Online radio zamani fm dutse

Online radio zamani fm dutse Labaran duniya

07/02/2024

I LOVE YOU DIN BANZA.

Wata rana wani malami yana zaune da jama'a ana ta hira, sai ya tambayesu "anya kuwa suna son matayensu?" gaba daya s**a amsa da "kwarai kuwa". Sai malam ya sake cewa "Yaushe rabon da kowannenku ya furtawa matarsa cewa yana sonta? Misali ya ce "I love U". To, anan ne s**a fara bada amsa, wani ya ce kusan wata daya kenan, wani ya ce fiye da shekara, wani ya ce ba zai iya tunawa ba, da sauransu. Daga nan malam ya ce kowa ya rubuta sakon ta wayar salula ya aikawa matarsa, domin ganin wadanne irin amsoshi zasu bayar. Cikin kankanin lokaci sai ga amsoshi sun fara zuwa daga wajen matayen k**ar haka:

1. Mhmm da kenan banda yanzu.....

2. Maganar auren naka ta rushe kenan?

3. Kana son na baka aron kudi kenan?

4. A mafarki kenan

5. Tab Allah ya k**aka, bari ka dawo ka fadamin wadda kaje aik**a wannan sako

6. Hmmm me kake nufi? Wannan karon ba zan yarda ba.

7. Waye wannan?

8. Wata sabuwa

9. Yau kuma?

10. Hmm munafiki wallahi ban hakura da abin da kamin ba....

11. I love u din banza.....

12. Nafada maka, ka daina shaye shaye......😄😃😃
Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un.... Yaku
jama'a kunsan waye masoyinku na gaskiya
kuwa??? To shine Manzon Allah saw, lokacin da
mala'ikan mutuwa yaxo domin karbar ransa sai
yaji zafi kwarai ya tambayi mala'ikan mutuwa
yace dama haka akejin zafi yayin mutuwa? Sai
yace masa haba ai kai nan an saukaka maka ne
matuka amma sauran mutane ai zafin yawuce
haka nesa ba kusa ba, Allahu akbar jama'a
kunsa me manxon Allah saw yace? To cewa yayi
yana neman alfarma cewar a hada masa
dukkan wani zafi da ukuba da ake yiwa Al
ummarsa yayin mutuwa shi ayi masa baki daya,
ya daukemana.... Allahu akbar jama'a wannan
bawan Allah yana yi mmana sonda ko
mahaifanmu basa yimana, ya Allah ka kara
tsira da Aminci ga shugabanmu Annabi
Muhammadu saw...
Allah ka yafe mana
dukkan laifukansa, ya Allah ka biya masa
dukkan bukatunsa na duniya

Nan bada Jimawa ba Za'a Kawo karshen Wahalhalun da Yan Najeriya ke Fuskanta -Cewar Remi Matar TinubuUwargidan Shugaban ƙ...
06/02/2024

Nan bada Jimawa ba Za'a Kawo karshen Wahalhalun da Yan Najeriya ke Fuskanta

-Cewar Remi Matar Tinubu

Uwargidan Shugaban ƙasa, Sen. Oluremi Tinubu ta bayar da tabbacin cewa nan ba da jimawa ba za a kawo karshen wahalhalun da ‘yan Najeriya ke fuskanta tare da ingantattun manufofin Gwamnatin tarayya.

Uwargidan Shugaban ƙasar ta bayar da wannan tabbacin ne a Yau Litinin a gidan Gwamnatin tarayya. Yayin wata ganawa da matan gwamnonin kan aikin Gidauniyar ta, Renewed Hope Initiative (RHI).

Ta bada tabbacin cewa shekarar 2024 na cike da "zaman lafiya, ci gaba, wadata da kuma manyan nasarori" don amfanin 'yan Najeriya baki daya.

Remi Tinubu ta yabawa matan gwamnonin bisa kokarinsu da goyon bayansu a shekarar 2023, inda ta bukace su da kada su yi kasa a gwiwa wajen magance bukatun marasa galihu a jihohinsu.

Lokaci irin wannan yana buƙatar tunani mai zurfi, don haka, dole ne dukkan hannaye su kasance a kan bene. Bugu da ƙari, yanayin wahala na ɗan lokaci ne, ba da daɗewa ba zai shuɗe.

"Ofishina ne ke tafiyar da manufar RHI don cika ajandar sabunta bege na Gwamnatin shugaba Tinubu," in ji ta.

Ta ce shirin tallafa wa aikin gona na mata (WASP), a karkashin RHI, zai baiwa manoma 20 duk wani, daga jihohi biyar na shiyyar Kudu maso Gabas.

“Wadannan manoma za su samu N500,000 kowanne sannan kuma za a ba da jimillar N10m ga ko’odinetocin jihohin RHI biyar

“Hukumar bunkasa filayen noma ta kasa tare da hadin gwiwar RHI za su tallafa wa karin mata manoma 80 daga kowace jiha tare da samar da horo da karfafawa da kuma kayan aikin noma.

"Zamu sayi duk amfanin gonaki bayan girbi wa," inji ta.

12/06/2023

Lalataccen Kiristan Kudu Ya Fi Musulmin Kwarai Dan Arewa Chanchantar Ya Zama Shugabancin Majalisar Dattawan Najeriya, Inji Kashim Shettima Daga Comr Abba Sani Pantami Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya ce ba daidai ba ne musulmin Arewa ya zama shugaban majalisar Dattawa ba. A yayin wani z...

