24/05/2024
SAKON BARKA JUMU’AH
Ranar Juma’a rana ce mai falala da girma, wannan ya sa Manzon Allah (Sallallahu Ailaihi Wa Sallam) yake girmamata, yake kuma ware ta da Karin wasu Ibadoji na daban, ga kadan daga abubuwan da ranar Juma’a ta kebanta da su:
1. Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) ya kasance yana karanta Suratus Sajada da Suratul Insan a duk asubar ranar Juma’a, kamar yadda Imamu Muslim ya rawaito.
Shaikhul Islam Ibni Taimiyya yana cewa “Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) yana karanta wadannan Surori ne saboda sun kunshi abin da ya faru, da ma abin da zai faru a wannan ranar, kuma Surorin suna dauke da bayanin halittar (Annabi) Adam, da ambaton makoma (lahira) da (bayanin) abin da zai faru ga bayi (a lahira), duk wannan zai faru ne a ranar Juma’a……..” (Duba “Zadul Ma’ad” (1/364).
2. Mustahabbi ne a yawaita salati ga Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) a daren wannan rana, da yininta, saboda fadin Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) “ku yawaita yi min salati ranar Juma’a da darenta” (Baihaki ne ya rawaito shi).
Imam Ibnil Kayyim yana cewa “Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) shi ne shugaban halitta, ranar Juma’a kuwa ita ce shugabannin ranaku, don haka yin salati ga Manzon Allah (Sallallahu Aliahi Wa Sallam) a wannan ranar yana da fifiko akan sauran ranaku…….” (Zadul Ma’ad) (1/364).
3. Yin sallar Juma’a da halartata yana daya daga cikin maya-mayan taruka na Musulunci, don haka ma duk wanda ya ki halartar Juma’a da gangan to Allah zai rufe masa zuciya, alheri ba zai rika shigarta ba.
4. Yin wanka acikinta.
5. sanya turare, an karbo Hadisi daga Abu Sa’id ya ce “Wankan Juma’a wajibi ne akan duk wani baligi, sannan ya yi aswaki, ya sanya turare in ya samu” Bukhari ne ya rawaito shi Hadisi na (880).
6. Mustahabbi ne yin aswki a wannan ranar, kamar yadda ya gabata a Hadisi.
7. Zuwa Masllaci da wuri.
8. Shagalta da sallahr nafila da Zikiri, kamar karatun Alkur’ani har zuwa fitowar liman.
9. Wajibi ne a saurari Huduba, da yin shiru ya yin da ake yinta.
10. Karanta Suratul Khahfi a wannan rana, saboda fadin Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) “Duk wanda ya karanta Suratul Khahfi a ranar Juma’a, wani haske zai daga daga karkashin kafarsa har zuwa kololuwar sama, zai zamar masa haske ranar alkiyama, kuma za a gafarta masa abin da yake tsakanin Jumu’o’in guda biyu”.
Hakim da Baihaki ne s**a rawaito shi (Shiekh Albani ya ingantaa wanan Hadisi a cikin :Irwa’ul Galil” (3/93).
11. Ana so a karanta Suratul Juma’a da Suratul Munafikun, ko kuma Suratul A’ala da Gashiya ya yin Sallar Juma’a.
12. Rana ce ta idi ga Musulmi, wanda yake maimaituwa duk sati.
13. Mustahabbi ne a sanya kaya kyawawa, saboda Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Ssllam) yace
“Duk wanda ya yi wanka ranar Juma’a ya sa turare-in ya samu-sannan ya saka kyawawan tufafina, ya fita cikin nutsuwa, har ya isa Masallaci, ya yi nafila gwargwadon abin da yaga dama, bai cutar da kowa ba, sannan ya yi shiru har liman ya fito ya yi Sallah, to hakan ya zama masa kaffarar abin da ke tsakanin Jma’a biyu” Imamu Ahmad ne ya rawaito wannan Hadisi.
14. Mustahabbi ne a gyara Masallaci asa masa turare. Umar Dan Khaddab (R.A.) ya yi umarni a lokacinsa a rika sawa Masallacin Madina turare a duk ranar Juma’a bayan rana ta raba.
15. Baya halatta ayi tafiya a ranar Juma’a, kafin ayi Sallar Juma’a in dai lokacinta ya shiga. Amma idan lokacin bai yi ba, to malamai sun yi sabani akan hakan. Sai dai zance mafi rinjaye ba laifi a tafi Duba “Almugni” na Ibnu Kudama (3/248). Da “Zadul Ma’ad” (1/370).
16. Ranace da ake son yawaita yin Ibada a cikinta, kamar yawaita Salati ga Annabi (Sallallahu Alaihi Wa Sallam), Zikiri, nafilfilu, karatun Alkur’ani da sauransu.
17. Yin sadaka a wannan rana daban yake da yin ta a sauran ranakun sati, kamar yin sadaka ne a cikin watan Azumi.
18. Ranace da Allah ya yi wa wannan al’umma kyautar ta kamar yadda Hadisi ya nuna (Duba Za’dul Ma’adi (1/40).
19. Rance da ba a kebance ta da Azumi, sai dai in mutum zai hada ta ranar Alhamis, ko Assabar.
Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) ya ce “ka da dayanku ya yi Azumin ranar Juma’a, sai in ya Azumuci ranar da take gabaninta ko bayanta” (bukhari da Muslim ne s**a rawaito).
20. Haramun ne saye ko sayarwa ga wanda ya ji kiran Sallahr Juma’a, lokacin da liman ya hau Mimbari. Idan kuwa an kulla ciniki a wananan lokaci, to malamai sun yi sabaani a kan ingancinsa. Imam Khurdabi da Ibnu kasir sun rinjaya rashin ingancinsa, don haka ya zama lalatacce (Duba Tafsirin Khurdubi (18/96) da Tafsirin Ibnu Kasir (4/392).
Muna Rokon Allah ya bamu ladan dukkan ibadun da zamuyi a cikin wannan rana mai albarka.