Daily News Hausa

Daily News Hausa Daily News Hausa, is a licensed Nigerian newspaper company dedicated to delivering verified news and entertainment content in the Hausa language."
(1)

WATA SABUWA: Bayan Auren Rarara da A'isha Humaira, Tini aka fara kiraye-kirayen Nasir da Stephanie, jaruman da su ke fit...
01/05/2025

WATA SABUWA: Bayan Auren Rarara da A'isha Humaira, Tini aka fara kiraye-kirayen Nasir da Stephanie, jaruman da su ke fitowa a matsayin miji da mata a fim ɗin nan mai dogon zango, Dadin Kowa, cewa su ma su Auri junan su.

Mezakuce?

TINUBU: Ma’aikata Su ne Garkuwar Tattalin Arzikin NijeriyaShugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa gwamnatin sa z...
01/05/2025

TINUBU: Ma’aikata Su ne Garkuwar Tattalin Arzikin Nijeriya

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da ɗaukar walwalar ma’aikata a matsayin ginshiƙin ci gaban ƙasa.

A cikin sakonsa na ranar Ma’aikata, wanda aka wallafa a shafinsa na X (tsohon Twitter) a yau Alhamis, Tinubu ya yaba da gudummawar da ma’aikata ke bayarwa wajen gina ƙasa, yana mai bayyana su a matsayin “injin tattalin arzikinmu da sirrin cigabanmu.”

“Ko kai matashi ne, ko babba, ko dan kasuwa, ko ma’aikacin gwamnati, gudummawar ka tana da muhimmanci wajen bunƙasar ƙasa – daga cikin gida, unguwa har zuwa matakin ƙasa baki ɗaya,” in ji Shugaban.

Tinubu ya jaddada cewa walwalar ma’aikata za ta ci gaba da kasancewa cikin abubuwan da gwamnatin sa ke baiwa muhimmanci, tare da ƙudurin gyara Nijeriya cikin haɗin kai da jajircewa.

Kotu Ce Kaɗai Za Ta Yanke Hukunci Kan Karata da Akpabio - Natasha Akpoti-UduaghanSanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta mayar...
01/05/2025

Kotu Ce Kaɗai Za Ta Yanke Hukunci Kan Karata da Akpabio - Natasha Akpoti-Uduaghan

Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta mayar da martani ga lauyan Sanata Godswill Akpabio, Olisa Agbakoba (SAN), wanda ya bukaci ta janye zargin cin zarafi da ta yi wa shugaban majalisar dattawa. A cikin wata wasika da ta fitar a ranar 30 ga Afrilu, 2025, Natasha ta bayyana cewa ba ta karɓi wata wasika daga Agbakoba ba, kuma ta jaddada cewa kotu ce kaɗai ke da ikon yanke hukunci kan lamarin.

Ta bayyana cewa akwai shari'o'i guda biyu da ke gudana a kotu: ɗaya da ta shigar a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja (FHC/ABJ/CS/384/2025) kan dakatar da ita daga majalisar dattawa, da kuma wani da matar Akpabio ta shigar a Babbar Kotun FCT (CV/816/2025) tana neman diyyar Naira biliyan 250 kan zargin bata suna.

Natasha ta zargi Akpabio da rashin adalci wajen jagorantar zaman da ya kai ga dakatar da ita, tana mai cewa hakan ya sabawa ka'idar "nemo judex in causa sua" wato ba wanda ya k**ata ya zama alkalin shari'ar da ya shafi kansa. Ta kuma bayyana cewa Agbakoba ba shi da ikon doka na buƙatar hujjoji daga gare ta a wajen kotu.

Ma'aikatan Makarantu a Jihar Oyo Sun Tsunduma Yajin Aiki Saboda Rashin Sabon Albashi  Ma'aikatan manyan makarantu mallak...
01/05/2025

Ma'aikatan Makarantu a Jihar Oyo Sun Tsunduma Yajin Aiki Saboda Rashin Sabon Albashi

Ma'aikatan manyan makarantu mallakar gwamnatin Jihar Oyo sun fara yajin aiki na sai baba-ta-dace daga ranar 10 ga Maris, 2025, saboda rashin aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi da kuma ƙarin albashi na kashi 25 zuwa 35 cikin ɗari da aka amince da shi tun Janairu 2024. Wannan yajin aikin ya shafi jami'o'i guda biyar da s**a haɗa da The Polytechnic, Ibadan; The Oke-Ogun Polytechnic, Saki; Adeseun Ogundoyin Polytechnic, Eruwa; Oyo State College of Agriculture and Technology, Igboora; da Oyo State College of Education, Lanlate.