10/06/2023

LABARI: Mamallakin kungiyar Man City Sheikh Mansour yana Istanbul don kallon wasan karshe na gasar zakarun Turai

Rabonsa da halartar kallon wasan Manchester City tun shekarar 2010.

Daga: [Fagen Wasanni]

22/05/2023

Yau Za a Kaddamar Da Matatar Mai Ta Dangote

In an jima kadan ne ake sa ran Shugaba Buhari zai kaddamar da matatar mai ta Dangote, wadda ita ce mafi girma a nahiyar Afirka.

Ana sa ran matatar, mai karfin samar da ganga 650,000 na tataccen mai a kullum za ta biya wa Najeriya bukatunta na man fetur da sauran dangoginsa 100 bisa 100.

Akwai kuma hasashen ‘yan kasar nan za su samu sauki daga abubuwan da matatar za ta rika samarwa irin su kananzir da man dizel da man jirgin sama da man fetur da dai sauransu.

Haka kuma ana hasashen za ta samar da Dala biliyan 21 — kimanin Naira tiriliyan 9.7 — a shekara, a bangaren danyen mai, duk da cewa sai nan gaba a cikin wannan shekara matatar za ta fara aiki.

Rahoton cibiyar S&P Global Commodity Insights mai nazari kan cinikayya ya nuna a cikin watan Yuni mai k**awa Matatar Mai ta Dangote za ta fara samar da tataccen mai.

‘Yan Najeriya na murnar ganin fara ikin matatar wadda kamfanin mai na kasa (NNPCL) ke da kashi 20 cikin 100 na hannun jari.

Masu ruwa da tsaki a bangaren mai na ganin matatar za ta sauya matsayin Najeriya daga mai shigo tataccen mai, zuwa mai fitarwa kasashen waje.

Wannan kuwa na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin kasar ke shirin soke tsarin biyan tallafin mai wanda kudin da take kashewa a kai y karu daga biliyan N351 a 2005 zuwa tiriliyan N4.39 a 2022, kafin ya karu zuwa tiriliyan N3.6 a watanni shida na farkon 2023.

Duk da cewa babu tabbacin fara aikin matatar zai rage tsadar mai a kasar, zai rage kudin da ake kashewa wajen jigilar man a irin asarar da ake yi.

Wasu masana na ganin za a saumu saukin farashin mai idan har gwamnatin Najeriya za ta ba wa matatar danyan mai a farashi mai sauki; sai dai kuma kamfanin mai bukaci haka ba tukuna.

Wasu masanan kuma na ganin fara aikin matatar zai bude wani sabon babi a kan batun tallafin da gwamnati ke neman cirewa.

Shugaban kungiyar ma’aikatan man fetur da iskar gas (PENGASSAN), Kwamred Festus Osifo, ya ce fara aikin matatar zai rage kudaden da ake kashewa wa

22/05/2023

Ba Zan Daina Rusau Da Korar Ma’aikata Ba, Har Sai Na Bar Mulki —El-Rufai

Gwamnan Kaduna mai barin gado, Nasir El-Rufai, ya ce ba zai daina da korar bara-gurbin ma’aikata da rusa haramtattun gine-gine ba, har sai ya bar mulkin jihar.

El-Rufai ya yi wannan faruci ne washegarin da ya kwace izinin mallaka tare da sanya alamar rusa wasu kadarori tara mallakin tsohon gwamnan jihar, Sanata Ahmed Mohammed Makarfi.

Da yake bayani a taron kaddamar da littafin da wani dan jarida, Emmanuel Ado, ya rubuta a kan ayyukansa, mai suna “Putting The People First”, ya ce, “Har zuwa ranar karshen mulkina, ba zan daina kawar da bara gurbin mutane da sauran miyagun abubuwa ba.”

A cewarsa, “Duk abin da na ga bai dace ba, zan kawar da shi, saboda kada su zama matsala ga sabon gwamnan da zai karbi mulki.”

A lokacin taron, Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, ya bayyana El-Rufai a matsayin mutum mara tsoro, wanda samun mai tsage wa gwamnati gaskiya k**arsa, ke da wuya.

A cewar Wike, “Samun shugaba irin El-Rufai sai an tona, wajen hazaka da jarumta domin tabbatar da adalci ga kowa.

“Shi ba dan amshin shata ba; Ba zan manta wasikarsa ga Shugaba Buhari a watan Maris na 2017 ba, wanda ya tayar da kura, inda ya ja hankalin shugaban kasa kan muhimmancin cika alkawuran da ya yi wa jama’a saboda kada ya bar mummunan tarihi.

“Da wuya a samu gwamnan da zai iya yin haka ga shugaban dan jam’iyyarsa, in ba jarumi wanda ba dan kanzagi ba.”

A wurin taron, Wike ya ba da gudummawar Naira miliyan 20, haka ma shugaban kasa mai jiran gado, Bola Ahmed Tinubu, wanda tsohon Shugaban Asusun Kula da Manyan Makarantu ta Kasa (TETFUND), Kashim Imam, ya wakilta.

