Kofufi da taga da

Kofufi da taga da Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Kofufi da taga da, Digital creator, Dan daji kofar gidan malam ya"u mai walda kwanar jagwa garejin yan kanta funtua, Funtua.

21/08/2023

MACE TA GARI

A mataki na farko na samun nagartacciyar mace shi ne, ka zama nagari. Matukar ka zama nagari, to ana sa ran za ka samu mace tagari.

A dabi’ar kowane mutum yana burin aurar mace tagari ko da shi ba nagari ba ne, domin kowa ya tabbatar da cewa mace tagari babbar alheri ce ga mijinta.

Akwai bukatar idan ka tashi neman aure, to ka tsaya ka yi zurfin tunani a kan wacce za ka aura, ka natsu ba a son gaggawa, kada ka biye kyale-kyalen duniya, ko wata karairaya da mace za ta yi maka, kada ka rudu da cewa mahaifinta mai hannu da shuni ne.

Ya dan uwa akwai bukatar ka lura da wadannan alamomin mace tagari kafin aure da s**a hada da: ana so ta kasance mai tarbiyya, mai ilimi da aiki da shi, mai natsuwa da kamewa, ta kasance mai lizimtar addini, ta kuma kasance mai kunya.

Bayan an yi aure kuwa: ga alamomin da ya kamata ka duba kamar haka: Rashin yi wa miji gori, godiya da dawainiyar da yake yi mata, rashin kushe kokarinsa, rashin dora masa dawainiya da wahalhalu na babu gaira babu dalili. Sauran sun hada da yi wa miji biyayya karfafa shi a kan irin kokarin da yake yi, neman shawararsa a kan al’amuranki, rashin cutar da shi, girmama iyaye da ‘yan uwansa,

Haka babu laifi ka duba mace mai kyawu, ma’ana ka ce kai mai kyau za ka aura kana da damar yin haka, ba laifi ba ne, amma Musulunci ya hana aurar mace don zallar kyawunta ko yawan dukiyarta, inda Ma’aiki SAW ya ce: “Kada ku auri mace don zallar kyawunta ko dukiyarta ko nasabarta, ku dai ku auri ma’abociyar addini hannunka zai ribatu”

Wani kuma ya fi son baka, wankan tarwada, wani kuma shi duk yadda za a yi ya fi son fara kamar yadda a zamanin nan mutane da yawa suke raja’a a kai. Idan har ka samu duk wacce kake so din, to lallai kada ka sanya yaudara a ciki, yi kokari, ka gaya mata gaskiyar halin da kake ciki, ita ma ta gaya maka gaskiya, kada ka bari ta yaudare ka, kuma kai ma kada ka yaudare ta.

Lallai ka more! Kuma abin a yi maka murna ne samun mace tagari, domin duk wani dadin duniya na gareta.

13/04/2023

What are you want to me know

Alhamdulillah
09/04/2023

Alhamdulillah

Congratulations 🎆

Congratulations 🎆
08/04/2023

Congratulations 🎆

07/04/2023

To idan kaine ya zakayi?

Address

Dan Daji Kofar Gidan Malam Ya"u Mai Walda Kwanar Jagwa Garejin Yan Kanta Funtua
Funtua

Telephone

+2348060361873

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Kofufi da taga da posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share


Other Digital creator in Funtua

Show All