![Gwamnatin Jihar Kebbi ta amince da cire kuɗi sama da Naira miliyan ɗari tara (₦925m) domin biyan kuɗin haƙƙoƙin ma'aikat...](https://img3.medioq.com/411/776/1405680864117769.jpg)
15/01/2025
Gwamnatin Jihar Kebbi ta amince da cire kuɗi sama da Naira miliyan ɗari tara (₦925m) domin biyan kuɗin haƙƙoƙin ma'aikatan da s**ayi ritaya da kuma waɗanda s**a rasu a bakin aiki mutum 367:
Daga Sani Twoeffect Yawuri
Maigirma Gwamna Kwamared Dakta Nasir Idris Ƙauran Gwandu ya amince da cire kuɗi sama da Naira miliyan ɗari tara (₦925m) domin biyan kuɗin haƙƙoƙin ma'aikatan Jihar da s**ayi ritaya na gratuity da kuma Death benefits na mutane 367.
Sanarwar hakan ta fito ne a cikin wata takarda da ta fito daga ofishin shugaban ma'aikatan Jihar mai ɗauke da sanya hannun Abdulrashid Muhammad Bala.
An rabawa manema labarai kofin takardun ranar laraba 15/1/2025 a garin Birnin Kebbi babban Birnin Jihar.
Takardar ta bayyana cewar ma'aikatan da za'a biya hakkokin nasu sun hada da ma'aikatan Jiha, ma'aikatan ƙananan hukumomi, ma'aikatan hukumar ilimi na ƙananan hukumomi wato LGEA, da kuma ma'aikatan wuccin gadi wato Contract staff da s**a aje aiki ko s**a rasu tsakanin 16/7/2024 zuwa 15/11/2024.
Wannan amincewa da Maigirma Gwamna yayi na biyan waɗannan kuɗaɗen ya nuna irin yadda Maigirma Gwamna ya ɗauki walwala da jindadin ma'aikatan Jihar da muhimmanci.
Sign Yahya Sarki