Taswira TV

Taswira TV Domin samun labarai da dumi duminsu ziyarci shafin tantabara mai albarka.

Hajiya Fatima Aliko Dangote ta tallafawa Fitacciyar kungiyar yan jaridu ta (Arewa Online journalist Forum) da tallafin S...
02/04/2024

Hajiya Fatima Aliko Dangote ta tallafawa Fitacciyar kungiyar yan jaridu ta (Arewa Online journalist Forum) da tallafin Shinkafa don rage raɗaɗi a watan Ramadan mai alfarma.

Hajiya Fatima tayi shura wajen ganin ta saka farin ciki a fuskokin Alummar Najeriya musamman arewacin Najeriya.

Hajiya Fatima ta kasance daya daga cikin jigo a kamfanin mahaifinta Dangote, ta biyo kalar kyawawan hali na mahaifinta Alhaji Aliko Dangote wajen ganin ta kyautatawa na kasa da ita

Shugaban Kungiyar yan jaridu ta (Arewa Online journalist Forum) Malam Barrah Almadany ya mika sakon godiya ga Uwar marayu Hajiya Fatima Aliko Dangote wajen yadda ta tsaya tsayin daka wajen tallafawa mabukata da kayan abinci a wannan wata na Ramadan.

Kazalika Almadany ya bukaci masu hannu da shinu suyi koyi da kalar halaye na Hajiya Fatima Aliko Dangote wajen taimakawa mabukata idan halin haka ya samu don rage raɗaɗi ga Yan kasa..

Dangote ya kaddamar da  tallafin rabon abinci na Naira Biliyan goma sha Biyar (15 Billion Naira)A wani mataki na rage ra...
24/03/2024

Dangote ya kaddamar da tallafin rabon abinci na Naira Biliyan goma sha Biyar (15 Billion Naira)

A wani mataki na rage radadin talauci a tsakanin al'umma, gidauniyyar Dangote ta kaddamar da tallafin rabon abinci na kasa a jihohin kasar nan inda mutane miliyan daya s**a amfana.

Alhaji Aliko Dangote ya tabbatar da cewa tallafin zai game dukkanin kananan hukumomin kasar nan 774, na kimanin buhunan shinkafa milyan daya me nauyin kilo 10.

Jihar Kano ta samu kaso mafi girma inda mutane 120,000 s**a amfana wanda daga bi sani rabon zai ci gaba a sauran jihohin kasar nan.

Haka zalika rabon shinkafa mai kilo 10 zai ci gaba a dukkanin sauran kananan hukumomi na Jihar Kano.

Bikin kaddamar da rabon abincin dai ya gudana ne a budadden dakin taro na fadar Gwamnatin Kano da shugaban rukunonin kamfanin Dangote Alhaji Aliko Dangote ya samu halarta da kuma Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf.

A cewar Alhaji Aliko Dangote , sun ga dacewar raba kayan abincin ne ba wai kawai don magance matsalar yunwa ba, har da batun saukakawa al'umma wajen gudanar da rayuwa a kasa ba-ki daya.

"Hakan kuwa ya zama wajibi duba da muhimmancin zumunci da 'yan uwan taka dake tsakanin mu, da kuma hadin kai a wannan lokaci da ake fusakantar kalubalen rayuwa.

"A wannan wata na Ramadan, lokaci ne da muke sadar da halayen nagarta, wanda ke taimakawa wajen tallafawa al'umma".

"Ina da kwarin gwuiwar sanar daku cewa wannan tallafin na yanzu na musamman ne, duk da cewar mun yi irin sa a kasa da wata guda da ya gabata, amman muka ga dacewar sake tallafawa al'umma musamman a wannan lokaci na Azumin watan Ramadan.

Attajirin Alhaji Aliko Dangote, ya shaidawa gangamin taron al'ummar cewa wannan kari ne akan tallafin da ya gudana na mutane dubu goma da ake ciyarwa kullum a Jihar Kano, yace Tallafin shinksfar Mai kilo goma da ya kaddamar kimanin miliyan Daya wanda ya lakume kudade Naira bilyan 15 a kasa ba-ki daya.