16/05/2023

Ƙungiyar Likitocin Najeriya Za Ta Shiga Yajin Aiki


Ƙungiyar Likitoci Masu Neman Ƙwarewa ta Najeriya ta ayyana shiga yajin aikin gargaɗi na kwana biyar kan gaza biya mata buƙatunta da gwamnatin tarayya ta yi.

Ƙungiyar ta bayyana ɗaukar matakin ne bayan ganawar da shugabanin kwamitin gudanarwarta ya yi ranar Litinin.

Likitocin sun ce za su fara yajin aikin gargaɗin ne daga ranar Laraba 17 ga watan Mayu zuwa ranar Litinin 22 ga wata.

Likitocin na buƙatar gwamnati ta gaggauta yin ƙari a tsarin albashin ɓangaren lafiya da kashi 200 kan albashin likitocin na yanzu.

Sannan a ƙara musu kuɗin alawus da s**a nema cikin wata wasiƙa da shugaban ƙungiyar ya rubuta wa ministan lafiya Dakta Osagie Ehanire ranar 7 ga watan Yulin 2022.

Haka kuma ƙungiyar ta buƙaci a gaggauta biyan su kuɗin horaswa na shekarar 2023, k**ar yadda yake ƙunshe cikin yarjejeniyar da s**a cimma a wata ganawa da masu ruwa da tsaki, da ma'aikatar lafiya ta jagoranta.

Sannan kuma ƙungiyar na buƙatar gwamnatin tarayya da ta fara biyan wasu mambobinta bashin albashin da suke binta a shekarun 2014 da 2015 da kuma 2016.

A ranar 29 ga watan Afrilu ne dai ƙungiyar likitocin ta bai wa gwamnatin tarayya wa'adin mako biyu da ta zartar da yarjejeniyar da s**a cimma ko kuma ta tsunduma yajin aiki.

15/05/2023

BREAKING NEWS
✊✊
MAI MARTABA SARKIN DUTSE ALH. MUHAMMAD HAMIM NUHU SANUSI ya halarci Taron Karramawa da Walimar Yaye Ɗalibai Saba’in da Huɗu (74) da s**a haddace Al_Qur’ani Mai Girma da kuma Ɗalibai Talatin da Bakwai (37) da s**a Sauke Al_Qur’ani Mai Girma cikin Shekara Ɗaya (1) Karkashin Cibiyar SHEIKH JA’AFAR MAHMUD ADAM FOUNDATION dake Rukunin Gidajen Malam Inuwa Dutse dake Ɗanmasara wanda aka gabatar dashi a yau a Malam Aminu Kano Triangle dake Dutse babban Birnin Jihar Jigawa.

Taron ya samu Halartar Uban Taro wato MAI MARTABA SARKIN DUTSE ALH. MUHAMMAD HAMIM NUHU SANUSI, Shugaban Taro Sheikh Dr. ABdullahi Bala Lau Shugaban Kungiyar Izala ta Kasa, Sheikh Dr. Kabiru Haruna Gombe Sakataren Kungiyar Izala ta Kasa, Babban Limamin Masarautar Dutse Dr. ABubakar Sani Birnin Kudu, Mai Masaukin Baki Shugaban Karamar Hukumar Dutse Hon. Bala Usman Chamo da sauran su.

Bayan Kammalawa da Bikin Yaye Daliban ne sai aka dunguma ya zuwa Fadar Mai Martaba Sarki yayin da Shugaban Kungiyar Izalar ta Kasa ya fara da Jawabin Godiya ga Mai Martaba Sarki kana da yi masa kyakkyawan Albishir da bashi Mukamin Grand Patron na kungiyar Agaji ta Izala a kasa baki daya. Yace muna sane da dukkan alkhairan da marigayi Mai Martaba Sarki yake wajen kwaso kananan yara wadanda s**a musulunta domin taimaka musu k**a daga harkar karatunsu da ci da shan su har sai sun girma. Ya kuma jaddada masa da cewa zasu bayar da gudunmawa wajen duba maganar da yayi akan mazauna Yankin Sumaila domin taimakawa wajen ganin an musu Da'awa domin shigowa wannan addinin Allah Madaukakin Sarki.

A nasa jawabin Mai Martaba Sarkin Dutse ya fara da jawabin Maraba sannan ya tunasar musu da yadda gidan nan yake domin daman chan akan harkar hidimtawa Sunnah ta Manzon Allah S.A.W yake bisa shawari da su Malaman Sunnah suke wa Marigayi domin sune fitulun da suke haskaka masa gabansa, ya kuma roki yadda s**a rike Marigayi haka shima su rike shi a wajensu, ya kuma ce In Sha Allahu yadda Marigayi ya rike su h

14/05/2023

Shugaba Buhari Ya Kammala Aikin Wutar Lantarki Ta Zungeru Kamar Yadda Ya Yi Alkawari.

Ministan wutar lantarki Injiniya Abubakar D. Aliyu ya sanar da cewa, an kammala aikin samar da wutar lantarki mai karfin megawatts 700 na Zungeru.

A cewar ministan, tuni kamfanin rarraba wutar lantarkin na Najeriya (TCN) ya shirya ya karbi wutar da aka samar daga cibiyar samar da wutar lantarkin.
Ya kuma ce hakan zai cike gibin da ake samu na bukatun wutar lantarkin kasar.

Injiniya ya fadi haka ne a ranar Asabar, 13 ga watan Mayu a jihar Neja a lokacin da yake bayani bayan ziyarar duba aikin da aka kammala.

