03/12/2023
Yana da kyau ku fahimci cewar ba duk mutanen da su ka ce suna son ku ba ne masoyanku, haka kuma don mutane ba su faɗa mu ku suna son ku ba, baya nufin su maƙiyanku ne. Ba duk mutanen da ku ke so ba ne za ku rayu tare da su, amma za ku iya son mutanen da rayuwa ta haɗa ku da su. Ba duk mutanen da ke ɓata mu ku rai ba ne maƙiyanku, a'a suma masoyanku za su iya ɓata muku rai wataƙil ma fiye da maƙiyanku, ba duk wanda ya faranta mu ku ko ya mu ku kyauta ba ne masoyinku wasu wata manufa ce take ingiza su ga mu ku hakan. Ba za ku samu dukkan kyawawan halayen da ku ke so daga masoyanku ba, amma ku za ku iya nuna musu dukkan kyawawan halayenku. Ba dukkan mutanen da ke maƙale mu ku suna bibiyar ku ba ne masoyanku, kuma ba dukkan wanda ba sa zuwa gare ku ba ne suke jin haushin ku, wasu sun zo gare ku ne don su cutar da ku haka wasu sun bar ku ne domin neman maslaha.
Zai kyautu ku gane, soyayya tana cigaba tana ci baya tana kuma mutuwa, kuna iya ƙulla ta a inda babu ita ta ko ku yanke ta a wurin da akwai ta, yana danganta ne da aiyukanku. Za ku fara soyayya da wasu amma ba za su so ku har abada ba, a hanyar tafiyar rayuwarku za su daina son ku ba lallai su zama mugaye ba idan sun daina son naku hakan ka iya faruwa don soyayyar ta cimma ajalinta ko abunda su ke so a tare da ku ya gushe ko sun riga sun samu, wasu za su kasance maƙiyanku a farko ana cikin tafiya son ku zai samu gurbi a zuciyarsu. Ku sani mutun tara yake bai cika goma ba har ma su son ku ba za su fita daga wannan ƙa'idar ba dole za su gaza a wani layin, su ma maƙiyan naku kada kuyi zaton ba za su taɓa zama sanadin alheri gare ku ba. Yana da muhimmanci ku sani za ku iya shiga wani hali da za ku so masoyanku da ku ka yarda su su zo gare ku don kawo mu ku ɗauki ko jajanta mu ku amma ba za su so ba, za su ƙi zuwa ba don basa son ku ba sai don ba za su iya zuwan ba.
©Anas Darazo