Da yake jawabi Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya yabawa shirin rabon tallafin.

21/11/2023
Kamfanin Sadarwa na TASWIRA MEDIA CONCEPTS, ya kaddamar da sabon Gidan talabiji me suna TASWIRA TV. Gidan Talabijin yana...
10/11/2023

Kamfanin Sadarwa na TASWIRA MEDIA CONCEPTS, ya kaddamar da sabon Gidan talabiji me suna TASWIRA TV.

Gidan Talabijin yana watsa shirye-shiryen sa akan utelsat Amos 17 Akan kwano, sannan ba dadewa ake sa ran fara k**a tashar akan DSTV da application din AVO TV da Googleplay.

Ana iya k**awa cikin kasashe 32 na Africa da Asia .

Zaku iya ganin wasu daga cikin shirye-shiryen su idan Kuka shiga shafin su na Facebook ://www.facebook.com/100049613665908/posts/925299409133839/?mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v

Ko.kuma YouTube @ Taswira studio.
Da kuma Twitter
Se tiktok @ taswira Tv.

Ana iya k**a TASWIRA TV akan utelsat Amos 17 Akan kwanu

Kuyi searching TASWIRA TV domin samun ingatattun shirye-shirye da s**a danganci Al'ada .

INNALILLAHI WAINNA ILAIHIR RAJIUN. *Asibitin Nasarawa dake kano yana neman zama makasar Al'umma*Daga:Tajuddeen shuaibu K...
10/10/2023

INNALILLAHI WAINNA ILAIHIR RAJIUN.

*Asibitin Nasarawa dake kano yana neman zama makasar Al'umma*

Daga:
Tajuddeen shuaibu Koki.

A yau Talata 10/10/2023 an fitar da Gawa ta kai guda Goma daga Asibitin.

Wasu Ajali ne .wasu kuma Ganganci da Sakacin Likitocin ne yake zama silar rasa Rayuwar su.

Kaf kano yanzu babu Asibitin da Jama'a suke kuka dashi irin Asibitin Nasarawa.

Majinyaci yana iya sati batareda Likita ko daya yazo kan sa ba duk suna private Hospitals.

Idan kanaso ka sayi magani akwai masinja da zaka bawa yaje ya siyo ma na sata a 6angaren pharmacy din 'yan inshora.

Da ido na naga yadda ake safarar masu Allura daga wajen Asibitin,saboda Nurses din se sunga dama zasuyiwa mara Lafiya Allura ko kuma kabiya su .

A 6angaren Lab ma hakan take .

Wallahi Tallahi ni ganau ne akwai Lokacin da kaf Asibitin babu Robar daukar sample din jini ko fitsari (container) sedai ayi sharing wannan yayi yabawa wannan. Sannan idan kanaso ayima gwaji a kwana daya sedai kabiya batareda receipt ba.

Idan ka zagaya Bandakunan Asibitin su ma sedai kayi kashi akan wani kashin ko kuma kafita ka nemi gidan wanka .

Dan Allah a taimaka ayi sharing har sakon yaje inda Yadace

Sanya Sarakuna A Harkar Filaye Da Gidaje Zai Taimaka Wa Tsaro - Shugaban Kungiyar DillalaiDaga Ibrahim Ammani KadunaAn b...
25/09/2023

Sanya Sarakuna A Harkar Filaye Da Gidaje Zai Taimaka Wa Tsaro - Shugaban Kungiyar Dillalai

Daga Ibrahim Ammani Kaduna

An bayyana cewa sanya Sarakunan Gargajiya a harkar sayarwa da bayar da haya na filaye da Gidaje zai taimaka wajen inganta fannin tsaro a fadin Jihar Kaduna.

Shugaban Kungiyar Dillalan Filaye da Gidaje na yankin ƙaramar Hukumar Kaduna ta Arewa Alhaji Maharazu Abdulwahab ya bayyana hakan a yayin wata tattaunawa da ya yi da wakilinmu a ofishin kungiyar dake Kaduna kan matakan gwamnatin Kaduna na inganta tsaro.