Ƙungiyar haɗin gwiwa ta ma'aikatan manyan makarantu (JAC) ta bayyana cewa duk da ƙoƙarin da s**a yi na tattaunawa da hukumomin makarantu da kuma wakilan gwamnati, ba a samu ci gaba ba wajen aiwatar da sabon tsarin albashi. Sun kuma nuna damuwa kan yadda wasu makarantu k**ar Ladoke Akintola University of Technology (LAUTECH) da Emmanuel Alayande University of Education s**a riga sun fara aiwatar da sabon tsarin albashi, yayin da su ke ci gaba da fuskantar ƙalubale.

Shugaba Tinubu Zai Ziyarci Jahar Katsina Ranar Juma'aA gobe  Juma’a ne shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai bar Abuja zuw...
01/05/2025

Shugaba Tinubu Zai Ziyarci Jahar Katsina Ranar Juma'a

A gobe Juma’a ne shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai bar Abuja zuwa jihar Katsina domin ziyarar aiki ta kwanaki biyu.

A yayin ziyarar shugaban kasar zai gana da masu ruwa da tsaki domin duba yanayin tsaro a jihar.

Kazalika, shugaban zai ƙaddamar da cibiyar injinan noma ta Katsina da kuma titin mota mai nisan kilomita 24 wanda Gwamna Dikko Umar Raɗɗa ya kammala.

Shugaba Tinubu zai kuma halarci gayyatar ɗaurin auren ɗiyar gwamna Raɗɗa kafin dawowa Babban Birnin Tarayya Abuja.

Aikin Gina Tashar Jirgin Ƙasa A Kano Yana Ci Gaba Gadan-gadanAikin gina tashar jirgin ƙasa ta zamani a Kano, ɗaya daga c...
01/05/2025

Aikin Gina Tashar Jirgin Ƙasa A Kano Yana Ci Gaba Gadan-gadan

Aikin gina tashar jirgin ƙasa ta zamani a Kano, ɗaya daga cikin manyan ayyukan gwamnatin Bola Ahmed Tinubu, yana ci gaba da tafiya babu k**a hannun yaro.

Kamfanin da ke gina tashar, wato CCECC na ƙasar Chana, ya bayyana a yau cewa a yanzu haka an kusa kammala tsawon ginin tashar.

Kamfanin ya ce yana sa ran kammala aikin tsawon ginin a farkon wannan watan na Mayu.

Faɗin ginin, wanda ya haura sukwaya mita 13,000, ya ƙunshi babban ginin tashar da ababen da ke tattare da shi, kuma zai kasance tashar da ta fi kowace girma a layin dogon da ake kira Kaka Reluwe.

Kaka Reluwe na nufin hanyar dogo daga KAduna zuwa KAno.

Kamfanin CCECC ya ce idan an gama aikin, zai taimaka gaya wajen haɓaka harkokin sufuri kuma ya kawo matuƙar sauƙi ga miliyoyin matafiya a ɓangaren Kano na hanyar jirgin.

Shi dai wannan layin dogo na Kaka Reluwe, hanya ce mai tsawon kilomita 204. Ta tashi daga Kaduna, ta bi ta Zariya, zuwa Kano.

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ne ya ƙaddamar da ita a ranar 15 ga Yuli, 2021, sannan gwamnatin Bola Ahmed Tinubu tana ci gaba da aikin babu ƙaƙƙautawa don tabbatar da ta kammala ta a kan lokaci.

📸 : CCECC Nigeria

Atiku Ya Bukaci Gwamnati Ta Girmama Ma'aikata a Matsayin Abokan Huldar Cigaba Kasa.A cikin saƙon bikin Ranar Ma’aikata t...
01/05/2025

Atiku Ya Bukaci Gwamnati Ta Girmama Ma'aikata a Matsayin Abokan Huldar Cigaba Kasa.

A cikin saƙon bikin Ranar Ma’aikata ta shekarar 2025, tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya jaddada muhimmancin ma’aikata wajen ciyar da ƙasa gaba. Ya bukaci gwamnatin tarayya da ta daina kallon ma’aikata a matsayin kayan aiki kawai, sai dai ta ɗauke su a matsayin abokan huldar ci gaban ƙasa.

Atiku ya bayyana cewa, duk da matsin rayuwa da ƙarancin albashi, ma’aikatan Najeriya suna ci gaba da ɗaukar nauyin burin tattalin arzikin ƙasa da jarumta. Ya bayyana damuwarsa kan yadda masu mulki s**a kasa mayar da martani mai ma’ana ga wannan sadaukarwa.