A lokacin ziyarar, yana tare da gwamnan jihar Abubakar Sani da kuma wasu manyan jiga-jigan majalisar da ke kula da ayyukan mak**ashi.

Da yake karin haske, ya ce an kammala dukkan gwaje-gwaje na aiki da na’urorin da ake amfani dasu, kuma za a kaddamar da aikin nan ba da jimawa ba a hukumance.

A cewarsa, tun shekarun 1960 rabon da Najeriya ta yi irin wannan aikin, amma sai gashi ya samu a karkashin jagorancin Shugaba Buhari.

Hakazalika, ya ce, gwamnatin Najeriya ta zuba dimbin hannun jari a wannan aikin na Zungeru don ta inganta samun wutar lantarki.

A gefe guda, ya ce irin wadannan ayyuka na daga buri da kudurin Buhari na ciyar da Najeriya gaba a karkashin ikonsa.

Baya ga samar da karin wutar lantarki ga ‘yan Najeriya, aikin a halin yanzu ya samar da ayyukan yi ga ‘yan Najeriya da dama kuma zai samar da hanyoyin magance ambaliyar ruwa, ban ruwa a noman rani, da kuma samar da ruwa wadatacce.

A nasa bangaren, gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello, ya yabawa shugaba Buhari kan kammala aikin samar da wutar lantarkin mai karfin megawatt 700 na Zungeru ta jihar Neja.

A tun farko, gwamnatin Najeriya ta bayyana yadda aikin wutar lantarkin ke cin kudi da kuma yadda 'yan Najeriya ke shakku.

13/05/2023

Ayyukan Raya Ƙasa: Najeriya na buƙatar kashe dala biliyan 100 duk shekara – Daraktan Kasafin Kuɗaɗe.

Babban Daraktan Ofishin Tsare-tsaren Kasafin Kuɗaɗe, Ben Akabueze, ya ce aƙalla Najeriya na buƙatar ta riƙa kashe dala biliyan 100 duk shekara, idan ana so a cimma samar da dukkan ayyukan raya ƙasa da ake tsananin buƙata.

Akabueze ya ce tilas an fa an raba ƙafa wajen kashe kuɗaɗen, wato gwamnati da kuma masu kamfanoni da masana’antu na kan su riƙa zuba kuɗaɗe wajen gudanar da ayyukan ci gaban da ƙasar nan.

Ya bayyana haka a ranar Laraba, a wurin taron nuna wa zaɓaɓɓun ‘yan majalisar tarayya sanin mak**ar aikin majalisa.

Ya ce k**a daga Gwamnatin Tarayya da gwamnatin jihohi sun kasa iya kashe dala biliyan 100 wajen bunƙasa ayyukan raya ƙasa a duk shekara.

“Na farko dai kafin a iya saisaita tattalin arzikin Najeriya, mu na buƙatar a riƙa kashe dala biliyan 100, aƙalla duk shekara.

Ya ce kasafin da ake samu daga gwamnatin tarayya a duk shekara bai wuce dala biliyan 30 ba. Jihohi da Babban Birnin Tarayya, FCT ba su ƙara wa kasafin Najeriya wani karsashi ko ƙarfi. Wato idan ma sun kashe dukkan kuɗaɗen da tarayya ke ba su, har yanzu dai ana barin giɓi sosai,” haka Akabueze ya bayyana.

Babban Daraktan na kasafin kuɗaɗe, ya nuna matuƙar damuwa ganin babu wata ƙwaƙƙwarar doka kan kasafin kuɗaɗe.

Sai dai ya ce akwai ƙudiri ajiye a Majalisar Tarayya. Daga nan ya yi kira ga majalisa mai barin gado su ƙoƙarta su saka hannu kan ƙudirin domin ya zama doka.

13/05/2023

Hukumar Raba Daidai Ta Nijeriya Ta Bukaci A Kara Wa Tinubu Da Gwamoni Albashi

Shugaban kasa mai jiran gado, Asiwaju Bola Tinubu, zai ci gaba da karbar Naira miliyan 1 da dubu dari biyu a matsayin albashinsa a duk wata k**ar yadda shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ke karba.

Tunibun zai ci gaba da karbar albashin a haka idan har ba a rattaba hannu kan kudurin karin albashin zababbu masu rike da kujerun siyasa da manyan ma’aikatan gwamnatin tarayya ya zama doka ba kafin ranar 29 ga watan Mayun 2003 ba.

Babban shugaban hukumar raba daidai na kasa RMAFC, Dakta Bello Muhammad Shehu, ya bayyana hakan a taron lakcha karo na farko kan tattalin arziki da kuma gabatar da wani Littafi da aka gudanar a Abuja.

Dakta Bello ya ce, gwamnonin na karbar Naira miliyan 1.1 a matsayin albashi duk wata, inda ya bayyana cewa, wasu manyan ma’aikata na hukomomin gwamnatin tarayya, na karbar albashi duk wata da ya dara na shugaban kasa da gwamnonin.

A cewarsa, ” Shugaban kasa na karbar albashin Naira miliyan 1.2 ne duk wata, ina kuma da tabbacin cewa wasu manya a hukomomin gwamnatin tarayya, a duk wata suna karbar albashin Naira miliyan 5, wasu kuma Naira miliyan 2.”