Maharazu Abdulwahab ya ƙara da cewar Sarakuna musamman dagatai da masu unguwanni sune mafi kusa da jama'a idan ya zamana suna da ruwa da tsaki wajen bayar da muhalli ga jama'a babu shakka hakan zai taimaka wajen tabbatar da tsaro da wanzuwar zaman lafiya a tsakanin al'umma.

Shugaban Dillalan wanda kuma Basarake ne dake riƙe da sarautar gargajiya ta Garkuwa Babba na Masarautar Chikum a jihar Kaduna ya yaba salon shugabanci na gwamna Jihar Kaduna Malam Uba Sani musamman akan abin da ya shafi batun samar da Filaye da Gidaje a faɗin Jihar.

"Mai girma Gwamna Uba Sani ya sanya farin ciki a zukatan jama'ar jihar a bangaren harkar Filaye da Gidaje inda ya hana rusa wa jama'a gidaje tare da bayar da umarnin a gabatar mishi da bayanan duk wani gini da ake korafi an yi shi ba bisa ka'ida ba ya bincika da kanshi, sannan da shirin bayar da kaso 30 na hakkin al'umma da ya yi abu ne da ya faranta ran jama'ar jihar".

Shugaban Kungiyar Dillalan ya shawarci abokanan sanar'ar tashi waɗanda har yanzu ba su yi rijista da kungiyar tasu ba da cewar su yi gaggawar yin haka domin dacewa da alfanun da ke cikin kungiyar.

Daga karshe ya shawarci jama'ar jihar Kaduna da su cigaba da mara wa Gwamna Uba Sani baya domin dacewa da shan romon mulkin Dimokuradiyya domin Hausawa na cewar dukkanin wata juma'a da za ta yi kyau tun daga Laraba ake gane ta.

Fitar Da Zakka Ne Makullin Dukkanin Talauci - Sakataren Gidauniyar Zakka Da Wakafi Na Jihar KadunaDaga Ibrahim AmmaniAn ...
24/09/2023

Fitar Da Zakka Ne Makullin Dukkanin Talauci - Sakataren Gidauniyar Zakka Da Wakafi Na Jihar Kaduna

Daga Ibrahim Ammani

An bayyana fitar da Zakka da kuma bayar dashi ga waɗanda addini ya tanada a matsayin wata hanya guda ta magance dukkanin wata kofar Talauci dake addabar jama'a.

Sakataren Gidauniyar Zakka da Wakafi ta jihar Kaduna Malam Nuruddeen Muhajid ya bayyana hakan a yayin wata tattaunawa da manema labarai da ya yi a Kaduna.

Nuruddeen Muhajid ya ƙara da cewar la'akari da halin da jama'a Musulmi s**a yi na sakaci da wannan rukuni cikin rukunan musulunci na bayar da Zakka ne ya sa s**a samar da wannan gidauniya wacce ta ke tattarowa gami da rarraba Zakka a tsakanin al'umma kuma ita ce ta farko irinta a jihar Kaduna.

Sakataren ya ƙara da cewar sun kafa Gidauniyar tasu ne tun a shekarar 2021 kuma tun daga wannan lokaci suke aikin tara kudaden Zakka daga hannun masu kudi, inda a shekarar farko s**a raba Naira miliyan Uku sannan a shekara ta biyu s**a raba Naira miliyan 10 yayin da a shekarar bara s**a raba Naira miliyan 16.

"A farkon shekarar nan mun gudanar da babban taro na ƙasa domin wayar da kan jama'a akan muhimmancin bayar da Zakka inda muka gayyato jama'a daga dukkanin jihohin ƙasar nan 36 harda Abuja aka yi babban taro anan Kaduna wanda kuma an samu nasara sosai.

Malam Nuruddeen Muhajid ya bayyana cewar matukar gwamnati za ta marawa shirin nasu baya a Jihar Kaduna to babu shakka za a samu gagarumar nasara wajen kawo karshen matsalar fatara da talauci dake addabar al'umma.