Ya kuma bayyana ma’aikata a matsayin “Zuciyar ƙasa,” yana mai kira ga masu tsara manufofi da su samar da tsare-tsare masu ƙarfi don kare mutuncin ma’aikata, walwala, da haƙƙoƙinsu. YaKuma ƙarfafa buƙatar haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da ma’aikata don gina al’umma mai Gaskiya da manufar ci gaba.

Akpabio Ya Musanta Zargin magudin Zaɓen da  a ke masa a 2019Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya kary...
01/05/2025

Akpabio Ya Musanta Zargin magudin Zaɓen da a ke masa a 2019

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya karyata zargin cewa ya amfana da magudin zaɓe da tsohon jami’in INEC, Farfesa Peter Ogban, ya aikata a zaɓen 2019.

A cewarsa, shi ne ya fi fuskantar Magudi Saboda, Lokacin an soke masa ƙuri'unsa sama da 61,000 a mazabarsa ta Essien Udim. Ya ce kotunan zaɓe sun tabbatar da hakan tare da umartar a sake zaɓe a yankin, don haka hukuncin da aka yanke wa Ogban yababbar da bashi yayi magudi ba, illa shi ne ma wanda aka zalunta.

CIKIN HOTUNA 📸: Gwamna Abba Kabir Yusuf da Mataimakinsa Sun Halarci Taron Ranar Ma’aikata a KanoGwamnan Jihar Kano, Abba...
01/05/2025

CIKIN HOTUNA 📸: Gwamna Abba Kabir Yusuf da Mataimakinsa Sun Halarci Taron Ranar Ma’aikata a Kano

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, tare da mataimakinsa, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, sun samu halarta a bikin ranar ma’aikata da ake gudanarwa a filin wasa na Sani Abacha, Kofar Mata, Kano.

Taron ya haɗa manyan jami'an gwamnati da ma’aikata daban-daban domin murnar wannan rana ta musamman.

Dalibar Firamare Ta Zama Shugabar Riko Na Karamar Hukumar Toro Na Tsawon Minti 30A ranar 1 ga Mayu, 2025, wata ƙaramar d...
01/05/2025

Dalibar Firamare Ta Zama Shugabar Riko Na Karamar Hukumar Toro Na Tsawon Minti 30

A ranar 1 ga Mayu, 2025, wata ƙaramar daliba mai suna Balkisu Aliyu Sale daga makarantar firamare ta gwamnati a Tilden Fulani ta rike mukamin Shugabar Karamar Hukumar Toro na riko na tsawon mintuna 30. Wannan dama ta samuwa ne bayan ta lashe gasar muhawara a bikin Ranar Ruwa ta Duniya da Gwamnatin Jihar Bauchi tare da haɗin gwiwar Ma’aikatar Ruwa s**a shirya.

A lokacin da take rike da mukamin, Balkisu ta sanya hannu kan kudurin gina rijiyar burtsatse a unguwarsu ta Kasa Tilden Fulani domin sauƙaƙa matsalar samun ruwa mai tsafta.

Shugaban karamar hukumar, Pharmacist Ibrahim Abubakar Dembo, ya yaba da wannan nasara, yana mai cewa Balkisu ta kasance abin alfahari da ƙarfafa gwiwa ga sauran yara mata. Ya kuma bai wa malamai da dalibai kyautar naira 100,000 a matsayin girmamawa da ƙarfafawa.

📸 Labari Daga Bauchi

NDM Ta Yi Watsi da Kiran AYCF na Ayya­na Dokar Ta-Baci a Zamfara, Ta Ce Barazana Ce Ga DimokuraɗiyyaA ranar 1 ga Mayu 20...
01/05/2025

NDM Ta Yi Watsi da Kiran AYCF na Ayya­na Dokar Ta-Baci a Zamfara, Ta Ce Barazana Ce Ga Dimokuraɗiyya

A ranar 1 ga Mayu 2025, Kungiyar National Democratic Movement (NDM) ta yi watsi da kiran da kungiyar Arewa Youth Consultative Forum (AYCF) ta yi na a ayyana dokar ta-baci a Jihar Zamfara, tana mai bayyana cewa hakan barazana ce ga tsarin dimokuradiyya.