Ya ci gaba da cewa, bai da ce a ce ma’aikacin gwamnatin tarayya na karbar albashin da ya zarce na shugaban kasa ko na gwamoni ba.

A cewarsa, alummar gari ne kawai za su iya kalubalantar hakan, inda ya ce, an yi nazari kan albashin zababbun ‘yan siyasa da na wasu manyan ma’aikatan gwamnatin tarayya da na bangaren Shari’a a shekarar 2008.

Ya ce akwai bukatar a sake yin nazari kan albashin na su, inda ya bayyana cewa, kundin tsarin mulkin Nijeriya da aka sabunta ya bai wa hukumar RMAFC damar yanke albashin zababbun ‘yan siyasa da na manyan ma’aikatan gwamnatin tarayya da kuma na ma’aikatan Shari’a.

Don haka bisa wannan tsarin, hukumar ta fara yin nazari kan albashin zababbun ‘yan siyasa da manyan ma’aikatan gwamnatin tarayya da kuma na bangaren Shari’a.

12/05/2023

Za A Tafka Mamakon Ruwan Sama A Arewa A Kwanaki Masu Zuwa - NiMet

Hukumar Kula da Yanayi ta Nijeriya (NiMet) ta gargadi mazauna wasu jihohin Arewacin kasar nan da su shirya tsaf domin samun ruwan sama mai karfi a cikin kwanaki masu zuwa.

A cewar wata sanarwa da aka fitar ranar Alhamis, “A halin yanzu ana ganin tsawa a sassan Arewacin kasar nan da s**a hada da Borno, Taraba, Gombe, Bauchi da Kano.

Ana sa ran wadannan za su yadu zuwa yamma 0don ba da tsawa daidai gwargwado ga wasu biranen.”

Sanarwar ta kara da cewa, ana sa ran samun masu tsawa a halin yanzu wanda za ta yadu zuwa gabas zuwa garuruwan Filato, Abuja, Nasarawa, Jigawa, Adamama, Yobe da Borno,

Jihohin Bauchi, Gombe, Kaduna, Kano da Katsina su ma za su fuskanci yanayin.

NiMet ta ce a yankunan da ake sa ran tsawa, ana iya samun iska mai karfi kafin damina kuma a saboda haka, ana iya sare itatuwa, da igiyoyin lantarki, da abubuwan da ba a tabbatar da su ba, da kuma raunanan gine-gine, don haka ana shawartar jama’a da su yi taka tsantsan tare da zama a gida musamman a lokacin ruwan sama k**ar da bakin kwarya don gudun kada walkiya ya same su.

NiMet ta shawarci dukkan ma’aikatan jirgin sama da su yi amfani da rahotannin yanayi lokaci-lokaci don ingantaccen shiri a ayyukansu.

Ta kara da cewa matsakaicin ruwan sama zai iya haifar da ambaliya.

Haka kuma an bukaci hukumomi da daidaikun jama’a da su tashi tsaye domin dakile asarar rayuka da dukiyoyi a lokacin damina.

12/05/2023

Ina Fatan Tinubu Ba Zai Sake Tafka Kuskure Irin Na Gwamnatin Buhari Ba - Khalifa Muhammadu Sanusi ll

Mai Martaba Sarkin Kano na 14 kuma Khalifan Tijjaniyya a Najeriya, Khalifa Muhammadu Sanusi II, ya ce dole ne gwamnati mai zuwa ta yi koyi da kura-kuran gwamnatocin da s**a shude ta hanyar nada kwararrun mutane a muk**ai da za su bunkasa cigaban Najeriya.

Da yake magana a wani taron tattaunawa da kaddamar da littafi a Abuja, wanda shirin Carnegie Africa tare da hadin gwiwar Agora Policy s**a shirya, Khalifa Sanusi ya ce yana fatan ganin jerin sunayen ministocin da shugaba mai jiran gado zai nada.

Taken taron shi ne "Yadda Najeriya za ta iya gina makomar tattalin arzikin bayan man fetur".

Ya kuma yi kira ga gwamnati mai zuwa da ta kare cibiyoyin gwamnati "daga wuce gona da iri na 'yan siyasa".

"Domin mu samu ci gaba a kasar nan, dole ne mu yi koyi da nagari da mara kyau. Dole ne mu ga abin da muka yi daidai. Ya kuma k**ata mu duba inda muka yi kuskure cikin wayo sosai,” inji Khalifa Sanusi.

"Idan ba mu fahimci inda muka tafi ba, ba za mu iya komawa kan hanya ba.

“Don haka, a ina muke a yau, za a rantsar da gwamnati a ranar 29 ga Mayu kuma ina ganin lokaci ya yi da za mu fara fadin me muke fata daga wannan gwamnatin.

Mun yi asarar kasa mai yawa da muka samu a baya. Kuma a nan ina magana ne ga ma’aikatan gwamnati da kuke da ikon da ba a zaba ba.

“Cibiyoyin da aka kafa don kare tsarin daga wuce gona da iri na ’yan siyasa wadanda abin takaici s**a shiga harkar siyasa.

“Kuna da babban bankin da ya k**ata ya samu daidaiton farashi da daidaiton farashin canji a matsayin aikin sa kuma an ba shi ‘yancin kai da cin gashin kansa ta yadda zai ce a’a ga ‘yan siyasa.