Har Yanzu muna da Visa ta aiki a Canada, Amma da kudi ake Neman kudi, suna da gwagwgwa6an salary 15CAD per hourDuk hour ...
23/07/2023

Har Yanzu muna da Visa ta aiki a Canada, Amma da kudi ake Neman kudi, suna da gwagwgwa6an salary 15CAD per hour

Duk hour 1 suna biyan Canadian Dollar 15 ne, shi ne mapi Qarancin salary su

Wanda yasan bashida kudi Dan Allah kada yayi mana magana

Da kudi ake Neman kudi Mallam

Cikin wata biyu in sha Allah ka mayarda kudin da ka kashe kapin katapi

Bazamu anshi kudin ka ba, saikazo da lauya, muyi rubutu mu fada maka lokachin tapiya

07019899260

19/07/2023

An shawarci musulmai da su maida hankali kan Salatin Annabi S.A.W da Istigfari ,maimakon surutai.
~Sheikh muhyiddin Gwani Ashir

12/07/2023

Ku danna mana like a sabuwar jaridar mu me suna jaridar Kaakaki domin samun ingattattun labarai

12/07/2023

KOWA DA KIWON DA YA KARBE SHI:-

Wani matashi Dan kasar k**aru me suna Town cried ya dauki hanyar kafa tarihi a kundin Guinness na cinye gasar shafe awa 100 ana kuka ,inda yanzu haka ya shafe fiyeda awa shida yana sharara kuka batareda alamar gajiyawa ba

12/07/2023

YANZU YANZU: Acikin Daren Nan Ƴan ƙabilar mwagavul sun tare hanya sun k**she mahajjata guda 9 a ƙauyen Kereng ƙaramar hukumar mangu jihar Filato akan hanyarsu ta komawa gida yelwan shendam daga saudi arabia.

10/07/2023

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, Ya Nada Sheikh Aminu Ibrahim A Matsayin Babban Kwamandan Hisbah Kano A Karo Na Uku

09/07/2023
Kuyi mana like da follow
08/07/2023

Kuyi mana like da follow

Allahu akbar. Ina cikin tafiya kwatsam se na ganni a titin Isah Waziri hanyar zuwa masallacin murtala .Aikuwa nan take g...
22/06/2023

Allahu akbar.

Ina cikin tafiya kwatsam se na ganni a titin Isah Waziri hanyar zuwa masallacin murtala .

Aikuwa nan take general murtala Muhd yafadomin saboda irin alkhairan sa da yadda yayiwa dan najeriya tsarin da baa ta6a yi masa ba,

Take na yanke shawarar tsayawa domin ziyartar sa da yi masa adduar samun rahamar ubangiji a kabarin sa .

Abin mamaki :-
Ina shiga se naga wajen sa6anin yadda nasan shi a baya ,sak**akon ina tsayawa nayi masa addu'a indai zan wuce wajen .

A shekarun baya idan naje nakan ga awakai a kwance akan kabarin suna hutawa hade da yin kashi akan kabarin saboda babu wani shamaki da akasa domin kare awakan daga shiga wajen ,to amma cikin ikon allah yau da naje se naga angyara wajen an gewaye shi da gini harda rufi ta yadda babu damar awakai su shiga suyi fitsari akan kabarin bawan allahn da ya hidimtawa kasar sa da addinin musulunci.

Allah kajikan murtala Muhd ka kyauta kwanciyar sa .kasada shi da annabi Muhammadu sallallahu alaihi wasallam.

©️Tajuddeen shuaibu Koki

Da yammacin wannan rana ne mai girma gwamnan jihar Kano Engr. Abba Kabir Yusuf ya karɓi bakuncin ɗaya daga cikin jakadun...
13/06/2023

Da yammacin wannan rana ne mai girma gwamnan jihar Kano Engr. Abba Kabir Yusuf ya karɓi bakuncin ɗaya daga cikin jakadun ƙasar Saudi Arabia dake nan jihar Kano (Saudi Console) H.E. Khalil Adamawy a fadar gwamnatin kano.