NDM ta bayyana cewa kiran na AYCF yana da tushe na siyasa kuma ba ya da wata hujja ta doka, tana mai jaddada cewa ayyana dokar ta-baci a Zamfara zai saba wa kundin tsarin mulki na 1999, musamman sassan 188 da 305.

Kungiyar ta kuma bayyana cewa akwai ci gaba a fannin tsaro a jihar karkashin jagorancin Gwamna Dauda Lawal, tare da yabawa kokarin Shugaba Bola Tinubu da rundunonin tsaro wajen dawo da zaman lafiya a yankin.

NDM ta yi kira ga Shugaba Tinubu da ya yi watsi da kiran na AYCF, tana mai cewa irin wannan mataki zai iya haifar da rikici da kuma tabarbarewar tsarin dimokuradiyya a jihar.

A karshe, kungiyar ta bukaci 'yan siyasa da su daina amfani da matsalolin tsaro don cimma muradun siyasa, tare da jaddada bukatar hadin kai da zaman lafiya a jihar Zamfara.

ALLAHU AKBAR: Madam Joy da 'Ya'yanta Biyu Sun Karɓi Addinin Musulunci a Fadar Sarkin Rano
01/05/2025

ALLAHU AKBAR: Madam Joy da 'Ya'yanta Biyu Sun Karɓi Addinin Musulunci a Fadar Sarkin Rano

Lokaci Ya Yi da Za a Inganta Walwalar Ma'aikata - Abbas TajudeenA ranar 1 ga Mayu 2025, kakakin majalisar wakilai ta tar...
01/05/2025

Lokaci Ya Yi da Za a Inganta Walwalar Ma'aikata - Abbas Tajudeen

A ranar 1 ga Mayu 2025, kakakin majalisar wakilai ta tarayya, Rt. Hon. Abbas Tajudeen, ya bayyana cewa ma'aikatan Najeriya sun cancanci kyakkyawan kulawa da walwala, yana mai kira ga gwamnati da ta dauki matakan inganta rayuwar ma'aikata.

A yayin bikin ranar Ma'aikata (May Day), Abbas ya jaddada cewa lokaci ya yi da za a aiwatar da manufofi masu inganci da za su tabbatar da jin dadin ma'aikata, ciki har da:

- Sabunta albashin ma'aikata daidai da halin tattalin arziki.

- Aiwatar da tallafin rage radadin rayuwa da aka sanar a watan Yuli 2023.

- Samar da tsare-tsaren rage hauhawar farashin abinci da kayayyakin more rayuwa.

- Kaddamar da shirin samar da motocin sufuri na CNG don saukaka zirga-zirga.

- Bayar da tallafi ga kananan masana'antu da masu farawa kasuwanci (MSMEs) don bunkasa ayyukan yi.

Abbas ya kuma bukaci gwamnati da ta tabbatar da cewa ma'aikata suna samun albashi mai kyau da zai ba su damar rayuwa mai inganci tare da iyalansu.

A karshe, ya yi fatan cewa gwamnati za ta dauki wadannan matakai cikin gaggawa domin tabbatar da jin dadin ma'aikata a fadin kasar.

Matukar munnirat abdussalm ta shirya yin aure to tazo mu daidaita kawai in aureta in kawota Medile.Wani matashi mai suna...
01/05/2025

Matukar munnirat abdussalm ta shirya yin aure to tazo mu daidaita kawai in aureta in kawota Medile.

Wani matashi mai suna Musa Rafinkuka ya bayyana sha'awarsa ta auren Munnirat Abdussalm, inda ya nuna cewa yana da niyyar gina rayuwar aure mai cike da kulawa da soyayya.

Awani Sakon da ya Wallafa a shafin Sada Zumunta , Musa ya ce, "Matukar Munnirat Abdussalm ta shirya yin aure, to tazo mu daidaita kawai in aureta in kawota Medile."

Musa, wanda ya bayyana cewa yana da shekaru kusan talatin, ya kara da cewa yana da burin auren mace da ta girme shi. Ya ce, "Zan ba ta kulawa, in ciyar da ita shinkafa da wake, yogurt, kifi da maltina."

Ya kuma bayyana cewa yana fatan su rufawa juna asiri tare da yin jihadi na soyayya.

Wannan furuci na Musa ya jawo hankalin jama'a a shafukan sada zumunta, inda mutane da dama ke bayyana ra'ayoyinsu game da irin wannan soyayya mai cike da nishaɗi da barkwanci.

Amma kuna ganin Gaskiya yake zai kuma Aurenta?

Address

Gombe
7979101

Telephone

+2348149675978

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Daily News Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Daily News Hausa:

Share