“Kuna da bangaren shari’a da ya k**ata a yi adalci kuma a ba ku ‘yancin cin gashin kai ta yadda za ta iya cewa a’a ga ‘yan siyasa. Kuna da 'yan sanda, kuna da hukumomin yaki da cin hanci da rashawa.

“An gina wadannan cibiyoyi. Dimokuradiyya ba wai kawai yin zabe ba ne, a’a ana bin doka da oda. Yanzu m

11/05/2023

Shugaba Buhari Ya Bukaci Majalisar Dattawa Ta Amince Masa Karbo Bashin Dala Miliyan 800

Makonni biyu bayan Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ta dakatar da cire tallafin mai, har sai lokacin sabuwar gwamnati, duk da haka gwamnatin ta roƙi Majalisar Dattawa ta amince mata ciwo bashin dala miliyan 800 ɗin da za a raba wa marasa galihu su miliyan 50, domin tausaya masu halin ƙuncin tsadar rayuwar da za su afka, idan aka cire tallafin fetur a ƙarshen Yuni.

Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan ne ya karanta wasiƙar da Shugaba Buhari ya aika a jiya Laraba a zauren Majalisa, saura kwanaki 19 ya sauka daga mulki.

Shugaba Buhari ya ce za a tura wa talakawa miliyan 50 ɗan alawus ɗin dannar ƙirjin ba su haƙuri su rungumi tsadar fetur, bayan cire tallafi.

Ya ce Majalisar Zartaswa ta rattaba hannun amincewa, yanzu Majalisar Dattawa kaɗai ya ke jira.

Majalisar Tattalin Arzikin (NEC) ta dakatar da cire tallafin fetur da shirya yi kafin ƙarshen mulkin Shugaba Muhammadu Buhari.

Ministar Harkokin Kuɗaɗe, Kasafi da Tsare-tsare ta Ƙasa, Zainab Ahmed ce ta bayyana wa manema labarai haka, bayan tashi daga taron su na ƙarshe a Fadar Shugaban Ƙasa.

Taron dai Mataimakin Shugaban Ƙasa, Yemi Osinbajo ne ya jagorance shi.

Zainab ta ce Majalisar Tattalin Arziki ta cimma yarjejeniyar dakatar da janye tallafin a yanzu, bisa la’akari da cewa idan aka yi haka a yanzu, lamarin ko kaɗan ba zai yi daɗi ba.

Zainab tace "Za a ci gaba da tuntuɓar gwamnonin jihohi da wakilan gwamnati mai jiran gado, domin tattauna yadda za a ɓullo wa lamarin.”

“Tun tuni ya k**ata a ce an cire tallafin fetur, domin gwamnati ba za ta iya ci gaba da biyan tallafin ba. To sai dai kuma tilas idan za a cire tallafin, a cire ta yadda raɗaɗin tsadar fetur ba zai yi wa talakawa ciwo sosai ba. Wato a samu hanyar rage masu raɗaɗin tsadar fetur ɗin.

“Kenan ana buƙatar ci gaba da tattauna mafitar da za a bi da kuma yadda za a tsara bin mafitar, har a tallafa wa mutanen da tsadar fetur ɗin za ta fi shafa.

09/05/2023

Jirgin ruwa ya nutse da mutum 20 a karamar hukumar Shagari da ke jihar Sokoto.

Mutanen sun bar gidajen a yau Talata da misalin karfe 12 na rana domin tafiya samo itacen dafuwa sai jirgin ya nutse da su gaba daya.

Masu aikin ceto sun tsamo mutum 15 a mace ana neman biyar a yanzu haka ba a gansu ba.

Gulbin kusan duk shekara sai mutane sun nutse a cikinsa tare da samun salwantar rayuwa.

08/05/2023

Dole Tinubu Ya Bayyana Kadarorin Sa Kafin A Rantsar Da Shi - Hukumar Ɗa'ar Ma'aikata

Kwanaki 22 gabanin rantsar da shugaban kasa, hukumar kula da da’ar ma’aikata ta ce zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Tinubu da Mataimakin sa, Kashim Shettima da sauran zaɓaɓɓun gwamnoni 28 masu jiran gado dole ne su bayyana kadarorin su kafin ranar 29 ga watan Mayu.

Ana sa ran sauran jami'ai da s**a hada da zababbun 'yan majalisar dattawa da na wakilai za su bayyana kadarorin su kafin ranar 5 ga watan Yuni da za a rantsar da su.

Mai magana da yawun hukumar Misis Veronica Kato, ta shaidawa jaridar PUNCH a Abuja cewa bayyana kadarorin wani bangare ne na tsarin rantsuwar, k**ar yadda doka ta tanada.

Ta bayyana cewa wasu zababbun jami’ai da dama sun fara karbar fom din bayyana kadarorin su a ofisoshin hukumar na kasa kuma ana sa ran za su mika kwafin ga hukumar kafin ranar rantsuwa.

Jami’ai masu barin gado da s**a hada da hadiman shugaban kasa, gwamnonin jihohi 28 da ministoci, ‘yan majalisar dokoki ta kasa da na jihohi da shugabannin kananan hukumomi za su karbi fom din bayyana kadarorin da hukumar za ta yi daidai da yadda kundin tsarin mulki na shekarar 1999 ya tanada.