Daga
Tajuddeen shuaibu Koki

Kaduna: Nazir Sanusi Ne Zaɓin Mu - Jama'ar Mazaɓar KawoAn bayyana ɗan takarar kujerar ɗan Majalisar dokokin Jihar Kaduna...
16/03/2023

Kaduna: Nazir Sanusi Ne Zaɓin Mu - Jama'ar Mazaɓar Kawo

An bayyana ɗan takarar kujerar ɗan Majalisar dokokin Jihar Kaduna mai waklitar Mazaɓar Kawo karkashin jam'iyyar APCHonorabul Nazir Sanusi Abubakar a matsayin wanda ya zarce tsara kuma shi ne fata ga jama’ar yankin.

Al’ummar mazabar Kawo ne s**a bayyana hakan a wata tattaunawa da s**a yi da Wakilinmu da ya ziyarci yankin a ranar Juma’a.

Sun bayyana yankin nasu a matsayin wanda ya dade cikin koma baya sak**akon rashin samun kyakkyawan wakilci, amma cikin ikon Allah samun Nazir Sanusi cikin ‘yan takara ya sanya sun samu karsashi da ganin wanda zai kai yankin nasu ga nasara, kasancewar shi wanda ya yi kuma an gani a baya a muƙamin da ya riƙe na mataimakin shugaban ƙaramar Hukumar Kaduna Ta Arewa.

A zantawar da ya yi da Wakilinmu ta wayar tarho Honorabul Naziru Sanusi Abubakar ya bayyana cewar damuwa da kishin jama’ar yankin nasu ne ya sanya shi fitowa takara domin bada gudunmawa na ciyar da yankin gaba.

Kungiyar Inyamuran Jihar Kaduna Sun Goyi Bayan Takarar Sanata Uba SaniKungiyar Ibo (Igbo), mai suna Kaduna State Igbo Co...
08/02/2023

Kungiyar Inyamuran Jihar Kaduna Sun Goyi Bayan Takarar Sanata Uba Sani

Kungiyar Ibo (Igbo), mai suna Kaduna State Igbo Community Welfare Association, ta nuna goyon bayan ta ga dan takarar zama gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani na Jam'iyyar APC.

Da ya ke magana a wurin wani taro ranar Lahadi a Kaduna, mai bada shawara na kungiyar, Valentine Ewuzie, ya ce, "Uba Sani, Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, shi ne ya cancanta da ya rike ofishin gwamnan Jihar Kaduna."

Ewuzie ya ce, Sanata Uba Sani ya nuna ya kaunar al'ummar Ibo (Igbo).

Ya kuma kara da cewa, "Mun yi nazari da tantance dukkan 'yan takarkarun, kuma mu na ji yanzu, ba tare da gutsutstsura kalamai ba, mun tabbatar kai ne dan takarar mu." Inji shi.

"Kuma kasancewa mafi tsari, za mu iyakacin kokarin mu, don ganin ka zama gwamnan jihar Kaduna."

Ya kuma tuna lokacin da Uba Sani ya ke mai bada shawara ga gwamna Nasir Ahmed El-Rufa'i, ya zauna da kungiyar Ibo na jihar, ya kuma tabbar da amincin sa.

Ya yaba wa Gwamnatin Jihar Kaduna na soke bambanci wurin daukar kwararrun aiki, har da malamai a kan cancanta. A cewarsa.

ALLAHU AKBAR: Wannan Bawan Allah da kuke gani sunan sa Malam Dauda me faci ɗan ƙaramar hukumar Malumfashi ne kuma ma zau...
08/02/2023

ALLAHU AKBAR: Wannan Bawan Allah da kuke gani sunan sa Malam Dauda me faci ɗan ƙaramar hukumar Malumfashi ne kuma ma zaunin ta yana sana'ar faci a garin.

