya cutuwa.

"Sannan za ka iya scan din jinin jikin ka don ka ga lafiyar ka kalau ko ba ka da lafiya.

" Wannan ba karamar fasaha ba ce wajen kula da lafiyar mu....."

"by khalifa Aminu
Kuyi share din sa da post don bunkasa abun."

An naɗa sabon kocin Super Eagles Kwamitin Zartaswa na Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Ƙasa (NFF) ya amince da nadin Éric Sékou C...
07/01/2025

An naɗa sabon kocin Super Eagles

Kwamitin Zartaswa na Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Ƙasa (NFF) ya amince da nadin Éric Sékou Chelle a matsayin sabon kocin tawogar ƙwallon ƙafa ta maza ta Najeriya, wato Super Eagles.

Matakin ya biyo bayan shawarar kwamitin fasaha da ci gaba na NFF ne a yayin taron da ya gudanar a Abuja a ranar 2 ga Janairu, 2025.

Daily Trust ta rawaito cewa daga bisani sai kwamitin zartarwa na NFF ya amince da nadin a ranar 7 ga Janairu, 2025.

Chelle, mai shekaru 47, tsohon babban koci ne na babbar kungiyar kwallon kafa ta Mali, kuma yana da kwarewa sosai, inda ya jagoranci kungiyoyi irin su GS Consolat, FC Martigues, Boulogne, da MC Oran.

A T**i Muke Kwana Ni Da Mahaifiyata Saboda Otal Din Da Muke Kwana Kudinmu Ya Kare Har An Kwace Mana Jakunkunanmu Saboda ...
07/01/2025

A T**i Muke Kwana Ni Da Mahaifiyata Saboda Otal Din Da Muke Kwana Kudinmu Ya Kare Har An Kwace Mana Jakunkunanmu Saboda Suna Bin Mu Ba Shi, Inji Iyalan Marigayi Tsohon Sarkin Kano, Marigayi Ado Bayero

Ko a kwanakin baya dai Zainab ta koka kan yadda iyalan marigayi tsohon Sarkin s**a yi watsi da ita da mahaifiyarta duk da cewa mahaifina nata ya ce su kula da ita da mahaifiyarta ko bayan ransa.

Me za ku ce?

Shugaba Tinubu ya yi ido da ido da Obasanjo a wajen rantsar da sabon shugaban kasar Ghana
07/01/2025

Shugaba Tinubu ya yi ido da ido da Obasanjo a wajen rantsar da sabon shugaban kasar Ghana

Za mu fitar da Afirka da ga talauci, in ji Tinubu Shugaba Bola Tinubu, a yau Talata ya ce shugabannin Afirka za su ci ga...
07/01/2025

Za mu fitar da Afirka da ga talauci, in ji Tinubu

Shugaba Bola Tinubu, a yau Talata ya ce shugabannin Afirka za su ci gaba da jajircewa wajen fitar da al’ummarsu daga kangin talauci da gina tattalin arzikinsu a matakan da su ka dace.

Tinubu, wanda ya kasance babban bako na musamman, ya bayyana haka ne a wajen rantsar da shugaba John Mahama a birnin Accra na kasar Ghana.

“Ba mu da wani abin da za mu tabbatar wa kowa sai kanmu. Mun sami hanya mai mahimmanci don samun nasarar mu. Za mu fitar da al'ummarmu daga kangin talauci, mu gina tattalin arziki mai dorewa a kan kan mu.

"A yau, na zo nan ba kawai a matsayina na shugaban Najeriya ba, har ma a matsayina na dan Afirka mai cikakken goyon baya ga Ghana da mutanenta," in ji Tinubu

Address

Tumfure
Gombe

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when GMM News posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Videos

Share