04/09/2024
Ku karanta abinda yace dan Allah!
SHUGABA TINUBU SHUGABA NE MAI TAUSAYIN TALAKA YANA ƘOƘARIN GANIN AN SAMU SAUƘI, -ABDULAZIZ ABDULAZIZ
Mataimaki na musamman ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan harkokin sadarwa, Malam Abdulaziz Abdulaziz ya tabbatarwa ƴan Najeriya cewa Shugaban ƙasa yana sane da halin ƙunci da suke ciki, kuma yana ƙoƙarin ganin an samu sauƙi.
Jaridar Dokin Ƙarfe TV ta ruwaito Malam Abdulaziz ɗin na bayyana haka ta cikin wata hira da ya gabatar a sashen Hausa na Rediyoj Faransa. "Ƙasar ce tun asali an gina ta a kan tubalin toka, Allah Ya sani, tun kafin na shiga gwamnati na sha faɗar cewa muna zaman ƙarya a Najeriya saboda kusan komai da muke amfani da shi a ƙasar k**ar man fetur, ilimi da wutar lantarki ana ba da tallafi a kai wanda lamarin kuma ba haka yake ba a ƙasashen Duniya da s**a cigaba". Ya ce.
Malam Abdulaziz ya ƙara da cewa hatta ƙasar Saudiyya da take sahun gaba ta fuskar ƙarfin tattalin arziƙin mai a Duniya ba ta ba da tallafin man fetur, kuma mai yana da tsada sosai a ƙasar fiye da a Najeriya. "Hatta a nan Afrika, duk ƙasashen da ke kewaye da mu irin su Chadi, Togo, Kamaru, da sauransu ba inda suke saida mai ƙasa da Naira 1,300". Ya ƙara da cewa.
Ya cigaba da cewa "Tun asali mun shagaɓa ne da yawa, shi isa idan muka ce za mu yi tsare-tsare irin na ƙasashen Duniya da s**a cigaba sai mutane su ji ba daɗi. Hatta haraji ba ma biya a Najeriya wanda kuma abin ba haka yake ba a ƙasashen Duniyar da ake kallo ake haɗa kai da su". In ji shi.
Malam Abdulaziz ya ƙara da cewa gwamnati tana da kykkyawan fata na cire tallafin man fetur. "Kuɗaɗen za su yi amfani a wasu fannoni na kyautata rayuwar ƴan Najeriya k**ar irin wannan tsari na ba wa ɗalibai tallafin rancen kuɗaɗen karatu (NELFUND) da sauran fannoni na gina rayuwar al'umma waɗanda sun fi tasiri fiye da man da za ka ƙona zuwa gobe ka manta".