Wannan bawan Allah tsakanin shi da mai girma Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru Rufa'i sun kasance asali abokai ne tare s**a taso aji ɗaya makaranta tun a lokacin yarin ta kwatsam jiya Dauda na zaune a wajén sana'ar facin sa sai ga kiran Gwamna Malam Nasiru El-Rufai Rufa'i a waya yace:

"Dauda gani na dawo daga katsina zan wuce gida na tsaya a garin ku Malumfashi wajenka kazo nan gidan hali sa'adu mu haɗu da kai yanzu.

Atake sai Malam Dauda ya hanzarta yayi sauri ya tafi yaje s**a samu ganawa da juna.

To kaji aminci da abota ta amana kar ka sake ka taba wulakanta abokinka na makaranta ko wanda kukai rayuwa ta yarin ta domin kowa bakasan irin baiwar da Allah yai massa ba a gaba.

©Amintaciyya.

Kaduna: Zan Tafi Da Mata Da Matasa Idan Na Zama Gwamna - Inji Sanata Uba SaniDAN takarar zama gwamnan Jihar Kaduna, Sana...
05/02/2023

Kaduna: Zan Tafi Da Mata Da Matasa Idan Na Zama Gwamna - Inji Sanata Uba Sani

DAN takarar zama gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya bayyana farin cikin sa ganin yadda mata su ka nuna masa ƙauna da goyon baya a kan takarar sa.

Sanatan ya yi godiya ga Allah da ganin irin cincirindon da mata su ka yi don nuna goyon bayan su gare shi.

Uba Sani ya ce, "Alhamdu lillah. Hakika mata su ne kashin bayan dukkannin al'umma, kuma kowa ya sa da cewa mata su ke bada kuri'a a ranar zabe. Don haka, k**ar yadda ku ka fito a yau, ku fito a ranar zabuka, ku zabi jam'iyyar APC tun daga sama har kasa, kuma ku bi 'yan'uwan ku mata gida gida, ku fada masu su zabi APC don ci-gaban ku da na 'ya'yan ku"

Uba Sani ya ce, "In Allah ya yarda za mu rike maku amana. Kuma ci-gaba da ku ka gani a Jihar Kaduna, wanda shugaban mu ya kawo Malam Nasir Ahmed El-Rufa'i, ba za mu ba ku kunya ba da yardar Allah. Za mu dora Kaduna na mata ne da yardar Allah."

Haka kuma ya yi godiya ga dukkan matan jihar Kaduna da su ka fito dubunnan su, su ka nuna goyon bayan su ga dan takarar shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, da ni kai na da kuma dukkan 'yan takarar jam'iyyar APC, ta bagaren hadin kai na tattaki, wanda matar gwamnan jihar Kaduna, Hajiya Hadiza Isma El-Rufa'i ta jagoranta.

Dan takaran ya ci-gaba da cewa, "Ayyuka za su ci-gaba ta hanyar saka mata a cikin siyasa da gwamnati, k**ar yadda da ma Malam Nasir Ahmed El-Rufa'i ya assasa."

Sannan ya yi godiya ga Mamman Lagos Support Group (MLSG) da The Women In Politics (W.I.P), bangare Kaduna na saka wa taron karsashi tare.

An dai yi wannan taro ne na tattaki a dandalin Murtala Square da ke Kaduna, wanda Ƙungiyar Mamman Support Group (MLSG) da Ƙungiyar The Women In Politucs (W.I.P), karkashin jagorancin uwargidan gwamnan jihar Kaduna, Hajiya Hadiza Isma El-Rufa'i.

YANZU-YANZU: Alhaji Muhammad Hameem Nuhu Sanusi Ya Zama Sabon Sarkin Dutse, Jihar JigawaMasu zabar sarki guda bakwai a m...
05/02/2023

YANZU-YANZU: Alhaji Muhammad Hameem Nuhu Sanusi Ya Zama Sabon Sarkin Dutse, Jihar Jigawa

Masu zabar sarki guda bakwai a masarautar Dutse sun zaɓi, Alhaji Muhammad Hameem a matsayin sabon sarkin Dutse, ciki harda kuriu uku na masu zabar guda uku da s**a nemi sarautar.