Har yanzu dai babu wani tabbaci ko shugaban kasa, Muhammadu Buhari da Mataimakin sa Farfesa Yemi Osinbajo da sauran jami’an gwamnati sun bayyana kadarorin su na shirin barin ofis k**ar yadda doka ta tanada ba.

Hukumar tayi gargadin cewa ba za a rantsar da duk wani jami’in da ya gaza yin aiki ba, yana mai jaddada cewa bayyana kadarorin na cikin shirin kaddamar da aikin.

“Amma abu daya ya tabbata; babu wani jami’in gwamnati da za a rantsar da shi ba tare da cike fom din bayyana kadarorinsa ba. Abin da ke cikin dokarmu ke nan. Kafin a rantsar da kowane zaɓaɓɓen jami'an gwamnati, dole ne su gabatar da fom ɗin bayyana kadarorin su. Yana daga cikin abubuwan da ake bukata na bikin rantsuwar,” in ji Kakakin hukumar Misis Kato.

Kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadi cewa dukkan jami’an gwamnati za su bayyana ka

04/05/2023

EFCC Ta Karbe Gidaje 324 A Kano

Hukumar da ke Yaki da Masu Yi wa Tattalin Arzikin Kasa ta’annati, EFCC, ta ce wata kotu ta ba ta damar karbe gidaje 324 a Jihar Kano da ake zargi an gina ta hanyar amfani da kudaden haramun.

Da yake magana bayan yanke hukuncin a wannan Larabar, mai magana da yawun EFCC, Wilson Uwujaren, ya ce galibin kadarorin na nan a wasu yankuna masu tsada da ke birnin Kano.

A cewarsa, Mai Shari’a Inyang Ekwo na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, “ya bayar da umarni a karbe” gidajen k**ar yadda EFCC ta bukata a wajensa.

Hukumar ta ce gidajen sun hada da guda 168 da ke Sheikh Ja’afar Mahmud Adam Bandirawo City; guda 122 da ke Sheikh Nasiru Kabara (Amana City), Kano da kuma 38 da ke Sheikh Khalifa Ishaq Rabiu City, Kano.

EFCC ta kara da cewa gidajen sun hada da masu dakuna biyar-biyar, hurdudu, uku-uku da masu biyu-biyu da sauransu.

A cewarta, ana zargi an gina gidajen ne da “kudin da aka samu ta hanyar haramun daga Hukumar Kula da ’Yan Fansho ta Jihar Kano.”

12/04/2023

Rashin Aikin Yi A Najeriya Zai Ƙaru Zuwa 41% a 2023 – Rahoto

Kamfanin bada shawara kan harkokin kuɗi da haraji, KPMG ya yi hasashen matsalar rashin aikin yi a Najeriya za ta ƙaru zuwa kashi 40.6 cikin 100 idan aka kwatanta da matakin da ta kai bara, wato kashi 37.7 cikin 100.

KPMG ya bayyana haka ne a rahotonsa da yake fitarwa kan tattalin arziki inda a ciki ya ce "matsalar rashin aikin yi za ta ci gaba da zama babban ƙalubale a 2023 saboda rashin zuba hannun jari daga kamfanoni masu zaman kansu da ƙarancin masana'antu da rashin bunƙasar tattalin arziki k**ar yadda ya k**ata da kuma kasancewar tattalin arzikin Najeriya ba zai iya samar wa mutum miliyan 4 zuwa 5 aikin yi ba duk shekara."

Rahoton ya kuma bayyana cewa ana fatan ma'aunin tattalin arzikin Najeriya, GDP zai ci gaba da samun tagomashi da kashi 3 cikin 100 a 2023 sai dai cikin yanayi irin na tafiyar hawainiya saboda yanayi na miƙa mulki.

Kamfanin ya kuma yi hasashe cewa ɓangaren sadarwa da harkokin kasuwanci da kuma ɓangaren mai za su farfaɗo sanadin matakan da ake ɗauka na magance matsalolin tsaro.

12/04/2023

Sojoji Sun Kashe Wani Fitaccen Ɗan Bindiga A Kaduna

Dakarun sojin Najeriya sun ce sun samu nasarar kashe wasu jagororin 'yan fashin daji biyu tare da kwace mak**ai da harsasai da kuma wasu kayyaki.

A wata sanarwa da rundunar ta fitar a shafin na Tuwita ta ce jami'anta sun k**a yaron 'yan fashin ne a lokacin da ubangidan nasa ya aike shi domin sayen harsasai a cikin gari.

A cikin sanarwar da mai riƙon muƙamin daraktan hulda da jama'a na runduna ta ɗaya ta sojin Najeriya Laftanar Kanal Yahaya Musa ya fitar, ya ce sun kashe 'yan bindigar ne sak**akon samun bayanan sirri.

Bayanan da rundunar ta samu sun nuna cewa wani fitattcen ɗan bindigar da ya addabi jihar mai suna Isiya Danwasa ya tura ɗaya daga cikin yaransa mai suna Yunusa domin sayo musu mak**ai da harsasai a cikin gari.

Tuni dai Gwamnan jihar Kaduna malam Nasir El-Rufai ya yaba wa sojojin rundunar Operation Forest Sanity kan nasarar kashe kasurgumin shugaban ‘yan fashin dajin.

