GANYE 24

GANYE 24 Jaridar GANYE 24 Naku Mai Albarka Domin Kawo Maku Sahihan Labarai Da ɗumi-ɗumin Su (Breaking News).
(5)

03/12/2024

Tsohon Mataimakin Shugaban kasa Alh Atiku Abubakar ya halarci wasan karshe (Final) na wasan kwallon Kafa da aka shirya a karamar hukumar Ganye jihar Adamawa domin sada zumunci (Unity Cup) a makon zagayowar ranar haihuwarsa.

03/12/2024

Dokar Haraji: Gwamnonin Arewa ba adawa su ke da Tinubu ba, in ji Gwamna Zulum

Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya musanta rade-radin cewa gwamnonin Arewa suna adawa da Shugaba Bola Tinubu saboda manufofin sauya tsarin haraji da ya gabatar gaban Majalisar Dokoki ta Ƙasa.

Yayin wata hira da aka yi da shi a tashar Channels TV a ranar Lahadi, gwamnan ya tunatar da cewa kafin zaɓen 2023, shi ne ɗaya daga cikin gwamnonin da s**a dage cewa dole ne mulki ya koma Kudu.

Gwamnan ya bayyana cewa, a matsayinsa na mamba a jam’iyyar All APC, ya mara wa burin takarar Tinubu.

A cewarsa, Arewa ba za ta iya zama masu adawa da Tinubu ba bayan ya samu sama da kashi 60 na ƙuri’unsa daga yankin.

Ya nuna damuwarsa kan yadda wasu ke yaɗa labaran ƙarya cewa Arewa na adawa da gwamnatin Tinubu.

“Ni mamba ne mai ƙarfi a jam’iyyar APC. Idan za a lissafa gwamnonin da s**a goyi bayan Tinubu kafin 2019 da 2023, za ka iya ambaton Gwamna Zulum. Ni ne gwamna na farko da ya fito fili ya ce dole ne mulki ya koma Kudu.

“Abin takaici, Shugaban Ƙasa ya samu labari daga da dama cewa Arewa na adawa da shi. Kashi 60.2 na ƙuri’unsa sun fito daga Arewa,” in ji shi.

Zulum ya bayyana cewa abinda gwamnonin suke buƙata shi ne a samu ƙarin tattaunawa kafin a amince da ƙudirin.

03/12/2024
02/12/2024

Ana tashi hutun rabin lokaci, kunnen doki a Wasa zagayen karshe tsakanin Karamar Hukumar Ganye da Karamar Hukumar Toungo.

02/12/2024
02/12/2024

KUN JI DAI: Yan Nijeriya na rayuwar karya kafin a cire tallafin man fetur in ji Shugaba Tinubu

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya ce 'yan kasar na rayuwar karya da hakan ya sa tattalin arzikin kasar ya yi mummunar faduwa kafin ya hau mulki ya cire tallafin man fetur.

Shugaban kasar ya ce akwai bukatar a ceto kasar daga yunkurin durkushewa da ya sanya ala-tilas sai an bullo da hanyoyi da dabarun da za su iya rike ta irinsu cire tallafin man fetur da kokarin daidaita canjin kudi.

Shugaban kasar da ya samu wakilcin shugaban jami'ar Ilorin Prof Wahab Egbewole, ya yi wannan furucin ne a wajen taron yaye dalibai karo na 34&35 na jami'ar tarayya da ke Akure jihar Ondo a karshen mako in ji jaridar Daily Trust.

01/12/2024

Daga karshe Gwamnatin jihar Katsina ta aminta da fara biyan ma'aikatan jihar Katsina sabon tsarin albashi na N70,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi daga watan Disamba

Ku karanta yadda tsarin albashin kowane ma'aikaci zai kasance da zarar an fara biya daga watan Disamba na 2024.

NYSC ta sake buɗe sansanin horaswa na Zamfara bayan wata 16Hukumar kula da matasa masu yi wa ƙasa hidima a Najeriya (NYS...
30/11/2024

NYSC ta sake buɗe sansanin horaswa na Zamfara bayan wata 16

Hukumar kula da matasa masu yi wa ƙasa hidima a Najeriya (NYSC) ta sake bude sansanin horaswa na jihar Zamfara, bayan rufe shi na wata 16 saboda dalilai na tsaro.

Yayin taron budewar da ya gudana a sansanin na wucin gadi da ke Gusau, an kuma rantsar da sabbin 'yan hidimar ƙasa na rukunin Batch C Stream 1.

Yanzu haka gwamnatin jihar na aikin sake gina sansanin horarwar na dindindin da ke karamar hukumar Tsafe.

Kulle sansanin da aka yi a shekarar 2023 ya janyo tsaiko ga matasan masu hidimar kasa da aka tura jihar, wadanda daga baya aka tura wasu jihohi kamar Kebbi mai maƙwabtaka.

Rashin kai matasan Zamfara na da nasaba da hare-haren da 'yanfashin daji ke kaiwa kusan a kullum, inda suke garkuwa da mutane don neman kuɗin fansa.

30/11/2024

Nijeriya ta kashe naira biliyan 8.8 wajen gyaran turakun lantarki da aka lalata - TCN

Kamfanin Samar da Wutar Lantarki na Najeriya ya bayyana cewa an kashe biliyan 8.8 wajen gyara turakun lantarki da 'yan bindiga da wasu bata gari su ka lalata a wurare daban-daban a fadin kasar nan.

Manajan daraktan kamfanin Injiniya Suleiman Abdulaziz ne ya sanar da hakan a Abuja, inda ya ce daga 13 ga watan Janairun 2024 zuwa yanzu manyan turakun lantarki 128 ne aka lalata.

Injiniya Suleiman ya nuna damuwarsa cewa duk lokacin da a ka cafke wadanda ke wannan aika-aikar ana gurfanar da su akan laifin sata a maimakon lalata kayan gwamnati, abinda ke sa ana bayar da su beli daga baya.

GANYE 24 MEDIA

30/11/2024

DA ƊUMI-ƊUMI: Gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Umaru Finitiri ya sanar da karin alawus alawus na masu yi wa kasa hidima na NYSC daga N10,000 zuwa ₦20,000 duk wata, daga Disamba 2024.

30/11/2024

Dole sai an haɗa kai domin samun zaman lafiya a Najeriya - Jonathan

Tsohon shugaban ƙasar Najeriya, Goodluck Ebele Jonathan ya yi wani gargaɗin cewa ana buƙatar haɗin-kai tsakanin ‘yan Najeriya, domin samun zaman lafiya.

Jonathan ya ce yadda ƴan ƙasar ke fifita kabilunsu fiye da biyayya ga Najeriya na da matukar barazana ga zaman lafiya da ci gaban ƙasa.

Tsohon shugaban ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su sake duba abubuwan da s**a sa a gaba da kuma ƙoƙarin samar da haɗinkai.

'Biyayya ko fifita kabilanci na kawo cikas ga ci gaban Najeriya, don haka ya kamata shugabanni su aiwatar da manufofin da za su karfafa haɗin-kai maimakon neman suna ko yabo na kankanin lokaci," in ji Jonathan.

Haka kuma ya nuna cewa akwai buƙatar sauya tunanin ƴan ƙasar, inda ya buƙaci ƴan majalisar tarayya da su ɗauki kowane ɗan Najeriya a matsayin nasu, ba wai ga jihohinsu ko kabilunsu kaɗai ba.

Address

Ahmadu Bello Way
Ganye

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when GANYE 24 posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to GANYE 24:

Videos

Share


Other Media/News Companies in Ganye

Show All