A wata sanarwar da masarautar Dutse ta fitar yau Lahadi, ta ce an gabatar da sunan sabon sarkin da aka zaɓa ga majalisar sarakunan jihar Jigawa wanda ta amince da sunan da masu Zaɓar sarkin masarautar Dutse s**a bayar.

Sanarwar ta kara da cewar majalisar sarakunan jihar Jigawa ta aike da sunan Muhammad Hameem da sauran yan takarar biyu ga gwamnan jihar Jigawa Muhammad Badaru Abubakar domin neman amnincewarsa kuma ya amince da wannan zaɓin.

Idan Allah ya kaimu karfe 4:00 na yammacin yau za'a miƙa wa sabon sarkin takardar k**a aiki a fadar sarki dake Garu.

Allah Ya Taya Riko!

Daga Jamilu Dabawa

Kaduna: Zan Ƙarasa Ayyukan Cigaba Da El Rufa'i Ya Fara A Chikum - Sanata Uba SaniDan takarar Gwamnan jihar Kaduna a jami...
03/02/2023

Kaduna: Zan Ƙarasa Ayyukan Cigaba Da El Rufa'i Ya Fara A Chikum - Sanata Uba Sani

Dan takarar Gwamnan jihar Kaduna a jamiyyar APC Sanata Uba Sani ya yi alkawarin ci gaba da koyar da mata sana'oin hannu don su zamo masu dogaro da kansu idan aka zabe shi a matsayin gwamnan jihar a 2023.

Ya yi nuni da cewa, gwamnatin jihar ce tilo a kasar nan da ta ke yin tafiya da mata, inda ya ce, in ya kai ga gaci, zai tabbatar da nada mata a cikin gwamnatin sa da kuma tallafa wa kasuwanci su.

Dan majalisar ya bayyana hakan ne a yayin da ya gana da alummar karamar hukumar Kajuru a lokacin da yaje gangamin yakin neman zabensa da mataimakiyar sa Haj Hadiza Sabuwa Balarabe.

Uba ya yi alkawarin taimaka wa jama'an tsaro da ke gudanar da da ayyukan yakar yan bindiga daji da ke aikata ta'asar su a wasu sasaan jihar.

Ya ce, akwai bukatar jihar da kananan hukomomin da ke jihar da kuma sauran dai daikun jama'ar da ke a jihar, suma su bayar da ta su gudunmawar don a kara tabbatar da tsaro a jihar.

Ya yaba wa gwamnan jihar Nasir Ahmed El-rufai akan samar da kayan aikin ga jami'an soji don su yaki yan bindigar inda ya ce, hakan ya taimaka matuka wajen dawo da zaman lafiya a jihar, mussman idan aka yi la'akari da yadda dakarun suke ci gaba fatattakar yan ta'addar daga mafakar su.

Uba ya kuma kaddamar da aikin dakin shan magani na matakain farko da aka gyra aka kuma sanya kayan aiki.

Har ila yau, a jawabinsa a fadar Etsu Chikun Sanata Uba ya yi alkawarin ci gaba da gudanar da ganawar da alummar gari musamman don wanzar da tsare-tsaren gwamnatinsa in Allah ya bashi nasara.

Ya yi nuni da cewa, nadin da aka yiwa Etsu na Chukun hakan ya kara tabbatar sa zaman lafiya a yankin, inda ya ce, rikice-rikicen addini da na kabilanci a yankin, sun ragu matuka.

Ya ci gaba cewa, in har aka zabe shi, gwamnatin sa za ta mayar da hankali wajen kammala ayyukan hanoyi a Chikun tare da kuma kara kirkiro da wasu sabbi .

Bugu da kari, Sanata Uba a jawabin da ya yiwa dandazon magoya bayansa

Address

Birnin-Kebbi

Telephone

8135460004

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Taswira TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Videos

Share


Other Media/News Companies in Birnin-Kebbi

Show All

You may also like