Wata sanarwa da Ma’aikatar Tsaro da Harkokin Cikin Gida ta jihar ta fitar ranar Talata ta ce Isiya Danwasa ya dade yana kashe-kashe da satar mutane da satar dabbobi a fadin jihar.

“Danwasa ya gamu da ajalinsa ne a yayin wani kwanton bauna da aka shirya a yankin Sabon Birni da ke karamar hukumar Igabi.

“Gwamna El-Rufai ya yaba wa sojojin kan wannan aiki nasu na bajinta da s**a yi da har ya jawo mutuwar Danwasa da wasu na kusa da shi,” in ji sanarwar.

Gwamna Nasir ya kuma roki jama’a da su ci gaba da bai wa jama’ian tsaro bayanai don kara samun nasara.

11/04/2023

Birtaniya Za Ta Daina Ɗaukan Likitoci Daga Najeriya

Birtaniya ta sanya sunan Najeriya a cikin jerin ƙasashen da ba za ta rinƙa ɗaukan likitoci da masu kula da masu rauni daga ƙasar ba.

Birtaniyar ta ɗauki matakin ne bayan sabunta ƙa’idojinta na ɗaukan ma’aikata daga ƙasashen ƙetare.

A yanzu sunan Najeriya ya faɗa cikin waɗanda aka sanya wa launin ja ko ɗorawa, wanda yake fitowa daga Hukumar Lafiya ta Duniya.

Jerin ƙasashen wanda WHO ke sabuntawa bayan shekaru uku na nufin cewa ba za a ɗauki jami’an lafiya daga irin waɗannan ƙasashe ba.

Hakan na nufin cewa Najeriya ba ta da isassun likitoci ko ma’aikatan lafiya da take buƙata, saboda haka bai k**ata su riƙa samun raguwar ma’aikatan ba.

Sabunta jerin sunayen da Birtaniyar ta yi tamkar biyayya ce ga shawarar Hukumar Lafiya ta Duniya.

A yanzu Najeriyar ta shiga jerin ƙasashe 55 waɗanda ba za a iya ɗaukan jami’an lafiya daga cikinsu ba.

Sai dai kundin ƙa’aidojin aikin da Birtaniyar ta fitar ya ce ƙasashen da ke cikin jerin waɗanda lamarin ya shafa za su iya fita daga jerin bayan tattaunawar fahimtar juna tsakanin ƙasa da ƙasa.

30/03/2023

DSS Ta Tabbatar Da Maƙarƙashiyar Kafa Gwamnatin Riƙo a Najeriya

Hukumar tsaro ta farin kaya ta ce ta shaida wasu jiga-jigai da ke kitsa wata maƙarƙashiya don kafa gwamnatin riƙon ƙwarya a kasar nan.

Hukumar ta ce maƙarƙashiyar, wadda wasu ke izawa ba kawai aba ce da ta saɓa wa doka ba, wani ƙoƙarin masu jamhuru ne na kifar da tsarin mulkin Najeriya da kuma jefa ƙasar cikin wani rikici da za a iya kaucewa.

Ta ce tunanin kafa gwamnatin riƙon ƙwarya, abu ne da ba za a amince da shi ba a tsarin dimokraɗiyya da kuma zaman lafiyar al'ummar ƙasar nan.

A saƙon da ta wallafa a shafinta na Tuwita ɗauke da sa hannun jami'in yaɗa labaran hukumar, Peter Afunanya, DSS ta ce tun bayan zaɓukan ƙasar nan da aka kammala cikin kwanciyar hankali, ake ta raɗe-raɗin kafa gwamnatin riƙo.

Sai dai DSS ba ta fito kai tsaye ta ce ga 'yan siyasar da take zargi da shirya wannan maƙarƙashiya ba.

Ta dai ce masu kitsa makircin, a jerin tarukan da suke yi, suna auna batutuwa da dama ciki har da yadda za su ɗauki nauyin zanga-zanga maras iyaka a manyan birane ta yadda daga bisani za a ayyana dokar ta-ɓaci.

Wani abin kuma shi ne, su samu umarnin kotu don hana rantsar da sabbin shugabannin da aka zaɓa da ƴan majalisa a matakin tarayya da jihohi.

Hukumar ta DSS ta bayyana goyon baya ga ƙudurin Shugaba Buhari na tabbatar da ganin an miƙa mulki ba tare da wani tashin hankali ba, kuma ta ce za ta yi aiki tuƙuru don ganin tabbatar hakan.

Ta kuma ce tana goyon bayan kwamitocin miƙa mulki da shugaban ƙasar ya kafa da kuma waɗanda aka kafa a jihohi.

Hukumar ta ƙara da cewa za ta yi aiki da sauran hukumomin tsaro don ganin an yi bikin miƙa mulki a ranar 29 ga watan Mayun 2023.

DSS ta kuma gargaɗi waɗanda ta kira masu shirin daƙile dimokraɗiyyar Najeriya su janye ƙudurinsu.

Ta kuma buƙaci hukumomi a ɓangaren shari'a da kafofin labarai da ƙungiyoyin farar hula su yi taka tsantsan don kada a yi amfani da su wajen tayar da fitina da ruguza zaman lafiyar ƙasar nan.

Address

New Market Street
Dutse
6-6

Telephone

+2349128097919

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Online radio zamani fm dutse posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Online radio zamani fm dutse:

Share

Category